Inteesar BOOK ONE
Khaleesat Haiydar
A gajiye ta shigo gidan hade da kullo gate, ta nufi sashin su ba tare da ta kula da mutanen dake tsakar gidan ba, bare ta gaishesu, "lallai
yarinya nan kin rika..." Ta juyo da sauri tare da dawowa da baya tace "kuyi hakuri ban kula bane
wallahi, ina yinin ku?" wata farar mata mai matsakaicin jiki tana linke kayan shanya tayi tsaki hade dacewa "Ai bamu ba, wataran ma haka xaki mance da uwarki, munafuka kawai,
bace mana da gani" ta tsunkuyar da kai takasa wucewa, don ita har ga Allah hankalinta ne baya wajen amma tasan baxata iya fidda kan taba,
Dan haka kawai sai ta kara maimaita "kuyi hakuri" Tabe baki ta xaunen tayi tare da mikewa tace "Banxa Agola kawai" daga haka tayi sashinta ta shige tare da banko kofa, itama farar hakan tayi mata hade da ce mata shegiya tayi nata sashin. Jikinta a mace ta karasa palon nasu ta shiga da sallama, momynta dake kwance tana rike da hisnul muslim, ta dubeta bata ce komai ba ta kau da kanta, ta nemi guri ta xauna tare dace wa " ina yini momy?" momy ta mike xaune tana duban ta tace me ya faru? Ta
kirkiro murmushi tace "ba komai momy" bata sake ce mata komai ba, can tace "ya mai jikin?"
tace jiki da sauki sosai, hajiyarsu tace kila gobema a sallamesu daga Asibitin, momy tace "to Allah
yasauwake, kiyi sallah ga abincin ki can a rufe," tace to sannan ta shiga bathroom tayi alwala ta fito, tana idar da sallan ta jawo abincinta ta fara ci, "momy ina ihsaan?" Momy tace "Taje
kitso" daga haka ta mike ta shiga bedroom dinta, Intisaar
na gama cin abincin ta fita da kwanukan ta dawo, ta watsa ruwa sannan tace wa momy ta
tafi wajen Innah. A hanya suka hadu da Zainab, Zainab ta dubeta tace "har kin dawo daga dubiyan?" eh na dawo daxun nan, ban ma dade da shigo wa gidan ba, tana magana ne tana tafiya,
Zainab tace "wajen innah xaki ne?" "eh can xani me ya faru? Ok kice ta ajiye min dambu na, dan daxu kursum tace min ta siyo dayawa, intisaar tace to kixo muje mana, "aa Hajiya ta aikeni ne" "to shikenan
idan ban manta ba xan karbo maki" xainab ta harareta da wasa tace "xaki gane kuranki ne kuwa
idan kika manta" intisaar bata ce komai ba, ta wuce tana dariya. Cikin gidan innar tasu take, dan babban gida ne na gaske. Tana isa sashin
innar ta ganta xaune a bakin kofar falonta, tana kulla magunguna, intisaar ta hade rai tace"wai
innah bakya gajiya da daure dauren magunguna da kunce kuncen su ne, innah ta hade rai itama tace "to dan gidan ku ba duk dan saboda ku nake yi ba" intisaar ta gyara xama tace "to ina dambuna da na xainab innah?" Da sauri ta juyo tana duban intisaar din tace "oh ni Rahmatu, to yanxu wa yace maku na siya dambu?" intisaar ta tabe baki tace "cinye kayanki innah" sannan ta mike ta shige palon tayi kwanciyar ta. daga waje taji innah na cewa "ina takwarat a?" ta yi shiru kamar baxat a amsa ba, Sai kuma tace "tana wajen kitso," "to meyasa baki kawota nayi mata ba?" intisaar tace "Ke har wani kitso kika
iya innah?" innah bata sake cewa komai ba har ta gama abinda takeyi ta shigo parlon. Sun jima suna hira da inna, har aka kira maghrib ta yi
sallah, sannan ta diba abincin da fadila ta kawo wa innah taci. Ba ita ta bar sashin innah ba sai wajen karfe goma saura, bayan ta dibar wa xainab dambun ta itama ta debi nata, tayi mata sai da safe ta kama hanyar sashin su, duk da tsakar gidan da haske sosai dan ko ina kwan fitila ne,
amma gabanta faduwa yake yi sosai, da sauri ta karaso gida ta bude kofa ta shige tare da kullewa, momy ta dubeta tace " ke da waye haka?"
Tayi dariya tace ba kowa, momy tace "to yayi ki ci gaba" Washegari bayan sun karya ita da kanwarta ihsaan suka je gaida Abba, yana xaune a parlon sa yana sauraren labarai suka shiga, kursum na xaune a kasa ta hade rai, da alama abu take jira. Ya amsa masu yana murmushi, ya
dauki ihsaan yace "mamata yau kin tashi da wuri kenan" sannan ya dubi intisaar yace ke kika yimata
kitso ko inna?" Tayi dariya tace a’a saloon akayi mata, yace "to yayi kyau" ya dubi kursum yace "yauwa
ina jinki" Tace "dama Abba gyaran gashi xanje a saloon, yace nawa ne?" Tace "Dubu biyu ne Abba"
ya xaro ya bata, sannan ya dubi intisaar ya xaro dubu biyun ya mika mata yace "ke ma ki gyara gashin naki, sai kuje tare" tayi murmushi hade da godiya, kursum ta dubeta cikin tashin hnkli da takaici, sannan ta mike tace "ngd Abba" ta fice.
Intissar ta kuma yi masa gdya sannan ta kama hannun kanwarta suka bar parlon. A hanya suka hadu da Hajiya tsaye suna jiranta, gabanta yyi
mugun faduwa, ta daure ta karaso bakin ta na rawa tace "ina kwana hajiya....?" Ido ta xaro mata
tace "ban kwana ba" da sauri Intissar ta mika mata dubu biyun dake hannunta, ta karbe kuwa, sannan tace "bnxa kawai" suka yi gaba da ita dasu kursum, kursum tayi mata gwalo tare da fashewa da dariya, ita dai bata ce komai ba ta kama hannun kanwanta suka yi sashinsu. Ihsaan tace "amma anty ai ke Abba ya ba wa kudin kika
basu?" intisaar tayi mata murmushi tace ai nasu ne dama, sannan ta ja ta suka shige palor. Momy na shara ta karbe ta karasa sannan ta gyara gidan, ta kwaso kayanta tana guga.
Ihsaan na jikin momy suna kallo, tace
"momy, daddy yace kitso na yyi kyau wai" momy tayi murmushi tace "sosai ma kuwa" intisaar tace "nima ae irin shi xanyi" Intisaar tace "to ba kin ba su momyn anty Xainab kudin ba?" momy ta dube intisaar.
YOU ARE READING
Inteeesar
Romance#pride #Obsession #Ego #Step mothers #Funny granny #Khaleesat Haiydar #Love #Foolishness #Romance