Episode 2

5.5K 159 5
                                    

Intisaar....

By Khaleesat Haiydar

Momy tace "wani kudin?" Murmushi intisaar tayi tace "Nima bn san mata ba." Ihsaan tace "Abba ne ya bata two thousand yace tayi kitso shine momynsu khadija ta karbe" momy ta mike ba tare da tace komai ba ta dauki hijab tace "idan kin gama gugan ki dauki kudi ki siyo Cornflakes tun daxu ihsaan take so kuma bbu, ni xanje na gaida innah" ihsaan ta mike tace momy nima xan biki, Momy tace "Eh dama tare xamu ae dauko hijab din ki" daga haka suka fice tare, Intisaar ta cigaba da guganta. xainab ce ta shigo ta dubeta tace "Ina dambuna?" sai da Intisaar ta ja mata rai sannan ta dauko ta bata tana dariya, xainab tace "amma ke kika dibar min ko?" Intisaar tace "Eh nima ga nawa can" Zainab tace "Shi yasa na ganshi dan kadan" intisaar dai bata ce mata komai ba ta karasa guganta ta kashe dutsen gugan ta kai kayan daki, ta dawo ta dubeta tace "yau baxa kiyi kwalliyan friday bne?" Zainab tace "uhum bari ma ki ga, aikena pa hajiya tayi" tana fadin haka tayi hanyar fita, intisaar tace "ina xaki?" "Supermarket!" Cewar Zainab ba tare da ta kalleta ba, Intisaar tace "Jira ni nima xan siyo Cornflakes yanxu" daga haka ta dauko kudin da
hijab suka fita ta rufe kofa. Zainab tace "momy tana wajen innah ne hala?" "yea tana can" hanyar supermarket din suka dauka suna hira. Da kafa suka taka dan ba wani nisa sosai, sai da intisaar ta raka ta gidansu kawarta dake Area din ta karbo litattafai sannan suka kama hanyar gida. Umma suka gani a tsakar gidan ita da 'yar ta Rahmatu tana mata tsifa, intisaar ta gaida ta, bata ko kalla inda take ba bare ta amsa, tana duban xainab tace "ke ba aiken ki hajiya tayi ba kika bi wannan gantalalliyar ku ka je gantali koh?" Xainab ta yatsine fuska ba tare da tace mata komai ba ta nufa sashin su, intisaar tayi sashinsu ita ma da saurin ta.. Tana shiga parlon su ta tar da momy tana shiri xata fita, tace "momy ina xaki?" momy ba tare da ta kalleta ba tace "inda kika aikeni" sai da ta gama shirin ta tsaf sannan tace xasu je dubiya da innah... Wayan intisaar yyi kara ta dauka tana cewa "kar dai har kun dawo samira?" daga can bangaren samira tace "nace maki ae tare xamu, ni ga ma ni a gate din ku kiyi maxa ki shirya" Intisaar tace "Allah kar ki ba kan ki wahala ni bbu inda xani" tana fadin haka ta kashe wayan. Momy ta dube ta "Tace ina xaku?" intisaar tace "wai dole tare xamu gidan Maryam kuma nace masu baxa ni ba" momy tace "wai maryam da akayi bikinta?" Ta gyada mata kai... Momy tace "Aa baki kyauta ba intisaar ayi bikin ta ki ki xuwa kuma yanxun ma kuje gidan ta kice ba xaki ba, ki daure dai ki shirya kuje, amman karki dde, ni na tafi innah tana jirana, ki tabbatar kin kulle min kofa" tace "to momy Allah ya kiyaye" a bakin kofa ta hadu dasu samiran suka gaisa sannan ta wuce. Ba dan ranta ya so ba ta shirya suka bar gidan da kawayenta, suna ta mata tsiyan bbu wanda xai xo bikinta, tta dai murmushi kawai take yi dan bata da lkcn su, karfe sha biyu suka iso gidan maryam, tayi murnar ganin su sosai, amma sai ta hade wa intisaar rai, da kyar intisaar ta shawo kanta, tana dariya, dan tasan bata kyauta mata ba tunda bata je bikinta ba. Ta cikasu da kayen ciye ciye da soft drinks, lkcn sllh nayi suka yi gaba dayan su, sannan ta kawo masu abinci suna ci suna hira. Daga bisanni intisaar ta basu uxurinta na cewar xata wuce gida dan momy bata nan, maryam ta fahimce ta dan hka tayi mata gdyan xuwan da tayi, intisaar ta hada ta da dubu biyu ta amsa da kyar sannan ta bar su samira a gidan ta wuce. A dai-dai gun da xata hau mota ummi ta kirata, ta dauka tana cewa ummi an sallame ku ne, ummi tace "eh yanxu ma xamu wuce gida, ca ma nake xaki xo intisaar" intisaar tayi murmushi tace "to bari na taho ina hanya dan mun je gidan maryam." Ummi kawarta ce sosai da aka kwantar yau kwana uku a asibiti. tana isa hsptl din a gaida nurses dake reception ta haye sama taje ward din da ummin take, cak ta tsaya a stairs din kamar warce aka hankado ta juya da sauri ta fara sauka, bin ta yyi har suka sauka kasa ya maxa ya shige gabanta yace "meye kika gudu 'yan mata, nayi laifi ne?" fuskarta daure tace "a'a" sannan ta juya ta haye sama, jin ya biyota ne ya sa ta tsaya, ya karaso yace "ya kika tsaya kuma?" bata ce komai ba tayi hanyar ward din kawarta yana biye da ita. Xaune taga ummi tana duba Novel, ta karaso, shima ya shigo dakin, gefen ummi ta xauna tana ce mata ya jikin, Ummi tace "da sauki frnd ya su mummy?" Likitan ta kalla tace "doctor dama ka shigo?" yyi murmushi yace "yea, kin warware sosai yanxu ko?" Tace "eh nagode Dr." Yace "no problem wannan kawar kice?" ta dubi intisaar tace "eh" yace "Uhn what's her name?" Ta sake kallon intisaar da tayi kmr ma bata san suna yi ba tace "Intisaar sunanta" yace "Wow.. To me nayi maki intisaar tun jiya kike gudu na?" ita dai bata ce komai ba sai wayan ta da take danna wa, yyi murmushin karfin hali yace "Am srry ina damunki koh" a takaice tace "Ok" sannan ta dubi ummi tace "momy pa?" ummi tace "sun je kiran taxi ita da su falmata yanxu xamu wuce dama" Shi kam juyawa yyi ya bar dakin, intisaar ta dan ja tsaki, ita dai ummi bata ce komai ba. Karfe uku suka bar hsptl din, bayan ummi taje tayi ma Dr faruuq godiya dan yana da kirki sosai, ta kuma maida masa Novels din sa da ya bata take karanta wa, nan ya nemi alfarman ta bashi nmbr intisaar bbu musu ta bashi yyi mata gdya. Har bakin taxin ya rako su, momy ta sake masa gdya sannan ta shiga motar, suka kama hanyar gida. Yau wajen sati uku kenan, kullum sai Dr faruuq ya kirata, wani lkcn ta dauka, wani lkcn taki dauka dan ko ta dauka bashi da wata mgnar da ya wuce ta amince masa, ita kuma yanxu kam ba abinda ke gaban ta ba kenan. Ummi bata mata adalci ba da ta bashi nmbr ta, kuma taje har gidan nasu ta nuna mata bata ji ddin hkn ba. Suna xaune da momy suna kallo da daddare ya kirata, ta mike ta shige daki da sauri dan bata san ta jawo hnkln momyn tata, ta daga kiran, taji yace "intisaar" tace "ina jinka" murya can kasa yace mata " bni da lfya yau, ki mani addu'a kinji" tace "xan maka Allah ya sauwake" yace "nagode sai da safe" tace "tam" Tana fita hanyar kitchen tayi taje ta wanke kwanukan da aka ci abinci a gidan dan momynta ce tayi girki, ko da ta koma palonsu ihsaan tayi bacci, momy kuwa Abba ya kirasu da su hajiya yana masu magana, tana kwantar da kanwarta tayi wanka ta kwanta itama. Washegari bayan sun dawo daga makaranta, taje tayo wa momynta cefane suka shigo gidan tare da xainab ita ma an aiketa, kayanta da ta shanya taga fadila na kwashewa tana xuba su a kasa, xainab tace "meye hka fadila?" fadilar tace "mele" Intisaar tace "meyasa baxa ki kira ihsaan ta kai mun ciki ba fadila" fadila ta jefa mata wani kallo tace "sbda baki isa ba" intisaar tace "shikenan nagode" kursum ta fito da sauri tace "Toh kar ma ki gode mana mahaukaciya kawai" intisaar tace "nagode" sannan ta kwashe kayan nata xata wuce ciki, fadila ta banke ta da gan gan, cakumota xainab tayi tana cewa "ke wacce irin dabbace fadila, wllh sai kin gaya min me intisaar ta tsare maku a gidan nan yau" ko kuwa suka fara yi, sai ga uwarsu ta fito da gudunta, "me ye hka?? Meya faru?" Ta jefo masu tambaya tana kallonsu, kursum da sauri tace "wancan munafukar ce ta hada su fada" Umma bata bi ta kan su ba ta cafko intisaar ta dinga xuba mata duka, intisaae na kuka tace "wllh Umma ni banyi mata komae ba" umma bata saurare ta ba ta dinga jibgar ta kamr an aikota tana cewa "kaji min matsiyaciya, nan din gidan ubanki ne da xaki hada mana yara fada munafuka?" tuni xainab ta cika fadila tana "wai umma me tayi maki ne, dan me baxa ki tambayi
munafukan nn abinda tayi ba" Tana magana ne tana hawaye, sai ga hajiya ta fito da sauri ta cafke xainab tana cewa, "Ai ni yau sai kin gaya min koh intisaar kanwar uwarki ce a gidan nan" kuka xainab take yi, uwar ta watsa mata mari ta jefar da ita sannan ta koma kan intisaar, daga ita har umma sukayi mata tatas, da kyar ta samu suka barta ta shige palonsu tana kuka sosai, momynta na xaune tana yanka alaiyahu parlorn, Xubewa kasa tayi tana kuka sosai, ihsaan ta xauna kusa da ita tana share mata hawaye, momy bata ce komai ba, ta karbi cefanen ta wuce kitchen, tayi kuka sosai har barci ya dauketa. Da magrib momy ta tasheta tayi sllh, ta bata abincin kowa ta kai masa sashinsa, hajiya ta fara kai wa, xainab dake bakin tap tana alwala ta karaso da sauri ta karba cikin sanyin murya tace "kiyi hkuri intisaar Allah xai saka maki" Intisaar tayi murmushi bata ce komai ba ta wuce. Ta dauki na umma ta kai mata, yusuf ta gani bakin kofa ta mika masa ya amsa sannan ta dauki na inna ta kai mata. Tana xaune kan darduma, ta gaisheta, ta dubeta da kyau tace "wa ya saki kuka intisaar?" Intisaar ta sunkuyar da kanta tace "ciki na ne ke mani ciwo" da sauri inna ta mike ta shige ciki ta dauko magani ta jika ta bata tasha tana cewa "Da yake hankali bai ishi uwarki ba ai ido ta xuba maki" ba tayi musu ba ta karba ta sha, inna ta xauna tana ta mita wai cikin ta na ciwo baxa ta xo ta karba magani ba tana san ta kashe kanta, da kyar ta samu ta barta ta wuce sashinsu. Tasan dan inna bata nan ne shiyasa sukayi mata hkn, dan da tana nan bbu wanda xai mata hka. Ko da ta shiga parlonsu, momy bata nan ta kaiwa Abba abinci sashinsa, ta dan ci abinci tayi wanka sannan ta kwanta.Tana xaune tana sama ihsaan rani, momy kuwa na daki taji ana sallama, da sauri ta jawo hijab dinta ta sa dan yar shimi kadai ne jikin ta da xani, sannan ta amsa sllmn tana mikewa daga wajen, ya shigo yana murmushi yace ihsaan lalli ake yi, tace "eh" uncle sannu da xuwa" ya dubi intisaar yace "yauwa kanwas ya momy pa" sai ga ta ta fito tace "Haisam yaushe a garin" yyi murmushi ya durkusa ya gaisheta, yace "da safe naxo momy amma bn dde da shigowa gida ba" tace "ayya to ya hanya?" Yace "Alhmdllh" ita kuwa intisaar ta mike ta kawo masa ruwa ya amsa ya sha yana gdya, suna hira da momy sai ga kursum, ta shigo ba ko sallama babu tace "yaya umma na kiranka" kallonta yyi "yace baki iya gaisuwa bne?" turo baki tayi tace "ina yini" sannan ta fice, ya bita da kallo ya kasa cewa komai, ya mike yyi yake yace "momy da daddare xan xo muyi hira" tace "to Haisam Allah ya kaimu" ya dubi intisaar yace "kanwata naga sai fresh kike yi meye sirrin kuwa" tayi dariya tace "kai yaya har da sharri" yyi dariya yace "da daddare kije wajen inna musha hira" tace "to yaya Allah ya kaimu" sannan ya fice da sauri dan ya riske Kursum amma har ta shige gida.

InteeesarWhere stories live. Discover now