DA IYAYENA kashi na biyu

128 11 0
                                    

*DA IYAYENA*
          Kashi na biyu

_Mai taken MAULA_

          Daga Alƙalamin
     Rahma Kabir Mrs MG

Wattpad @rahmakabir

*GAJEREN LABARI*

1 ~ karshe.

              "Karime! Karime!!"
Muryar Jimma ce ya karaɗe gidan da sassafe, a hanzarce ta fito ta iso gabanta, Jimma ta miƙa mata buhu tana gyara mayafinta.
"Karɓa mu tafi kar ayi bamu, yau gidan Alh. Madu ke sadakar hatsi, gara mu isa da wuri mu samu gaba-gaba ko ma bar wajen da wuri mu isa bakin titi."

Karime ta tsaya sororo tana mamakin furucin ta, Jimma ta katse ta.

"Ban son sakarci kin ji! Da yawon maula nake tara abin da nake kawo muku ƙauye"

Duk da tsananin yunwa da gajiyar hanyar da ke addabar Karime ta ji komai ya gudu, sai Kalmar "Maula" da take maimaitawa a zuciya da kan leɓenta.

'DA IYAYENA da gatana zan yi maula? meyasa Jimma zata boyewa su Inna gaskiyar abinda take yi a birni? Haka kawai zaki saka ni a rayuwa mara tabbas mai cike da kaskanci da tozarci'

Karime tayi zancen zuci cike da kunan rai da dana sanin biyo Jimma da ta yi. Jimma ce ta daka mata tsawa wanda ya dawo da ita cikin tunaninta ba shiri ta amsa buhun tayi gaba cikin damuwa. Tun daga wannan ranar da sassafe Karime da Jimma ke fita yawan MAULA ba sa dawowa sai yamma lis, kafin daga baya Karime ta zama ƴar gari ta goge ta haɗu da ƴan tsararrakinta suna fita tare.

Karime suna cikin tafiya wata mota kirar Toyota ta zo a guje ta tsaya a gabansu, Karime ta matsa kusa da ƙofar motar aka zuge gilashinta, kafin ta furta wani abu matashin da ke ciki ya hura mata wata ƴar hoda, nan take ta fita cikin hayyacinta, matashin ya yi dabarar riƙe ta ta yadda waɗanda ke waje ba za su gane meke faruwa ba, ɗayan matashin da ke zaune a gidan baya ya fito ya riƙeta ya sakata a motar, fahimtar abin da ke shirin faruwa ya sa abokan tafiyarta suka runtuma a guje ba ko waiwaye. Haka motar ta wuce a guje suka isa da ita wani gida da ba'a karasa gininsa ba, in da samari uku suka yi mata fyaɗe suka yasar da ita a gefen wani kango suka gudu.

Wasu daga cikin ƴan MAULA ne suka yi ratse ta jikin wannan kangon, suka ganta shame-shame tana kakarin numfashi kamar ranta zai fita.

"Wannan Kamar Karime."

Ɗaya daga cikinsu ta faɗa hankalinta a tashe, haka suka yi kanta domin tabbatar da gaskiyar abun da idonsu ke gani, duba da halin da take ciki ne ya sa suka kakkamata suka kai ta asibitin gwamnati na sha ka tafi da ke can gangaren kangon, sannan daya ta je ta sanarwa da Jimma halin da Karime ke ciki. Karime bata kuma sanin halin da take ciki ba sai da ta ɗauki kimanin kwana uku a sume, farkawanta ta ganta a gadon asibiti ana mata ƙarin ruwa, Jimma tana gefenta tana matsar kwalla.

Satin ta ɗaya aka sallame ta, duk ƴan kuɗin Jimma sun ƙare a wajen jinyarta, Jimma ta yi ta masifa tana mita, ita dai Karime tana jin ta bata iya furta komai ba, domin a wannan lokacin ji ta yi ta tsani kanta da kuma rayuwar ƙasƙancin da suke ciki.

Tana ƴar shekara sha biyar, ta riski kanta a cikin murɗaɗɗen rayuwa, duk a sanadin son zuciyar Jimma yaya ga mahaifinta, ta zama tinkiya uwar tamɓele tamkar marainiyar da bata da iyaye. A zuwan Jimma birni akan dalilin yin sana'ar sharar kan hanya a nan cikin garin kaduna, wacce Gaje ƙawarta ta yi mata hanya, kuma a zahirin gaskiya yawan maula ce suke yi. Duk bayan wasu lokuta ta ke zuwa ƙauye ta duba su tare da sha tara na arziki, wannan dalilin ne ya sa a wani zuwa da ta yi ta ce za ta tafi da Karime, Babanta bai musa ba ganin cewar ƴar uwarsa ce, a ganinsa Jimma za ta inganta rayuwar Karime ne har ta fita zakka a ƙauyensu.

A zuwansu ne Karime ta tabbatar da cewar ta rasa gatanta, domin ta koma yin rayuwar kan titi da ƙasar gada, duk in da suka samu su rakuɓe su kwanta, garin Allah ya waye su bazama cikin gari yin bara, su kama gararamba tamkar tumaki.

***
Bayan wasu kwanaki da aka yiwa Karime fyaɗe ta warware ta koma sana'ar Maula, tunda ta hakan ne kawai rufin asirin ta. A kwanar wani layi mara ɓullewa Karime ta yi saurayi mai facin taya wanda ya jagorance ta har ta sauya sana'a ba tare da sanin Jimma ba, ita kaɗai take fita zuwa wajensa ta shige ɗakinsa dake ta bayan in da yake facin, ya bata abincin da ranta ke so, haka zata yini cur suna tare sai in an kawo masa aikin da yaronsa ba zai iya ba ne ya fita ya yi, in ya gama sai ya dawo ciki, har daga bisani ta kulla alaƙa da abokinsa, kafin wani lokaci ɗakin mai faci ya zama fadar Karime da abokan hulɗar ta, sai dare ta ke komawa wajen Jimma da kayan lashe-lashe, ta yi ta murna tana washe baki. Harkan ya karɓi Karime ta koma har ta share mako guda ba tare da Jimma ta saka ta a ido ba, zuwa ɗan ƙanƙanin lokaci Karime ta faɗa rayuwar bariki ba-ji-ba-gani.

Haka suka ɗauki tsayin lokaci a wannan ƙazamin ruyuwar da babu riba sai faɗuwa, kuma har lokacin ba su leƙa ƙauye ba. A wannan lokacin ne Allah ya yiwa Jimma rasuwa a sanadin mota da ta bige ta a kan babban hanya wurin tsallakawa, kafin a kai ta asibiti ta cika, a wulaƙance aka yi mata sutura aka kaita kushewa. Tun da Karime ta yi jimamin mutuwar Jimma na ƴan kwanaki, a dalilin rasuwar da zai sata ta yi hankali ta koma ƙauyensu, sai kawai ta ƙara rungumar harkar ta buɗe sabon shafin cin duniyarta da tsinke, ta sauya sheƙa ta koma wata unguwar da masu zaman kansu ke zama ta sanadiyar sabuwar ƙawarta Talatu.

Karime ta shaƙi iskar duniyar bariki ta kuma yi amanna da hakan, duk da tana da ƙarancin shekaru bai hana ta zama gogaggiyar ƴar bariki ba, cikin ƙanƙanin lokaci ta yi fice, sanadin uwar riƙo da ta samu mai suma Azumi Reza, ita ce wacce ta tsaya mata ta koyar da ita saɗara- saɗara a littafin ƴan bariki, Karime ta ɗau hadda gami da ɗammarar inganta Duniyarta.

Manyan Alhazawan birni na rububi akan ta, bata Abuja bata Lagos, tana zaga garuruwan cikin Najeriya a duk lokacin da take so, kuɗi na shigo mata yadda take so ba irin maula ba, domin a cikin kawayenta ƴan bariki tana a sahun farko na wadda zakaranta ya yi tsara, yanzu ne take jin cewa ta shigo birni, a cikin ƙanƙnin lokaci ta tara abin duniya ta zama babbar yarinya.

Karime na da shekaru ashirin da biyu, barikin da ta runguma ya fara ƙoƙarin kwace mata, rayuwa ya fara mata bauri, wani ruwa mai wari dake yawan fito mata a gabanta, abokan harkanta suka ja baya, ko ita kanta warin na damunta, ta fara zaryan asibiti zuwan farko an tabbatar mata da cutar sanyin mara ne ya kama ta, tun tana ganin lamarin abu ne mai sauƙi tana shan magunguna, tana samun sauƙi sai ta koma ruwa.

Watanni kaɗan ta fara jin raɗaɗi da ciwon mara mai tsanani, daga ƙarshe kuma ta soma zubar jini ba ƙaƙƙautawa. Da kyar Talatu ta kai ta asibiti bayan ta kwashe kwanaki uku tana mata magiya.

Bariki ya juyawa Karime baya cuta ya aure ta, abokan bariki daga maza har mata sun ƙaurace mata, lokaci ɗaya suka ɗauke ƙafa kamar ɗaukewar wutar lantarki, komai ya yi mata duhu, kuɗaɗen da take taƙama dasu suka fara tafiya a wajen magani, bokaye da ƴan tsibbu sun kwashi nasu, asibiti ma na ɗiba, a cikin irin gwaje-gwajen da aka yi mata ne aka gano sanƙarar mahaifa ne ya kamata, duk ta lalace ta ɗashe, ta zama abin kyama babu me zuwa duba ta balle a taimaka mata, haka zata yini kuka idan ta yi na hawaye sai ta koma na zuci. Uwani ma'aikaciya ce da ke sharan asibiti, ita kaɗai ke mata sannu a duk lokacin da take sharar sashin da Karime take, tana jin tausayin ta kwarai, hakan ya sa wata rana ta nufeta da tambayar ƴan uwanta.

"Iya bani da kowa, yayar Babana ce ta ɗaukoni zuwa garin nan, bayan ta kalallame iyayena da daɗin bakin romon da ake sha a birni, ni kuma a garin yawon maular da muke na yiwa bariki hawan ƙawara, daɗinta ya yi silar gamuwata da wannan cutar, don Allah ki taimake ni ki sadani da iyayena."

A hankali Karime ke labartawa Uwani rayuwarta, duk da tsananin azabar da take ji a jikinta, Uwani ta yi alƙawari washe gari zata kai ta tunda bata da aiki a ranar. Da taimakon wani likita aka samu motar da zai kai Karime garinsu, suka miƙa hanya, sai a lokacin ta shiga nadamar irin mummunar rayuwar da ta saka kanta a ciki, wanda duk a sanadin maula ne.
A fili Karime ta furta.

"Jimma kin ɓata min ƙuruciya, kin zalunci Iyayena"

Ta dubi madubin motar dake fuskantarta ta ga yadda halitarta ta sauya, sai ta tuna yadda take a ƴan watannin da suka gabata, duk abin da take taƙama da shi babu komai ya ƙare, ta yi tsantsar nadama akan rayuwar da ta yi wanda take masa kallon zanen ƙaddara.

Ƙarshe.

*Rahma Ce*

rahmakabir1313@gmai.com domin tuntuba.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Apr 04, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

DA IYAYENAWhere stories live. Discover now