page 5

486 23 0
                                    

🅱 *RILLIANT WRTER'S* *ASSO*🖊

{Pen's of freedom, home exceptional and magnificent writer's}





*KOMAI DADIN DUNIYA!*
   _Kiyama ta fishi_



*Ummerherny Nerserllerh*


*Sadaukarwa*

*SURAYYAHMS*
_OFFICIAL CATTY_🐈







*FEEDON INA MIKA* *TA'AZIYARMU TARE DA* *ABOKAN AIKINMU BAKI* *DAYA GA BISA* *RASHIN DA MUKAYI NA* *KAKA ALLAH YA* *JIKANTA DA RAHAMA,* *ALLAH YASA TA HUTA,* *ALLAH YA KYAUTATA* *MAKWANCINTA ,ALLAH* *YA KYAUTATA* *KARSHENMU, AMEEN*





5

Hira suka shan sosai cikin soyaya da shakuwa, daga bisani sukayi sallama, ta shiga cikin gida da farin ciki tana wak'a,, aganka a barka ya zama dole, akwana a tashi Zan kwana kan makiyi na, haka ta wuce husna na karatu, murmushi Husna tayi ta cigaba da karatunta,yarkazuna ta Kira ta sanar dashi halin da ake ciki, dariya yayi irin ta marasa imani ya ce, yarinya saura kiris,godiya tamar ta katsai wayar, tana raira wak'a tana rawa.

Bangaran amina abun ba sauki,rabonta da Jamal sati biyu kenan, ga, jinin yanxu har yafi na baya, yanxu KO cikin mutane bata iya shiga"domin karnin da take,.
   Amina ta kasa fad'an matsalarta wa kowa, ita tana ga in ta farawa wa wani, za'a ce mijinta ya kasa kula DA ita,, wata zuciyarce ta bata shawara ta sanar amma wani gefen zuciyar tana azazalar ta da ta boye sirrinta, haka kuwa akayi shiru tayi ta cigaba da addu'a, ta mika al'amarinta ga Allah.
 
   Jamal kuwa tunda Allah ya hadashi da Nuwaira yake jin kansa na Kara huruwa, kusan kullum sai yayi zuwa uku ko hudu gidansu, Haka awaya suna manne.
   Yau da misallin karfe biyu na Rana Jamal ya tafi wurin nuwaira kamar yadda ya Saba, daga isarsa ta tsaraishi da zance akan cewa innarsu ta ce in da gaske yake ya turo magabantansa, daman yarkazuna ya sanar da ita, yau ta sanarmar ya turo ayi zancen aure, cikin jin dadi, wadda farin cikinsa ya kasa boyiwa ya ce, Alhamdulillah,baby nayi kusan a malakamin ke amatsayin uwar 'ya'ya na".

Sosai ma kuwa kalbi, na dade da mafarkin wannan Rana amma sai akayi min cikas, wata ta budeka a kwali, banso na same ka a matsayin wadda wata ta Fara amfani ba, har maniyinka ya shiga mahaifanta, nayi ta kace da maniyinka na farko ya Fara raban wata, amma ba komai yanxu ma bata baci ba.

  Jamal murmushi yayi ya ce Baby kenanAi duk tarayan da nayi da amina ban dauketa amatsayin wata aba ba, ,Bari na ta kaice miki bayani, Nuwaira rabona da amina 2week ne"
  KO Zan iya sanin dalili?
 
Eh!Nuwaira akwai dalili, amina ta kasance cikin dan wannan kwanki tana yawan zub da jini kuma ba al'ada take ba, na tambayeta komai tayi amafani dashi ya kawo Mata wannan matsalar amma ta ce bata sani ba, bana iya zama da amina saboda karni da take!

  Nuwaira farin ciki ne fal zuciyarta, amma a fili ta nuna damuwarta ta ce Ayyah, ai wannan ba wata matsala ba ce, kalbi daman akwai matan da suke wannan abun, wasu akayi sa'a su warke wasu kuwa haka zasu cigaba har tsawon rayuwansu, karka damu za'a samu mafita, nan ba da dade wa ba, Zanyi magana da innata ,akwai wata sister ta tana da wannan magnain matsalar ta bamu.
   Baby banso ki wahala kinji, karki bawa Inna wahala, yanxu dae ba wannan ba, yaushe kike ga zasu zo ne?
  Kai ta d'aga alamar tunani, hmm!gobe ma yayi?
Yes!
  Kalbi kasan me, labarin da ka bani na Anty na kasa naji wani iri ,ka Bari na karbi wannan maganin kaji, yadda ta yi da fuskarta kamar gaske.
  Badamuwa amma kinsan dae ba zuwa gidan nake ba ko?
   Ko baka zuwa kayi
dabara, kayi Mata note ka aje a inda zata gani,
   Ai ba lalai ne ta yi amfani  da maganin ba"
  Haba kalbi zata yi domin nasan tana bukata kai dae Bari akawo"
Toh!ba matsala Allah ya miki albarka baby, kina da kyauta na musamman,.
   Murmushi tayi, kasan wacce kyauta nake so kayi min kalbi?
  A'a sai kin fad'a.
Ina son ka malakamin kanka sannan ka gyaramin kanka, yadda Darenmu na farko naji ka a matsayin gwarzon namiji"
  Indae wannan ne, baby an gama, yanxu bari Zan je na samu Abba muyi magana zaki jini anjima.
  Toh, kalbi sai na ji ka, nima wurin Jidda zani, sallama sukayi dukansu suna farin ciki.

Ta sanar da Jidda duk halin da ake ciki kuma sunyi murna mallaminsu yayi aiki .

   Bayan sallah mangarib Nuwaira ta samu Inna da magnar jamal, Inna tayi tunanin wane jamal kasancewa ta San jamal a baya, Nuwaira tayi wa Ina bayani yadda ya kamata, bata jira amsar Inna ba, ta ce gobe zasu zo, dan haka ki sanar da yayanki, ko kanin Baba, daga fad'ar haka ta wuce, Inna baki sake take binta da kallo, Inna tayi farin ciki da haka domin zata huta da ciwon baki, Husna ta aika gidansu ta sanar da kawo buba zance fatan alkairi yayi kuma ya bata lokcin da zasu zo,.
  Bayan husna ta dawo ta sanar wa Inna abinda kawu buba ya fad'a kiran nuwaira Inna tayi ta sanar da ita lokacin da zasu zo, baki ta tabe tayi gaba.







Pls comment

KOMAI DADIN DUNIYA KIYAMA TAFI SHI😭Where stories live. Discover now