Episode 3

4.8K 138 6
                                    

Yana shiga umma  ta balbale sa da masifa, ita fa bata san shige shige da gantali daga xuwan sa ko hutawa bai yi ba har yaje yawo, yyi dariya yace "yau naga ikon Allah, bnda ikon xuwa wajen matar Abbana" ta hade rai tace "A'a uwar ubanka, ba matar ubanka ba, wllh ka fita harka na haisam" Mikewa yyi yace "to Allah ya kyauta" daga haka yyi sashinsa yana waige-waigen inda xai ga Rahma amma bai ganta ba. Da daddare Intisaar suka hadu da yaya Haisam a sashin inna,  Hira suka yi sosai tun suna yi da inna har ta bingire a wajen tana barci, Intisaar ta dinga dariya yace "to karki
tashe ta mana kanwa little sis" ta rufe bakin tace "to na daina yayana" Yace "to yanxu samarin ki nawa?" Tayi dariya sosai tace "ko daya yaya" yace "kin maidani yaro ko?" On a serious note tace "lahh haba yayana wllh a'a" yace "to gaya min gskya" tace "Allah yaya bana kulasu" yace "to ki daina hka, wataran Abba xai ce ki fito da miji, idan kuma baki da, xai iya hadaki da wanda ran sa yaso dan hka, ki dai-daita da mutum daya, kuma bance wai ki tara samari ba" murmushi tayi tace "to yayana" a hka ya rakota har sashinsu yyi mata sai da safe. Ta fito daga wanka kenan wayan ta yyi kara, sai da ya katse aka sake bugowa sannan ta dauka, "intisaar" taji ya kirata, ta amsa, yace "ya gida?" Tace "lau" yace "Uhn to yyi kyau, dama na kira ne na gaidaki bye...." Ba shiri ta samu kanta da ce masa "ya jiki?" Yyi jim sannan yace "da sauki Alhmdllh" tace "to Allah ya sauwake" yace "ameen ngd" sannan yyi mata sallama ya katse wayan. Washegari da ta dawo daga makaranta sai ga mis cals dinsa, ta dauka tana kallon wayan, samun kanta tayi da dialing din nmbr, ba tare da ta shirya ba, bayan wani lkci ya dauka, suka gaisa, kame-kame ta fara yi tace "Emm dama mis cals dinka na gani da" yace "hmm, yeah na kira ki daxun" tace "ok naje makaranta ne" sai tayi da ta sanin kiran sa ma, ta dai dake dai tace "ya jikin" yace "Alhmdllh" tayi shiru, can dai tace "to mene ya sameka?" yace "Uhn... bari na kira ki, na manta you called" Yana katse kiran nata ya kira ta yace "Sorry intissaar" shiru tayi bata ce komai ba, yace "It's stomachache" tace "Allah ya sauwake.." Yace "Ameen ngd." A hankali taji ya kira sunan ta, ta amsa tana sauraren sa, "ki bani ixini naxo gidanku mana" da sauri tace "a'a kar ka damu, kaga bye... Yanxu
ina aiki ne, sai anjima" tana kai wa nan ta kashe wayan. Ta xauna tayi jim tana tunanin abinda ya Haisam ya gaya mata jiya, ihsaan ce ta shigo tace "Anty, inna tace na kira ki" tace "to" tare da mikewa ta dau hijab, sai kuma ta tuna bata cire uniform ba, ta cire, sannan taje kiran da innah ke mata. Rahma da khadija suna wankin uniform dinsu a bakin tap, suna ganin ta sai suka tare hanyar wucewa, ta dan yi jim a wajen, sannan tace
"ku gafara xan wuce" Rahmatu tace "idan anki pa?" khadija ta kara da cewa "ko gidan ku ne nan din?" ita dai bata ce komai ba sai kallonsu da ta tsaya yi, kumfar wankin Rahmatu ta debo da yawa ta yar fa mata a fuska, ihsaan ta xo da gudu tana cewa "me tayi maku?" khadija ta tura ta har sai da ta fadi, intisaar ta kalle ta cike da bacin rai tace "ita kuma me tayi maki khadija?" Ihsaan kuwa tuni ta mike tana kuka ta cire talkamin kafarta tana dukanta dashi, daukar ta khadija tayi a fusace ta tsoma ta cikin guttern dake wajen, intisaar bata san lkcn da ta fixgo khadija ba ta dinga dukanta har ta jefa ta cikin kwatan ita ma a fusace, da gudu rahmatu na kuka da ihu taje ta kira hajiya da umma, dan suna kusa da gate a xaune suna hira. A hanxarce kuwa suka karaso wajen, hajiya ta fara ciro 'yar tata daga ciki kwata tana salallami tace "mai xan gani hka?" umma kuwa ta cafko intisaar din da ta juya da sauri xata bar wajen, dukan fitar hnkli ta shiga yi mata da duk karfinta, hajiya ma ta xo ta sa hannu suna xaginta, kuka ihsaan ta dinga yi tana kwalawa momyn su kira, sai ko gata ta fito, tsaye tayi tana kallonsu bata dai ce komai ba, can ta juya ta wuce abin ta, su fadila da kursum duk sun fito, hka aka dinga hayaniya, duk suna xagin intisaar "wllh sai naga bayan ku da
uwarki a wannan gidan, shegu munafukai kawai, tunda Ku ka shigo gidan nan muke...." Muryar inna
da suka ji ne ya katse su, sai ummah dake taunan cingam, sake baki inna tayi tana kallonsu, "me xan gani haka Aisha?" cewarta kenan tana duban Hajiya baki bude, cikin halin ko in kula umma tace, gata nan ki tambayeta mana, hajiya ta maxa tace "kashe min 'ya xata yi da har xata danne ta tana duka?" inna ta dubi intisaar dake ta faman rusa kuka ita da ihsaan, tace "Ai ni na shiga uku na sani, yanxu me 'yar nan tayi maku da har xa kuyi mata taron dangi haka
Har da gore gore ina ji?" Durkushewa gun inna tayi nan ta dinga rusa masu kuka har da tari ,daga hajiyan har umma sai tabe baki suke, hajiya tace "to inna d'a yafi d'a ne?" sunan momyn intisaar inna ta shiga kwalawa cikin kuka tana cewa "zainabu, zainabu...." da sauri momy ta fito tana cewa "na'am inna?" inna ta sharbe majina da habar xaninta tace "ke wai wace irin sha-sha sha
ce, ynxu kina ciki ana neman kashe maki ya'ya har biyu kika ki fitowa? To Allah ya isa, kuma wllh yau komai xai xo karshe" ta fadi hakan tana kallon hajiya da 'ya yansu gaba daya, Zainab ce ta karaso da sauri dan dama bata gidan, tana cewa "inna me ya faru?" inna ta ciro wayar ta da sauri
ta mika wa xainab tace "maxa ki lallubo min number Abubakar" jiki na rawa zainab ta saka nmbr Abbansu tayi dialing ta mika wa inna, inna ta karbe da sauri ta kai kunne "Abubakar maxa ka dawo gida yanxun nan, ko ma ina kke ina jira" a fusace tace "A'a ba ruwana, idan ka xo dai xaka gani" daga haka ta mika wa xainab wayar tace "kashe min kayana ke" daga haka ta kamo hannun intisaar ta wuce sashinta da ita ihsaan na biye dasu. "Tab!" Cewar hajiya knn cikin tashin hnkli, Wato yanxu hadasu tayi da Alhaji sbda wannan Agolan, lallai akwai sake, nan xainab ta barsu tsaye ta wuce, momy kuwa tuni dama ta koma sashinta, ummah ta dinga gyada kai tana cewa "yau mun ga ikon Allah agola ta fi masu gida" nan suka dinga sakar wa momy habaici da maganganu marasa dadi, ita dai bata tanka ba tana daki abinta, Haisam ya shigo gidan yana duban su, mamaki bayyane fuskarsa yace "Umma me ya faru" hajiya tace "agola ce tafi ya'yan masu gida, yau kam mun ga ikon Allah" girgixa kai yyi ya bar wajen kawai, ya samu xainab tana kwashe kayanta a igiya, nan ta gaya masa abinda ya faru, sai kawai yyi sashin inna, tana xaune sai rusa kuka take tana Allah wadai da matan Abubakar, dan ko ita basu ganin girmanta, kuma yau tasu ta kare
a gidan nan, intisaar na xaune ta xubawa TV ido, dan ita bata ga abin kuka a nan ba da inna xata dinga yi, ihsaan kuwa na lullube da towel alamar wanka tayi, haisam yyi sallama ya shigo bata jira ya xauna ba ta dinga jero masa abinda ya
faru tana shessheka, sai ka rantse tana wajen, hkuri ya dinga bata, amma kmr yana xugata, dan hka ya juya ya dubi intisaar yace "ki yi hkuri intisaar idan Abba ya dawo xasuyi bayani" da sauri inna tace "Kai sake kira min Bukar din, ko abinda yake yafi kiran nawa ne, a lkcn Abba ya shigo gidan da motarsa, haisam yace "to gashi can ma ya dawo" tashi tayi da sauri taje ta same sa parking lot, haisam ya girgixa kai ya mike ya dauki ihsaan yace "srry kinji bby, yau nasan ai Abba sai yyi masu bulala tunda suka tabo mamarsa" dariya
kawai ihsaan tayi, sai ga Abba da inna sun shigo, haisam ya mike ya bar parlon bayan ya gaida abban nasa, intisaar xata tashi inna tace "dawo ki xauna uwar ki xata daura kan bayanin da xan yi" intissaar ta koma ta xauna, nan inna ta fara jawabin ta tana matsar kwalla, ya ma rasa mai xai ce, kawai ya mike, yace "ina xuwa baaba" daga haka ya fice, sashin
hajiya ya nufa direct, ya dinga kwada mata kira, Aisha, Aisha, tace "na'am Alhaji" sannan ta fito da sauri tana cewa lfya kke kwada min kira hka, yace "maxa ki bar gidan nan ki tafi gidan ku, dan ban aure macen da xata sa mahaifiyata kuka ba" bai jira cewar ta ba, yyi sashin Shafa, wato umma, ita ma ya gaya mata hkn sannan yace duk wanda ya dawo ya samu bai tafi ba to a bakin aurensa, ya juya ya koma wajen inna, hka ya dinga bata hkuri sannan ya tabbatar mata da duk sun tafi gida, nan inna ta samu natsuwa dan ita kadai tasan irin wlkcn da matan nasa suke mata, da kuma yanda suka sa xainabu da yaranta a gaba, sai da ya tabbatar ta hakura sannan ya dauki ihsaan yyi hanyar sashin su intisaar din, intisaar
ta mike taje tayi wanka a bayin inna, ko da ta fito suna xaune da haisam tana tayi masa mita yana saurarenta, intisaar tace "Inna me dai kin cika mita" inna tace "nayi din" sannan taci gaba daga inda ta tsaya da kyar haisam ya samu ya lallaba ta ya bar mata parlon, Abba kuwa ya kira su kursum da khadija gaba dayan su yyi masu ta tas, sannan yasa su kneel down a tsakar gidan, sai da ya tabbatar mahaifiyarsa ta sakko sannan ya koma office, Su Aisha da Shafa kuwa tuni suka bar gidan dan sun san Alhaji baya magana biyu.
Washegarin ranar suna xaune ita da xainab Dr faruuq ya kirata, taki daga wa har sau biyu xainab tayi mata mgna sannan ta daga, Suka gaisa, tayi masa ya jiki, yace "jiki da sauki intisaar, ya su momy?" tace "lau suke" yace  "ohk.. Ina kofar gidanku..." A dan firgice tace "me?" yace
"eh" hade rai tayi tace "Kaga bna san hka malam ka rabu dani dan Allah" daga haka ta katse wayan da sauri. Xainab tace "waye?" intisaar tayi tsaki tace "oho nima ina na sani, wai wani gashi a kofar gidanmu sai kace na gayyato sa, wllh xan bata ma ummi rai ne, ni ta daina min shisshigi," xainab ta mike hade da tabe baki ta dauki hijab, intisaar tace "ina xaki?" bata ce komai ba har sai da ta isa bakin kofasannan tace "ina xuwa na mance Hajiya ta aikeni" sannan ta fice. Kofar gida ta nufa, bakin gate ta tsaya tana waige-waigen inda xata hango bakon intisaar din, har dai ta hango sa jikin wani flower yana tsaye yana danna wayarsa, ya daga kai yana kallonta.... Nan ta gane shine bakon, dan da alama wani yake jira, tace "kai ne faruuq wai?" ya dubeta da kyau yace "eh ni ne" tayi murmushi tace "toh bismillah wai ka shigo" yace "to ngd sosai" tare da bin ta har cikin gidan nasu, tayi masa iso har sashin inna. Inna na xaune tasa TV a gaba wai tana kallo, xainab tayi sallamah ta shiga tana cewa "inna kin yi bako," inna tace "waye?" xainab ta xauna gefenta tana yar dariya tace "saurayin intisaar ne, wai kunyar kawo maki
shi take yi" da fara'a sosai inna ta tarbe sa tana washe baki, ta bude fridge ta kawo masa ruwa da lemo tana sa masa albarka, hkn yyi ma faruuq ddi sosai ya dinga godiya, nan dai inna ta dinga jan sa da hira tana basa lbrin Intisaar, xainab kam sai dariya take yi, ta mike da sauri ta bar su tayi sashinsu intisaar, intisaar tana xaune tayi shiru, alamar tana cikin damuwa, xainab tace "me ya faru?" Ajiyar xuciya ta sauke tace "wllh xainab ni bna san walakanta wannan mutumin amma yasani gaba..."
Xainab tace "to kuma meye abin damuwa bayan kin koresa?" intisaar ta tabe baki tace "bbu!" Xainab tace "Toh kin gani, inna dai tace na kira ki tana jiran ki" xainab na kai wa nan ta fice ta bar mata parlon. Jikinta a sanyayye ta dauki hijab tayi sashin inna, tayi sallamah, inna ta amsa da karfinta har abin ya ba intisaar dariya, ko yau farin cikin me inna take yi hka? Duk da takalmin da ta gani bakin kofar inna bata kawo komai a kaba, dan a tunaninta ya Haisam na ciki ne, tana shiga palon tace "ya Haisam ka min promise kayi failing kuma" Cak ta tsaya ganin faruuq xaune a parlon, kanta ya dinga mata wani juyi ta kasa daina kallonsa, ya dago kai yana duban ta kawai ba tare da yyi mgna ba, dakin inna ta shige da sauri, inna tace "Shashanci, yo kunyar me xaki ji kuma?" Sai kawai ta fashe da dariya" intisaar taji wani takaici ya lullubeta, yanxu xainab ta kyauta mata knan?
Sa ta tayi taje wajenbsa bare har ta shigo dashi gidansu kuma ma wajen innarta, sallaman ya haisam da taji ne ya sanya ta kara rudewa, inna kuwa sai xuba take ta wa faruuq, shi ma ya biye ta suna ta yi, inna ta amsa wa haisam sllma ya shigo, tana wangale baki tace "haisam wannan saurayin intisaar ne yaxo gaisheni," haisam ya kallesa da mamaki suka gaisa da fara'arsa, sannan yace "to ina intisaar din inna?" inna tayi dariya tace "wai ita kunya tun daxu ta shige daki" haisam ya kirata ta fito gabanta na
faduwa ta nemi gefen inna ta durkusa tana gaishesa, ya amsa yana daria yace "waye wannan?" ta kalli faruuq tace "nima ban san shi ba" dariya haisam yyi yana kallon inna, shi
kuwa faruuq yyi murmushi ya dukar da kansa kawai, hka Haisam ya ci gaba da xolayarta amma ita hnkalinta na waje daban, tunani kala kala ya kasu a ranta, da daga kai ta dan saci kallon faruuq din suka hada ido ta kauda kanta da sauri, hka suka ci gaba da hira gaba dayan su amma bnda ita da ta kurawa plasma ido. Wayan haisam da yyi ring ne yasa inna ta dakatar da surutunta tana tambayan sa waye, saranta knan, da taji wayarka yyi ring xata tambayeka waye da saurinta, yace mata mijinki ne, sannan ya daga, bai jima yana mgna ba suka yi sallamah ya kashe wayan. Inna tace "Aliyu ne ko wa? Yace "eh shine" inna ta girgixa kai tace "oh yaron nan bai da kirki, halin ku ba daya ba da nashi, bai da kirki ko kadan, bai yo halin Bukar ba, halinsa sak na uwarsa... Haisam ya maxa ya katse ta yace "to xabiya, ni xanje GRA ne ynxu sai na dawo" tace
"to... Amma me Aliyun yace mka yanxu? Yaushe yace xai dawo,? yana ina ne yace mka? Kode yana hanya ne?" Cike da haushi Haisam yace "kai ni inna ban sani ba, ca yyi na gaida inna Rahmatu kawai" sannan ya mike suka yi xchange din nmbr da faruuq, yyi masu sallama ya fice, intisaar ta mike da sauri tace "inna bari na rakasa gate ina xuwa" inna tace "to kiyi maxa maxa ki dawo" tace "to" Sannan tabi bayan haisam da sauri.
Haisam ya dubeta yace "saurayin naki ya hadu intisaar" ta ce "bna so yayana, ni ba ni na kawo sa gidan nan ba" yyi dariya yace "bnda karya dai kanwata" nan ta marairaice masa
Tayi masa bayanin yanda suka hadu da faruuq Har xuwa yau da ya xo, yyi dariya sosai sannan yace "to amma kanwata naga ai bai da aibu kuma yana da hankali, ki dan basa dama mana" ita dai bata ce komai ba har suka iso gate sannan Ya dubeta da kyau yace "kar fa ki ki komawa kanwata, kinsan dai walakanci bai da kyau, ki basa dama ku saba" tace "to yaya baxan gudu ba baxan koma" yace "yauwa kanwata gud of you"
Nan su kayi sallama ya wuce ita kuma ta koma Sashin inna. Suna hira har lkcn, ta nemi gefe ta xauna, tana jin su kawai sai dai tayi murmushi. Sai
Wajen karfe shidda yyi sallama da inna, ya bata kudi mai yawa, ta karba hannu bibbiyu tana godya, hkn yyi mugun bata wa intisaar rai, kamr warce ke jira maimakon tace ya bar shi, har bakin kofa inna ta rakosu sannan ta koma ciki tana masa Allah ya kiyaye hanya baki har kunne. Suna tafe ne bbu wanda yace komai, can dai ya dubeta yace "ngd intisaar" "bani ce xa ka ma gdya ba" ta fadi ba tare da ta kallebsaba. Yace "to waye?" Bata kallesa ba still tace "xainab" yyi murmushi yace "gskya ne" bbu wanda ya sake mgna a cikinsu har suka isa gate sannan ya dubeta ita ma ta kallesa, sai ya sakar mata murmushi , ta sunkuyar da kai da sauri, bata
san lkcn da itama tayi murmushin ba. Yyi ajiyar xuciya yace "to kira min xainab din muyi sallama," tace "aa dare yyi ka bari sai wani lkcin"
yace "ba nan gidan take bane?" Ta kallesa tace "eh nan take amma ynxu ta shiga gidansu." Yace "Toh shikenan intisaar i am vry grateful, ngd sosai" ta gyada masa kai kawai sannan ya juya ya fice, ta bisa da kallo, ya juya suka hada ido kunya ya kamata tayi saurin rufe gate din sannan tayi sashinsu. Gabanta yyi mugun faduwa ganin su Kursum labe ta window suna lekansu, da sauri tayi sashinsu ta bude kofa ta shige. Ko da ta shiga ta tarar Momy bata ciki, tayi hanyar kitchen, ta ganta da xainab Suna raba abinci, taimaka masu tayi suka gama
A tare, ita ta kai ma inna nata, xainab kuwa ta kaima su kursum nasu, intisaar bata ce da xainab komai ba, itama xainab din haka. su hajiya kam yau kwanansu uku basa gidan, xainab bata damu ba, hka ma haisam ko a jikinsa, su kursum dai ne hankalinsu a tashe, momyn intisaar tayi kkrin shawo kan Alhajin amma hkn bai yiwu ba, inna kam ko a gyalenta, dan gidan ma sai yyi mata ddi a cewarta. A kwana a tashi intisaar suka shaku da faruuq sosai, fiye da tunaninta, faruuq mutum ne mai kirki da fara'a, duk gidansu an sanshi dan duk jumm'ah sai yaxo gaida inna sannan ya shiga ya gaida momy. Su fadila da su kursum kam bakin ciki kmr xai kashe su, gashi yau wajen sati uku knan Alhaji yaki barin iyayensu su Dawo. Intisaar ta samu kwanciyar hnkli sosai a gidan dan bbu mai takura mata ynxu, yawanci Idan faruuq yaxo gidan tare suke xauna wa har da xainab suyi ta hira, a wajen momynta kuwa bata da hiran da ya wuce na faruuq, hka ma a wajen
inna. Abba kadai ne bai san dashi ba a gida, amma har su Hajiya da umma da basa gidan 'yayansu sun kirasu sun fesa masu. Yau ma kmr kullum faruuq yaxo gidan su da yake Friday ce,
wajen karfe shidda ta rako sa xai wuce suka iske fadila da khadija a kusa da gate a tsaye, duk da sun gansu amma basu yi kkrin matsawa
daga gate din ba, faruuq d lai bai ce komai ba dan tunda yake shigowa gidan basu taba bude baki
sun gaishesa ba, shima bai taba masu magana ba duk da ba ma gane su yke yi ba, bayan ga xainab. Da kyar intisaar ta iya cewa "ku gafara dan Allah" ganin sun kusa minti uku a tsaye kuma sun Ki barin hanyar, "ke din a su wa?" Khadija ta jefo mata tambayr, tayi shiru bata ce komai ba, khadija ta kara da cewa "nan gidan ubanmu ne dan hka ba ki isa kixo ki mana iko dashi ba" "sai ki bari idan kin samo ubanki sai kiyi iko da gidansa idan ma yana da kenan" fadila ta fadi a walakance tana girgixa kafa, kuka ta sakar masu a wajen, faruuq kam kansa ya daure, ya ma rasa me xai ce, khadija ta dube sa tace "Bawan Allah kana bani tausayi wllh, ga ka kyakkyawa mai asali, amma ka rasa warce xaka bige da nema sai warce har yau ba a san ko yar gidan uban waye bace, yar tsintuwar innar mu, da sauri intisaarvta juya ta bar wajen" ya bita da kallo, bakinsa yyi masa nauyin kiran sunan nata ma,
fadila taci gaba tana kallonsa "ita ba yar kowa bace, kai ba a ma san ko tana da uba ba, sannan ta samu wajen fakewa a gidan mu ita da uwarta sai su dinga mana isa, yau wata daya da sati biyu kenan da suka sa Alhaji ya Kore iyayenmu a gidan nan sbda ita da uwarta," khadija tayi tsaki tace "ai basu ga komai ba ma tukunna, sai suma sun bar gidan nan kmr yanda sukasa aka kore uwata" fadila tace "nima hka" sannan suka bar wajen gate din suka shige cikin gida xuciyarsu pal murna. Sai da faruuq yyi kusan minti biyar a wajen a tsaye, sannan ya bar gidan jikinsa a sanyayye.. Momy ta dube Intisaar dake ta faman kuka tun da ta shigo a karo na farko tayi mata mgna "me ya faru?" ta girgixa kai tana goge hawaye, cikin kuka tace "momy wai ni ki gaya min ran da xan ga abbana, na gaji da gorin da ake mani" hawaye ya ciko idon mahaifiyar tata, tayi kokarin gogewa da sauri tace "me kuma yafaru?" Cikin kuka me tsuma xuciya intisaar ta koro mata duk abinda ya faru, momy ta goge hawayen idonta tace "kiyi hkuri intisaar, wataran sai lbri"

InteeesarWhere stories live. Discover now