Page 01

4.1K 114 11
                                    

MUTUNCI MADARA NE...
(The story of two side).

BY SAFIYYA (MRS J MOON.)

WATTPAD @Mrsjmoon.

*Allahumma salli wa sallim ala sayyiduna Muhammadu adada mafi ilmi salatin da'imati bi di'a'un janna. S.A.W.*

Page 01.

KADUNA.

Cikin rashin kuzari nake shiryawa dan zuwa office domin yau Monday. na kammala shiryawa cikin riga da zani na atamfa super na sanya fassion hijab da heel shoes duk brown colour kamar yarda atamfan take, na fice da sauri ina kallon agogon dake d'aure a left hand d'ina tare da gyara zaman farin gilashin dake kan fuskata.

A parlour nasami Momy zaune na isa gabanta na sunkuya kad'an.

"Good morning Momy?"

"Morning, kintashi lafiya?"

"Fine Momy."

"Good, dafatan kinyi breakfast?"

"No Momy amma in na isa office zansha black tea."

Harara ta cillamin na kauda kai gefe ina murmushin gefen baki. Ta nunani cike da takaici "Wai sai yaushe zan daina yi miki maganar akan daina wasa da cikinki ne Batul? A ce tun kina k'arama nake fama har zuwa girmanki, wanda inda muna Alk'alere ne tabbas da yanzu kina da d'a ko d'iya na kanki. Anya hakan da kikeyi ya yi miki kyau kenan Momyn Dad?"

B'ata rai nayi sai kuma na saki murmushi dimple dake gefen cheek d'ina na dama ya lotsata ciki na k'arasa nayi hugging d'inta tare da sauke kiss a both kumatunta na saketa tare da ficewa cikin hanzari ina cewa "Kiyimin Addu'a Momyna."

"Allah ya tsare ya kare cikin amincin Rabbi."

"Amin!."

Na amsa da k'arfi domin nariga dana fice harabar gidan.

Ina driving amma tunanin yarda zamu kwashe da Mamie Zulfa'a nakeyi.

"I'm sorry Mamie." Na furta a hankali.

8:30am Na isa harabar *A. A BASIT INVESTMENT COMPANY LIMITED.* Parking nayi cikin rashin karsashi kamar yarda na fito gida.

"Good morning mah, how are you?

"Morning, Alhamdulillah Samuel." Na amsa.

Yana shirin sake magana nayi gaba dan cikin abinda na tsana har da yawan gaisuwa. Amma dik da haka kafin na k'arasa office na amsa gaisuwa daga abokanan aikina zuwa bak'in da sukanzo dan aiwatar da lamuran gabansu yafi a irga.

"Hajiya k'arama sannu da isowa, ya su Hajiyar da Alhaji tare da 'yan uwanki?"

"Dik suna lafiyalau Baba Musa." Na amsa a gajiye.

"Masha Allah, sannu fa kwana biyu dai Hajiya Babba na rigaki isowa."

Shigewa nayi batare da na kula zancen ba, domin gulma ce tsagwaro ke cinsa.

Kama hab'a masinja Malam Musa ya yi yace "Kai jama'a yarinya kamar mai d'auke da iffiritu a ka? A ce yin magana yazamo mata abar wuya, Allah ya kawo miki sauk'i kam."

"Amin, kai kuma gashi kana son jin zak'in miryanta ko tsoho?"

"Kai Habibu banson bakantan iya shege, kazo kenan zaka soma mannamin hauka."

Dariya wanda aka kira da Habibu ya yi ya kama hannun k'ofar office d'insa yace "Kai ne ai Baba da neman magana, a kullum sai kayi wannan k'ofarin akan Batul kamar karin kumallo."

"Kai kuma da baka gani ka kyale sai ka tanka tamkar abincin dare."

Sosai Habib ya dara "Kai Baba Musa sam baka barin bashi."

MUTUNCI MADARA NE...Where stories live. Discover now