BABI NA D'AYA

427 7 0
                                    

😭😭 *ƘANWAR MAHAIFINA* 😭😭

*_LABARI:_* '''MISS XERKS'''🌺

*_RUBUTAWA DA TSARAWA:_* 

''' Serdeyerh Lerwan

'''UMMU HANASH''')

🌈KAINUWA WRITER'S ASSOCIATION✍
(United we stand and succeed, Our ambition is to entertain and motivated the mind of readers

*_LABARIN GASKE_.*

*_SADAUKARWA GA:_*
'''IYAYE MAZA❤'''
(Allah ya saka maku da gidan aljannah).

*📓2019📓*

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JINƘAI*

_dukannin abinda zakuji acikin wannan littafin gaskiya ne bawai ƙagagge bane, dukkan al'amarin da zai faru acikinsa kama daga arziƙi ko talauci gaskiya ne babu batun ƙarya, sunaye kawai zan canja sai ɗan abinda baza'a rasa ba...._

*BABI NA ƊAYA*.

✍cikin banɗaki nake tsaye cikin shower ina wanka.jiyo ƙarar ring tone ɗin wayata yasa nayi saurin surar towel na ɗaura ba tare dana gama wanka ba saboda nasan mamallakin wannan taken kiran.

turus nayi naja na tsaya ina turo baki gaba lokacin dana ƙarasa bakin gadonmu ina jina kamar nayi kuka saboda yankewar kiran wayar.

inata ɓata fuska na juya na koma banɗaki na ƙarasa wankan sannan na fito.

da fitowata nai sauri na shafa mai na murza farar hoda sannan na saka kwalli na zira uniform ɗina ,ko man leɓe ban saka ba na ɗau hijabi da jakata na fice a ɗakinmu.

a parlo na tarar da Mamana ita da ƙannena suna hira, ido muka haɗa da ita ta saki murmushi tare girgiza kai.

murmushin nima nayi nai kan abincin ƙanina Muhammad dayake ci na saka hannu, sai dana kai loma ɗaya sannan nace.

"Hajia Mamata kenan, yaufa na fito da wuri duba agogo kiga"

"ai ganin ne ma yasa ban cema komai ba, ko lokacin tashin kika kai ai haka zakice baki makara ba"

dariya nayi na miƙe naje na wanke hannuna sannan na saka hijabi na nayi ƙofa ina ce mata saina dawo sai sauri nake.

da adu'arta data saba yimin kullum ta bini ina amsawa da amin.ƙofar ƙaramin gate ɗinmu na buɗe na fita bayan danayi adu'ar fita daga gida.

kaina aƙasa nake tafiya ina tinanin yanda zamu kaya yau nida Malm Ali, dariya nayi ni kaɗai.

ina shan kwanar layinmu naji machine na bina a baya,ɗan tsayawa nayi na bashi hanya ina jiran wucewarsa,gani nayi bai wuce ba na taka zanci gaba da tafiya sai naji ya kuma biyoni da alamu dai da gangan yake min hakan.

girar sama da ƙasa na haɗe na cije haƙorana na wani juyo a sukwane da niyyar zazzaga masifa sai bakina ya ƙulle sakamakon tozali danai da abin ƙaunata yana dariya.

numfashi na sauke na lanƙwasar da kaina ina kallonsa,shima niɗin yake kallo girarsa a sama yana kwaikwayon yanda nake, mun ɗau kusan mitina biyar muna aikawa da juna kallon soyayya sannan na sauke nawa tare da aika masa da harar ƙauna wanda na lura tana ƙara shauƙin sona a zuciyarsa sannan na juya zan tafi.

da sauri ya kashe machine ɗin ya sauko yasha gabana, hannayensa ya harɗe wanda sabonsa ne hakan.cikin daɗɗaɗar muryarsa da nake jin tamkar sarewa a kunnena yace,

"haba gimbiya, ke kya tafi baki tsaya kinji muryata ba"

"umm saina tafi mana tinda ka gaji dani"
nayi maganar cike da shagwaɓa wanda hakan nature ɗina ne.

K'ANWAR MAHAIFINAWhere stories live. Discover now