chapter 6

104 6 0
                                    

A b'angaren su queen Noor kuwa ta saka an kai wa king Nadeer abincin sa.bata je dakan ta ba Sabo da tasan hali kuma ba da cewa bace, sannan ta akaiwa queen Falila da nata. Ta zauna ita kadai yinin ranar tunani kala kala a ranta.
Bayan sallahr Azahar ne ta tashi ta kira jakkadan ta guda ukku suyi mata abinci mai kyau don kanta ciwo yake kamar zaya fad'o haka su ka zo su ukku tayi ordering dinsu dasu yi mata abinci(macroni da miyar peak milk da kaza,sai zobo mai cucumber  )su ka ansa.ta basu girkin ne saboda sun iya kuma ta yarda da su.haka suka tashi suka tafi . bayan awowi kadan suka gama abincin suka zo suka gayawa queen Noor tace su zuba wa amarya da nata sai na sarki sai na queen Falila.nan ma suka ansa da girmamawa suka ce Allah ya taimake ki ba za'a kawo muku ba tace A'a kubarshi ni na koshi amman ku ku zuba kuci.zasuyi gardama tace bani son hayaniya kuje kuci.suka tashi Simi Simi dad'i fal aransu kuma suna kara kaunarta a zuciyar su.
Haka suka Kashi su ukku daya tayi bangaren sarki,daya gun amarya sajeeda,daya gun queen Falila.
Koda jakkadiyar da za ta kaiwa queen Falila da nata taje ta mata sallama aka mata iso ta shiga tayi dan kirari sannan ta ajiye mata agaban ta ta kara kirari ta tashi zata tafi ta kirata ta dawo tace ina ita queen Noor din tace tana daki bata da lafiya kanta ne ke ciwo ta tashi da sauri tana subahanallah tana ina muje na ganta sai a kira mata family doctor suka tashi da sauri suka tafi a hanya suka hadu da king Nadeer yace ummi queen Noor bata da lafiya tace ai nima wajenta zani je suka tafi su hudu a tare Koda zuwansu bakin kofa su jakkadai suka kama gabansu su kuma suka kulle kofar su biyu suka shige a kwance suka iske ta king Nadeer ya yo kan gadon da gudu ya jawo ta ya dago ta . yaji jikinta zafi sosai ga idonta a kulle sai ruwa yake ta lumtse shi gada gam duk ya rikice yace ummi Noor bata da lfy jikin ta yayi zafi ta matso kusa da su ta taba jikinta taji zafi ta dauki wayar queen Noor dake a kan bedside tayi searching number family doctor ta kira yace gashi nan zuwa.taja gefe ta zauna kan sofa ta zauna tana kallon su cike da tausayi sannan tana ganin laifinta a komai ita ma kamar tayi kukan haka ta zauna tayi shiru . ba'a dau lokaci ba sai ga family doctor yazo ya auna ta yace masu masassara ne da ciwon kai kuma bata cin abinci da sauri king Nadeer ya dago ya  kalli doctor kamar ya bata cin abinci to to ya ma rasa mai zayace kawai ya tashi da kanshi ya fita ya kira duka jakkadain da masu aikin part din ta yace su same shi a parlourn queen Noor suna ta dardar suna gani sunsan  ba lafiya suka hallarta dukansu yace wace shugabarku aka nuna wata jakkadiya ta fito kai Akasa yace mata wake kula da abincin part dinnan aka nuna wata ita ma ta fito yace wake kai mata abincin wata ma ta fito yace toh ku zaku iya tafiya sauran suka tafi yace ku zauna muyi magana suka samu waje k'asa suka zauna yace har tsawon wane lokaci queen Noor bata cin abinci kallon kallo suka dinga yiwa juna da tsawa yace bazaka ku bani amsa ba suka ce Allah ya taimake ka muna kai mata abinci har d'akin ta wani ma sai dayake ita keyi sai ta dauka ta tafi dashi da kanta in tayi anman bamu san bata ci ba sai yace shikenan abun da kuka sani sai ta kusa da jakkadiyar tace kuma gaskiya in na dauko abinci daga dakin ta bata ci dayawa kuma duka an chakwakwalkwalashi sama sama yace shikenan ta kusa da ita tace mai martaba kuma da atare wani sai'n muke ci anman yanzun bama ta san hayaniya da ankawo mata zamu tafi mu bata waje yace shike nan ku tashi ku tafi suka tashi suna yan maganganu tsakanin su suka tafi.ya shiga ya iske doctor na rubuce yana shiga yace mai martaba gashi waanan magungunan za'a siyo yace inzaka iya ka siyo mana yace ba matsala anman taci abinci kafin nan kuma za'a yi mata allura harara sarki ya watsa mai wanda sai da ya sha jinin jikinsa sannan sarki yace Mar ka siyo Allurar magani kadai zata sha yace angama mai martaba.zaya fita queen Falila tace ina zaka yace zan je in dauko mata abinci taci yace ina abincin yace yana side dina tace A'a dawo ka zauna bari Asa jakkadiya taje ta dauko gyada kai kawai yayi yadawo kusa da queen Noor dake kwance wacce tasan me ake anman bata iya magana duk haushin kanta ta ke ji queen Falila ta kira jakkadiya ta aike ta sashin ta tace je ki dauko mun abincin da kika kai mun daxu ta ansa Allah ya taimake ki ta wuce da sauri ba'a dade ba ta kawo queen Falila ta ansa ta dawo dashi d'akin da suke ta gansu ta k'arasa kusa da ita ta d'ago ta ta jinginar da ita jikin gado still idonta a kulle yake tace queen Noor ahankali itama ta bude ido tana ta kuka tana ummi danAllah kuyi hakuri tana ta  basu hakuri shiko ji yake kamar ya cire zuciyar shi ya Yada saboda bakin ciki shima ya dawo kusa da ita ya rike dayan hannunta yana cewa miyasa baki cin abinci tace ina cin abinci yace anman doctor yace bakici tace yau ne kawai banci ba baya son Jan magana kawai ya kyaleta yace ummi ina abincin tace gashi nan   ta miko masa ya dauko zaya bata tace zan iya ci da kaina ummi ta lura saboda ganinta ne ta tashi ta bar musu dakin tace in kun gama ku kirani ya amsa da toh ummina.haka ya dauko yana bata bata son ci hakanan dai ya tilasta ta bayanda zata yi taci ba laifi sannan ya fita yace masu su samo mishi yogurt ba dadewa aka kawo mishi ya dawo cikin d'akin ya zuba a cup ya bata ta ansa tasha bayan yan minting sai ga doctor ya dawo yana zuwa ya kira shi yazo da kansa ya anshi maganin yace namaka transfer ta account dinka yace nagode Allah ya saka da alkhairi sarki nadeer yayi gaba bai bashi ansa ba yana shiga sai da ya wahala kannan tasha maganin.haka aka kira sallahr asr wanda a dakin ta yayi itama ta tashi ya tsaya bayan shi ya ja su sallah wanda bata so ba tana ta cewa ta warke shi bai yarda ba suna gamawa suka yi addu'a suka tashi

Acan fada kuwa ana can ana jiran sarki za'ayi suna ganin baizo ba gudun fitar lokaci suka yi sallahr su kawai

Abangaren  queen sajeeda kuwa abin duniya ya isheta taga dai har asr ya wuce baizo yaganta ba tun da safe kawai tayi deciding ya fita tana tashi taji bata iyawa ta koma ta zauna gashi ya tafi kuma ya barta cikin azaba waccen tsohuwar da ya saka a kula da ita ba abun da ta iya niko lovebirds nace kodai ke ke baki sonta ba
Ta kira jakkadiyar ta tana zuwa tace taje ta kira mata sarki jakkadiya taji abun wani bambara Kwai a kira sarki kuma ya za'ayi a kira sarki tace Allah ya taimake ki anman ya za'ayi a kira sarki tace bangane ba baza'a kira shi ba shi ba mutum bane tace ranki ya dade anman sarki fa tace bazaki kira shi ba to na kore ki daga yau tace toh nagode don tasan ba yanda za'ayi ta bar gidan tun da ba ita ta kawo ta ba beside ma taji dad'in korar daman bara son ta haka ta tashi queen sajeeda nata Burma mata zagi ko da fitar jakkadiya straight dakin queen Falila taje aka mata iso tana shiga ta gaya mata tace me ya hada ku ta bata labarin abinda ya faru tace toh tashi kije ba komai na maida ki bangare na daga yau tace Allah ya taimake ki godiya nike ta tashi ta tafi.fitar jakkadiya ke da wuya sai ga kiran hajiya aisha ( ummin amaryar sarki nadeer ) ya shigo cikin wayarta ta daga da fara'arta  suka gaisa bayan gaisuwa queen Falila ta tambaye ta ya gajiyar biki tace mata Alhamdullilah hajiya aisha tace daman kira nai ince maki wai sajeeda ce bata da lfy kuma sarki baya zuwa wajenta wani irin abu queen Falila taji tace subahanallah bata da lfy bari inje in duba ta tace toh shi yana ina tace yana fada aiki ne ya Mishi yawa tace toh shikenan aminiya sai anjima queen Falila tace sai anjima  nagode tana aje wayar wani haushi ya ziyarce ta watikam baza ta kira tayi mata sannu da gajiyar biki ba sai don yarta ta tashi ta kira jakkadai biyu suka tafi side din queen sajeeda koda shigarsu taga warmers din abinci kan daina guda 6 ta biya gun duk ta bude ba'a taba ko data ba tayi mamaki ta wuce dakin queen sajeeda tana zuwa taga queen sajeeda na kukan munafirci tana kokarin tashi anman ta kasa da gudu taxo ta d'aga ta tace sajeeda baki da lfy tace mama kafafuna ke ciwo kuma yunwa nake ji tace sannu saboda ta d'ago ciwon kafar sannan tace toh miyasa baki ci abinci ba ga abinci fa chan kan dining tace mama ni ba a kawo mun abinci ba tace anman naga abinci ai tace toh basu gaya mun ba tace shikenan me kike son ci yanzun ta lissafo mata abincin cika dayawa tace duk ke kad'ai aa yanzun bari inje in sama maki abu marar nauyi da ruwan shayi tace toh mama nagode ta fita tana tausayin ta kuma tana jin haushin nadeer a ranta da fitowarta jakkadan ta suka Mara mata ba ya ta wuce waje jakkadain queen sajeeda tana zuwa suka gaida ta daga musu kai ta fara magana miyasa basu gayawa queen sajeeda1 an kawo mata abinci ba suka ce sun gaya mata tace bazata ci bane ta daga kai kawai tace toh kuyi mata faten tsakii da yakuwa sai ruwan tea na na'ana'a da lemon grass with girma suka ansa.   ta fita straight part din queen Noor ta wuce ta na zuwa ta wuce dakin ta shiga ba tare da da kwankwasawa ba tana shiga ta gansu manne da juna queen Noor tayi saurin zamu jikinta shiko gogan ko a jikin sa tana shiga tace ya jikin ta ce mata da sauki tace Allah ya kara sauki tare da momy na gode gyada kai kawai tayi tace ina son magana da kai kawai ta fita ta wuce part din ta. Yayi ma queen Noor sallama ya wuce bangaren queen Falila da zuwansa ya shiga dakin ta ta bashi umarni ya zauna.ya zauna ta fara magana kamar haka Nadeer kasani yanzun hakkin dake kanka ya karu kaji tsoron Allah ka ringa adalci a tsakanin matan ka yanzun fisabillillahi ko baka son sajeeda ai ya kamata ka bata hakkin ta a matsayinka na mijin ta shidai tun da ta fara be gane ina ta nufa ba yace ummi ban fahimta ba sajeeda nasaka ayi mata duk abun da ya dace kuma ina fada ina attending to people's complains sannan aka zo aka ce queen Noor bata da lafiya ummi shine naje sai yanzun me nayi tace anman ai kasan abun da kayi jiya ko kabar yar mutane da ciwo kunya ta dan kamashi yace mum kafin na fita na tambayeta abun da take so tace mun ba komai sannan naje gurin baba tabawa separately

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Nov 18, 2019 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

Princess Ayrah : The Light of Ni'ima kingdom   Where stories live. Discover now