Episode 4

7.5K 269 64
                                    

Momy ta mike tace "sai kiyi ma faruuq din bayanin komai" daga haka ta shiga dakinta. Bayan faruwan hkn da wajen kwana uku faruuq bai ce mata komai ba har lkcn, iyaka dai ya kira ta suyi hira a waya. Ranar wata laraba yake ce mata yana so su hadu gobe da daddare a kofar gidansu, bata yi masa musu ba tace "Allah ya kai mu" amma fa sai da taji gabanta ya fadi dan tasan baya xuwa gidansu sai ranar juma'ah. Washegari da ya kasance ranar alhamis ta gayawa
Ummanta yanda suka yi dashi, tace "shikenan, amma karki boye masa komai intisaar" tace "to momy" sannan ta wuce sashin inna ta taya ta aiki. Koda wasa bata gaya wa inna abinda su fadila suka yi mata ba, ta bar shi a xuciyarta kawai. Da yammacin ranar wajen karfe bakwai da minti goma faruuq ya iso gidan nasu, ta nemi ixini gun momynta ta fita bayan ta ce mata kada ta dade kar Abba ya sameta a waje. Yana xaune kan dakali, ta karaso wajen sa, ya sakar mata murmushi, tun kan ta karaso wajen Kamshin turarensa mai ddi ya doki hancinta, ta kallesa hade da sunkuyar da kai, ya mike yana mata sannu da xuwa. A hankali ta gaishesa, ya Amsa yace "ya momy da inna?" tace "suna lfya" sannan ya xauna ya nuna mata gefensa, ta dan yi jim, kmr mai naxari sannan ta xauna. Shiru bbu wanda yace komai, can dai ya katse shirun yace "u knw i luv yhu my Intisaar" ta rufe fuskarta kawai bata ce komai ba, ya kalli fingers dinta yace "ring din waye wannan?" tace "na xainab ne" yace "ita ta baki knn?" "Uhm ko kana so ne?" Ta fadi tana kallonsa yace "Aa da dai naki ne" tayi murmushi kawai bata CE komai ba. "intisaar" taji ya kirata a hankli, tace "na'am" a sanyaye, yace "Lbrin rayuwarki nke so ki bni yau, kinga na ajiye komai aside na xo, dan naji tarihin intisaar dita" ta kirkiro murmushi kawai bata ce komai ba. "Bismillah if u re ready" tace "uhm to ta Ina xan fara?" yace "ko ta ina ma Intisaar," nan da nan taji hawaye ya ciko idonta sannan ta fara ba tare da bata lokaci ba. "Ni sunana Fateemah Umar faruuq" Ya xuba mata ido yana kallonta, can dai ya sakar mata murmushi ya gyada mata kai alamar ta cigaba, ta cigaba ba tare da ta kallesa ba, "Na taso ne a Zoo road nan kano da mahaifiyata, tana yi ma wata aiki lkcn ina da shekara hudu, momy tace min a nan gidan ta haifeni in da take aiki, dan ta fara aiki da sati biyu ma ta haifeni. Inna ita ce warce ummata ke yi ma aiki, da farko dai ni na taso a tunanin inna ce ta haifeni, amma daga baya ita da bakinta ta kan ce min na daina damunta ga mamata can, a hankli dai na gano wacece mahaifiyar tawa, inna mutumce mai kirki sosai, ko sau daya bata taba walakantamu ba, ta dauki ummata kmr ita ta haifeta, ni kuma ta daukeni jikarta. A kwana a tashi inna ta sani a sch, lkcn har na isa primary 5, watarana a sch aka ce mana kowa yaxo da babansa xa'ayi PTA meetin, duk sanda xa ayi irin wannan meeting din momy ce ke xuwa min, amma muna shiga aji sai wata classmate dita maimuna tace min "intisaar ke kina da Abba ma kuwa? Bamu san babanki ba, mu babanmu xai xo gobe." Tun da nake ban taba kawo mahaifi a rai ba sai rannan, sai naji ba ddi ganin yanda kowa ke dokin babansa xai xo, na kagu mu tashi naje gida a gaya min inda babana yake, dan ba'a taba min maganarsa ba, ina isa gida kuwa da tambayar da na tari momy kenan tana wanke wanke, naga confusion bayyane a fuskarta sosai, inna ta fito da sauri tana cewa "waye ya aiko ki?" Nace "gobe aka ce mu kawo babanmu a makaranta" inna ta ja ni ta shigar dani dakinta tace "ki kwantar da hankalin ki yarlele ta, gobe uwarki xata je" nan na fashe mata da kuka nace ni dai babana ne xai je ba mamata ba. Inna ta hassala tace "to ba mu san inda babanki yake ba, mahaifiyar ki na tsince ta a titi ne ranar na dawo daga gidan aminiyata, tana da cikin ki lkcn, a sume muka kai ta asibiti mu da bayin Allahn dake wajen, bayan kwana biyu ta farfado, cikin bayin Allahn da muka kawota asibiti ni da wata baiwar Allah kadai muka rage, dan sauran duk sun tsere
da washegarin ranar ana sallamota na kawo ta gidana. Ita kuwa talatu, sunan matar kenan da muke ta sintiri da ita a asibiti, na nuna mata xan kula da mahaifiyar ki xainab, dan itama ta damu kwarai da gaske, to kin ji dalilin ganin ki nan gidan da ki kayi, inna ta ci gaba tana kallona, bayan satin ta daya naga tawarware sosai, nake tambayar ta ita wacece" Shiru intisaar ta dan yi kafin tace  "Nan momy tavbawa inna tarihin ta, tace daga Misra taxo nan Nigeria, mijinta ne ya bar ta wajen wata tara knan bata san in da yake ba, sbda Bakin cikin hkn ne ya sanya ta baro Egypt, ta dawo Nigeria, ta sanar da  inna tana da kishiya amma ba tare suke ba, to bayan sati daya inna tace ummata ta haifeni a nan gidan nata, d'an ta tasa ya yanka min rago aka sa min fateemah, murmushi ta d'an yi tace "Da yake lkcn ba wani wayo gareni sosai ba ban wani nuna damuwana da labarin inna ba, ni dai jin ta kawai nake. washegarin ranar inna ta kira d'an ta muka je meeting din makarantar tare. Inna ta mana abinda ko na jininmu ba lallai ya mana ba, inna ta tausayawa mahaifiyata sosai, duk da dai a lkcn duk wannan abun da take ba da san ran d'an nata bne, dan baya san yanda inna ta makale mana daga ganin mu ba wai sanin mu tayi ba kuma ta yrda damu, amma ta nuna masa bai isa ya hanata abinda tayi niya ba. Lkcn ina da 5 yrs inna ta tilasta ma d'an ta yyi mana visa muka je egypt nemo mahaifina har da ita. Da kyar ummata ta iya gane gidan abban nawa, amma koda suka je, sai suka ga wai stepmum dita ta saida gidan don duk takardun na gunta dama, hka muka sake dawowa Nigeria hankalin momyna a tashe, inna ta dinga kwantar mata da hankali tana cewa wataran abbana xaixo gareta, wannan ba komai bne illa aikin asiri da muguwar abokiyar xaman tata tayi kawai. Tun daga lkcn inna ta dauki ummata kmr yar ta, Ta nemo wata yar aikin daban dan yanxu wai munvxama yan gida sai abinda baxa a rasa ba kadai momy ke mata, inna da ta tashi sani a makaranta sai ta sani a mkrntar kudi, Abba na biya, ummata gani tayi kmr inna ta daurawa dan nata nauyin mune, dan shima yana da nasa iyalin, dan lkcn matansa biyu da ya'ya shidda, hkan yasa momy tace wa inna ta barta dan Allah ta nemi wani dan aikin da xata dinga yi, inna ta nuna bacin ranta sosai, tace momy kar ta sake mata hka, bbu ruwanta da lamarinta da na d'anta dan tsakaninsu ne, sau dayawa duk bayan sati biyu sai jikokin inna sun xo gidanta, ba karamin tsanata sukayi ba baya ga xainab dake sona sosai, kuma dama sa'a ta ce, na sha hantara wajensu da na iyayensu, basa sona da momyna, sun tsanemu, bn san ko dan muna cin arxikinsu bne, Abban nasu kuwa tun yana d'aure mana da, har dai ya sake sbda yanda yaga mahaifiyarsa ke sanmu sosai. Ya maida ni kmr y'ar sa, komai yyi ma yayansa sai yyi min nima. Tun asali dama yaya haisam yana ji dani sosai, ya daukeni tamkar kanwarsa kuma yana girmama mahaifiyata. Ina da shekara 12 lkcn ina jss2 inna ta hada auren mahaifiyata da danta, wato Abbansu Haisam. Ba karamin tashin hnkli momyna ta shiga ba dan babana bai sake ta ba ai, inna ta dinga mata jaraban wai ynxu kusan shekara 13 kenan tana jiran wanda kila yanxu ya mace, kuma ma ai a musulince ya halatta tayi aure tunda ya dde rabon da ta gansa ko sanin inda yake. Haka nan inna tasa Alhaji Abubakar ya aure ummata, Shi bai nuna abin ya dame sa ba, dan duk abinda mahaifiyarsa take so shi yake yi. A hka ni da momyna muka koma gidansu dake shagari qtres, wato wannan gidan na yanxu... ta dan yishiru sannan taci gaba ganin yanda faruuq ke kallonta "tun daga ranar har yau ni da ummata bamu samu farin ciki ba gidan nan, sai gun Abba da inna, sai kuma xainab da step brother dinta Haisam, sun tsane mu, basa son mu, sun takura mana, kuma har yau basu taba shiri da ummata ba, ita kuma tun da take basu taba mata abu ta tanka masu ba, shiyasa har gobe Abba ke alfahari da ita kuma yana ji da ita, momyna tana da hkuri sosai da kauda kai akan abu. Ihsaan kadai momy na ta haifa a nan gidan, bayan nan bata sake haihuwa ba, yanxu ihsaan shekaran ta kusan 6 knan. Sbda irin yanda suka samu gaba ne ya sanya inna ta sa abba ya gyara mata sashinta na nan gidan ta dawo, dan dama can yayi-yayi da ita ta dawo nan da xamavdan ya kula da ita da kyau amma taki dan ba girmama ta matan nasa ke yi ba. Hkn ya karawa momyna tsana a wajensu hajiya, dan inna ta fi fiffitata a kansu, kuma tafi son ni da ihsaan kan ya'yansu, a makaranta daya muka gama sec sch da xainab, fadila da kursum, khadija da rahma kuwa suna ss2 ne ynxu hka. Hajiya Aisha ita ce matar Alhaji ta farko, ya'yanta uku, yaya Aliyu, xainab da khadija, ita kuma umma shafa ya'yanta hudu, yaya haisam, fadila, kursum da rahma, sai jikanta yusuf dan fadila ta taba aure amma sun rabu da mijin. Faruuq yyi ajiyar xuciya yace "to shi yaya Aliyun yana ina?" ta dan xaro ido tace "nima ban sani ba wllh, amma baya gidan ynxu hka" yace "ok xainab ce kanwar tasa knan" "eh..." tace kanta a sunkuye, buda ido yayi yace "to meye na kuka intisaar,
Wllh naji na kara sonki ne fisabilillah" ya ciro handkercief ya goge mata fuskarta yace "i luv you dear," ta gyada kai kawai ta kasa cewa komai, yace "ki bani ixinin na turo gidan ku plss" ta dan yi jim sannan tace "to sai nayi shawara da inna ta" yace "Ok gobe ma xan xo ai wajen innar" har bakin gate ya rakota ta shiga sannan ya wuce, taji ranta yyi fari sosai, ta kuma ji ta kara son faruuq……. Washegarin ranar da magrib faruuq ya bar gidan su, sun dde suna hira da inna daga bisanni tace idan tayi shawara da dan ta xata gaya masa lkcn da xai turo, har gate ta rakosa, yaya haisam ya shigo suka gaisa da faruuq, ya dan xolaye ta Sannan ya wuce, faruuq ya dubeta yace "yana aiki ne haisam?" tayi dariya tace "Lahh barrister ne pa da ka gansa, a Abuja yake aiki kila hu2 yaxo nake ga" yace "to shi da Aliyun waye babba?" ta dan yi jim sannan tace "ya Aliyu ne mana" yace "O.k shi kuma Aliyun wani aikin yake yi? Ko bai fara ba?" Tace "nima bn sani ba," ya dubeta da tuhuma yace "baku interact dashi ne?" tayi murmushi tace "Aa ni bamu san juna sosai ba" yace "Ok... Duk xaman ki gidan nan baya nan ne?" Ta dan xaro ido tace "A'a yana nan mana"
Faruuq yyi murmushi yace "ko bae sake maki bne?" Ta dan yi shiru sannan tace "uhm" dan ita ba ta ma son ana tuna mata ya Aliyu ko kadan, duk ta kagu ya rabu da ita da xancen Aliyu, shi kam murmushi yyi yace "to shknan intisaar, ni xan tafi" ya ciro kudi mai yawa ya bata" tace "haba na
Mene yaya" yace "yau juma'ah shi yasa" tace "a'a nagode, ka barshi kawai" ya bata rai yace "tun da muke dake na taba baki abu intisaar? ki karba nace" da kyar ta karba tayi masa gdya sosai, sannan tayi sashinsu da saurinta. Xaune take a kasan parlon Abba yana duba jarida, can dai ya dubeta yace "ya aka yi intisaar?" a hankli ta fara magana muryarta na rawa, "Abba dan Allah kayi hkuri ka bar su Hajiya da umma su dawo" Abba ya katse ta da sauri yace "to ai ni bni da ta cewa a nan, sai abinda kakarvku tace, dan ita ke da iko dani, kin ga kuwa bni da laifi a nan" tayi shiru, sannan ta mike tace "to Abba" daga haka ta fita ta bar palon. Yyi murmushi dan yasan uwarta ce ta turo ta, dan ya nuna mata kar ta sake masa mgnarsu Aisha kwanaki uku da suka wuce tana basa hkuri. Intisaar na fita sashin inna ta nufa, ko da tayi mata mgna ma bata rai tayi sosai, tace "maxa fice ki bni waje kafin raina ya baci, idan ma uwar ki ce ta turo ki kije kice mata nace ta shiga hankalinta, idan ba naci da kinibibi  ba ma mutanen da ba sonta suke ba ta wani damu kanta a kansu" intisaar ta fice mata daga palon nata a fusace dan ita bata san me inna take
nufi ba, to don me baxa su ci darajar ya'yansu ba ma a bar su su dawo gidan. Ita kam tausayin xainab dasu kursum take yi sosai, shi kuma ya haisam ko a jikinsa dan ko xancen ma baya so. Tana tafe tana waya da faruuq a hanya, ynxu kam shakuwar su ya wuce misali, dan inna kadai yake jira tayi ma abba magana dan shi a shirye yake, kuma yace xai dauke mata nauyin kara2n ta gaba daya, dariya tayi sosai tace "kai ya faruuq wajen inna pa xani ba wani gun ba, yace "ohk ai nayi xaton fita xa kiyi ne shiyasa nace hkan," a hka ta karaso sashin inna tana ce masa "yayana ko sllh ma ban yi ba" yace "haba de kanwata gashi har wajen karfe takwas, to kiyi alwala a bakin tap, nan waje kafin ki shiga mana," tace "dama hkn xanyi yayana" ko da ta isa bakin tap din ma sai ta tarar ana alwala, tace "ka ga yaya haisam ma na alwala a wajen," ya haisam, yayana yana gaishe ka wai, ta fadi tana kallon mai alwalan, jin bai ce komai ba ta ci
gaba da hira da faruuq tana jiran ya gama itama tayi alwalan "hmm to shknan kanwata yi alwalarki anjima mayi magana" faruuq ya fadi yana kkrin kashe wayan tace "a’a ai ya haisam bai gama ba" dariya faruuq yyi yace "baki gajiya da jin muryata ko bbynah?" kunya ya kamata tace "lalle ma to bye" da sauri yace "oh srry my intisaar wasa nake maki" a dai-dai lkcn mai alwalan ya dago, suka yi ido hudu da ya Aliyu, wani irin muguwar faduwar gaba ya xo mata, bakinta ya fara rawa ta ma rasa nemo gaisuwar da xa tayi masa, kallo daya yyi mata ya dauke kai ya shige parlon inna. Faruuq kam ya kira sunanta yafi sau biyar, duk da wayan na kare a kunnanta amma ta kasa cewa komai, har ya gaji dan kansa ya kashe. Kasa koda motsi tayi daga gun da take, ta dai dake a hnkli ta juyavxata koma sashinsu taji inna ta kwado mata
kira, da sauri ta dawo amma ta kasa amsawa ta kuma ki shiga, taji inna na cewa "Aliyu ba muryar intisaar naji a waje ba?" shi dai bai ce mata komaivba illa dardumar da ya dauko ya shimfida, tace "a'a baxa ka masallaci bne?" A takaice yace "eh..." Ya tada sallan sa. Sai da inna ta leko tayi ma intisaar magna sannan tayi alwala ta shigo palorn a sanyaye. "Sai yanxu kika ga daman xuwan knan?" Cewar inna tana kallonta, intisaar ta dube innar tace "aiki nake yi ne" tace "to ke da faruqu kuke waya ko wa?" Tayi shiru bata ce Komai ba sai hararan innar da take yi, inna ta tabe baki taci gaba da dama furar da take yi tace "Zainabu kike harara ba ni ba dai" Aliyu na idar da sallahn ya mike, inna tace "Toh ba ki ga yayan naki bane ke, daxun nan da yamma ya diro ya ma ce min jirgin sama ya hau" ta dube sa a hankali tace "ina yini yaya?"

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Oct 06, 2019 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

InteeesarWhere stories live. Discover now