13

397 18 3
                                    

🅱 *RILLIANT WRTER'S* *ASSO*🖊

{Pen's of freedom, home exceptional and magnificent writer's}





*KOMAI DADIN DUNIYA!*
   _Kiyama ta fishi_



*Ummerherny Nerserllerh*


*Sadaukarwa*

*SURAYYAHMS*
_OFFICIAL CATTY_🐈










13





*Haleema 2o ,muna mika sakon gaisuwarmu na rashin da mukayi Allah ya jikanta da rahama Allah ya sa tayi tafiyar sa'a   ,Allah ya kyautata abinda ta bari Allahya kyautata tamu in tazo ,da ni da madadin brilliant* 😭👏🏻

Hajiya kan Amina tayi da sauri, lokaci daya Hajiya ta rude hankalin ta ya tashi, Nurses station ,wata nurse ta samu, kasa magana tayi sai nuni da take Mata da ya tsa da hannu .
Nurse din ce, ta ce mama me ya faru, bangane abinda kike fad'a ba.
  'Yata, dan Allah Ku taimakamin, da saurin nurse din ta bi hanyar room din daAmina take, hajiya bayanta ta bi, abin gwaje gwaje ta dauka ta shiga dubata, hannunta ta Kama ta ji yanayin tafiyar jininta, sai dae bugun zuciyarta ya  tsananta, nurse din ne ta dubi hajiya ta ce, hajiya akwai abunda kuka sanar da ita ,shi Yayi sandaiyar d'aga Mata hankali .

  Idon hajiya fal da hawaye ta ce,babu yanxu mijinta ya fita, shigowar da nayi ne na tarar da ita haka.
   Mama akwai dalili, amma Bari na Kira doctor domin asan abunyi, taimakon gagawa suka bata,.
  Hajiya waya ta dauka ta Kira Abba, lokacin Abba na hanyarsa ta dawowa daga gidansu Amina,dashi da su umma, sanar dashi halin da ake ciki tayi ,daga bisani ta katse wayar,.
  Kiran Ummi ne ya shigo wayar Hajiya dauka tayi muryanta na rawa, Ummi ta ce lafiya kuwa?
Ina lafiya, yanxu yayanku yazo bayan ya tafi amina jikinta ya rikice, Ummi in amina ta mutu ya zamuyi.
  Hmm!yaya jamil na daf da aikin danasani da nasani kuma kyeya ce, Nima gani zuwa Abulkhairi Yayi barci Zan barshi wurin ummikursum su kwana, in yaso sai ki dawo gida,Ummi bazan iya barin Amina a wannan halin ba gaskiya, sai dae ki zo in Alhaji zai koma kwa tafi, sallama sukayi Ummi ta shirya ta bar ummikursum da Abulkhairi dake ta barcinsa.

  Dae dae lokacin da isa lokaci su Abba suka iso har kasa Ummi ta tsugunna ta gaida su umma da abbansu amina, wucewa sukayi kowa da abunda yake sakawa a ransa domin Umma kallo daya zakayi Mata kaga tsananin tashin hankali a tatarai da ita ,haka suka isa gwaiwan kowa Yayi sanyi, basu sami ganinta ba, sai daaka gama duk wani abunda aka yi Mata, bayan wani lokaci doctrs din suka fito sai sharai zufa suke,.
  Hajiya ne ta taraisu da ciwa, doctor ya dae Mai jikin fatan dae'yata zata tashi kamar kowa, sai da kowa ya tausayawa hajiya domin tafi kowa rudewa, harta umma tausayin hajiya take duk da tana tausaya wa kanta,.
In sha Allahu ,ganin hajiya KO ya Mata bayani bazata fahimta ba, ya sa ya ce da su Abba su biyo shi,.
Bayansa su Abba suka bi.
  Umma ta Kama hannun hajya ta zaunar da ita a kujera, ta daurai ta ce, haba hajiya zainab kiyi tawakali man, komai da kika gani jarabawa ce, ba abinda ya fi karfin Allah, Allah bai saukar dacuta ba sai da ya saukar da maganinsa,kuma Allah ya man jarabi bawansa da abubuwa iri iri, daman rayuwan da muke akan jarabawa ce, muyi hakuri mu dauki, lalurar da Amina take ciki, jarabawa ce, muyi hakuri mu rugumi kaddarar Allah, mu bar wa Allah, shi yafi mu sanin komai, duk son damuke wa Amina Allah ya fi mu sonta.

   Hajiya ta ce haka ne raihanatu, amma bazaki gane rad'adin da ke zuciyata ba ne, mun kasa rike amanar da muka daukaJamil ya cutar da amina, ni ma ya cutar da ni,ba don ni na haifi jamil ba, gaskiya da na dasa ayar tambya akansa, komai da ya samu amina shine sila, bazan taba boye aibun jamil ba saboda ni na haifaishi, ka so naka duniya ta ki shi, suyimar tofin Allah tsine, ka ki naka duniya ta so shi ta sanya mar albarka, nan ta kwashe duk abunda yake faruwa ta gayawa umma ,umma hankalinta ya tashi amma sai ta dae ne na ta saboda yadda, hankalin hajiya yake tashe.
  Umma ce ta gyara zama ta ce, hajiya ba wai na raina naku d'a wainiyar da kuke Amina bane, Zan so Ku bani amina mu gwada maganin Islamic domin ina ga kamar da aikin sihiri.
   Haba raihana, yaushe amina ta yi magna balle ta samu abokin gaba da zai Mata wannan danyen aiki ""
   ""Murmushi Umma tayi ta ce, haka ne hajiya amina bata da abokin fad'a nasan haka, sai dae makashinka na bibiyarka duk inda kake, kiyi hakuri mu Fara wannan din kafin wani lokaci.

  Sai lokacin Ummi tayi magana ta ce, umma nima nayi tunanin sihirin ne sai dae bazaka ce ga wadda Yayi ba, saboda ba ilimin hakan kake dashi ba.
  Raihana, bazan iya baki amina ba, ko da na yarda da zancenku, amina baza motsa daga inda nake ba.
  Hmm!hajiya kiyi hakuri!
Raihana kiyi hakuri, bazan iya ba, tashi tayi ta vasu wuri ta tafi kofar room din da Amina take.

Bayan shigan su Abba doctor Yayi musu bayani akan cewa zuciyar amina ta kumbura sakamakon abunda ya d'aga Mata hankali tun farko, to yanxu ma abinda ya sanya ta Kara shiga wannan hali,akwai matakan da ya kamata mubi domin ceto rayuwanta,a guji abinda zai d'aga Mata hankali a gaskiya ta shiga yanayin da tashiga yanxu zamu iya rasa rayuwanta,.
Abba ya ce, in sha Allahu zamu kiyaye, sai dae har yanxu ba Ku bamu bamu bayani game dazuban jinin ba?
  Eh!to zuban jini fanin sa dabam, yanxu abinda yafi damunmu shi ne kunburin da zuciyarta Yayi shima jinin in sha Allah zamuyi iya kokarinmu ganin cewa, ya tsaya.
Allah ya yarda,. Musabaha sukayi, suka tafi wurin su Hajiya.

KOMAI DADIN DUNIYA KIYAMA TAFI SHI😭Where stories live. Discover now