7

427 23 0
                                    

🅱 *RILLIANT WRTER'S* *ASSO*🖊

{Pen's of freedom, home exceptional and magnificent writer's}





*KOMAI DADIN DUNIYA!*
   _Kiyama ta fishi_



*Ummerherny Nerserllerh*


*Sadaukarwa*

*SURAYYAHMS*
_OFFICIAL CATTY_🐈










7

Washe gari, nuwaira ta tashi ta fice gidansu Jidda ta sanar da ita yau iyayen, Jamal zasu zo domin Neman aurenta, Jidda sai da taji ba dadi ,take fuskarta ta sauya ta cikin zuciyarta ta ce,tayama hakan zai faru bayan tare muke fadi tashi amma ace yau ita ce za'azo tamabayar aurenta, Kai never karya ne Nuwaira, baki isa ki Bari a titi Ina gantali ba, in kuwa haka ta faru sai dae na kashe Kai na.
Nuwaira ta Lura da shirun da Jidda tayi na wucin gadi, murmushi tayi da ya bayana kyau ta, ta ce ,qawata nasan tunanin da kike, Zan tafi na barki, toh ki sama ranki bazan barki ba, muna tare da ke ,zanso ki sama ranki da zarar na sa kafa na bar gida kema kin barshi, domin xan sanar da Jamal amiki muhali, a kusa damu, saboda muringa jin numfashi juna, kuma Jidda nan da yan kwanaki zakiyi naki miji, Ina son na sami wasu kudi ne a hannuna domin na bawa yarkazuna ya duba mana tauraronki dan naga kamar akwai matsala.
  Hum !Nuwaira kenan ,shin kina ga hakan zai yiwu ?
Sosai ma kin manta waye nuwaira magna daya nake bana maimai tawa.
Nuwaira bata Jamal nake ba yan uwansa, fa, zasu amince da haka?
  Tuni mana yadda Jamal ya bada Kai dole su bada, KO uwarsa ne ,keh tsaya ma, nayi tuya na manta da albasa so nake naje ayimin maganin uwarsa Mai bakar aniya.
Kai kawata baki da dama.
Allah kuwa, so nake naga tana bani girma sama da kowa a danginta, ya zama magnata kawai ake ji, in na ce ayi, ayi in na ce a'a abari .
Haka ne.
  Bayan wani lokaci Nuwaira ta koma gida, Jidda ta nuna hasaddanta a fili bata boye ba.

  Nuwaira ta samu Husna kwance tana hutawa kasancewar yau tayi musu wanki.
Da sallama ta shiga.
Sallamar nuwaira ya bawa husna mamaki, amsawa tayi fuskarta dauke da mamaki, wuri ta samu ta zauna, rabon nuwaira da shiga dakn Inna kusan shekara daya da rabi kenan,ta kebe kanta cewarta karsu shafa Mata kashin tsiya,.
Lafiya Nuwaira?
Lafiya lau, Husna dan Allah Ina so ki taimakeni ki rufamin asiri.
   Name kenan !
Amma Jamal nake son kiyimar abinci, yau yaso ya karba, kinsan matarsa bata gida, toh nikuma kinga ba wani iyawa nayi ba.
Dariya abun yabawa Husna ta ce, Haba yanmata kin ban kunya jibeki fa, mace iya mace amma ba girki, Sam hakan baiyi ba, kinga nagaji bani da lokacin yiwa wani kato girki, yanxu kije kawai ki zuba basirarki.
  Nuwaira taji zafin maganar Husna amma ta cizai, haba Husna bani tunanin Zan nemi Abu a wurinki na rasa, kiyi hakuri ki taimaka kiyimin ba wani Abu Mai yawa bane, sakwara ce da shinkafa sai dankali da zaki soyamin da kwai, nasan a lokacin kad'an zaki gama .
Haka ne ,ga wadda baisan aiki ba, wai tsaya nuwaira a hakan kike ikirarin zuwa gidan miji,kayyahToh, Bari nayi miki karatu duk da nasan ba lalai ne, ki dauka kasancewar bako wane ke da basirar daukar darisi ba, wani KO zaka shekara dubu kana maimaitamar karatu baya ganewa, ki sauke girman kai da kike dashi ki koyi abinda zai fisheki, mace duk wayewar da iya kwarkwasa in bata iya girki ba banza ne,sann!kafin ta karisa ta ce, Husna bafa nazo ki cimin mutunci bane, domin kinsan nafi karfin wulakanci, ina da kudi ki fadi nawa zan baki ,banyi kallan matsiyata ba ,fadamin nawa ne ladanki.
   Dadin abun halinmu ba daya ba, zanmiki domin karai mutuncin Inna kada duniya ta zageta bata koyamiki girki ba,.

Aikin banza kenan,bangaranki ne wannan, ni zaman aure na ,ba aikin gida bazan rugumi aiki kamar jaka ba, keh,da kika ga zaki iya sai kiyi, Husna dae mamaki Nuwaira take ba,.
  Haka husna tayi girki cikin kwaraiwa da tsafta, ta shirya Mata komai yadda ya kamata, nuwaira kuwa anyi kwaliya ta daukar hankali, ko godiya bata yiwa husna ba,
ba a wani jima ba, Jamal ya iso, tafiya take kamar hawainiya, ta isa motarsa, Jamal tunda ya ga fitowar Nuwaira ya bude baki, har ta iso bai sani ba, fura mar iska tayi afuska ya sauke numfashi,.
Motar ta shiga, suka wuce,sosai Jamal ya ci abinci sosai yana santi, kyauta maitsoka ya bata
   Bayan la'asar su Abba suka iso, gaisuwa sukayi da kawu buba cikin mutunci da girmamawa, hira suka sha sosai, kamar yadda shari'a ta shimfid'a haka Abba ya nemi auren nuwaira, ya bada kudin aure 100k  ,Abba ya sanar da bukatar Jamal cikin sati yake so a gama komai,.
Kawu buba ya ce kayi hakuri, Alhaji bamu da kudin da zamuyi hidima a sati kuyi hakuri mu gama shiri, .
Abba yayi murmushi ya ce, Mallam buba kayi hakuri bazanyimaka katsalada cikin sha'aninku ba, matar muke bukata ba kaya ba.
Hmm!kayi hakuri muyi shawara damahaifiyarta.
Sallama sukayi cikin mutunci.

KOMAI DADIN DUNIYA KIYAMA TAFI SHI😭Where stories live. Discover now