😭😭 *ƘANWAR MAHAIFINA* 😭😭
*_LABARI:_* '''MISS XERKS🌺'''
*_RUBUTAWA DA TSARAWA:_*
'''Serdeyerh Lerwan'''
'''(UMMU HANASH)'''🌈KAINUWA WRITER'S ASSOCIATION✍
'''United we stand and succeed, Our ambition is to entertain and motivated the mind of readers'''
*_LABARIN GASKE_.*
*_SADAUKARWA GA:_*
'''IYAYE MAZA.'''❤
(Allah ya saka maku da gidan aljannah).📓 *2019*📓
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JINƘAI.*
_dukannin abinda zakuji acikin wannan littafin gaskiya ne bawai ƙagagge bane, dukkan al'amarin da zai faru acikinsa kama daga arziƙi ko talauci gaskiya ne babu batun ƙarya, sunaye kawai zan canja sai ɗan abinda baza'a rasa ba...._
*BABI NA BIYU.*
✍daren ranar dana sanar da Faruq ya aiko rayashi yayi da farinciki ba tare daya runtsa dan bacci ba.
in tsaya faɗa maku irin shaƙuwar dake tsakanina da Faruq ɗina zamu shekara ban gama ba, gani muke duk faɗin duniya babu wasu masoya da suka zartamu a son juna.
mahaifin Faruq Alhji Muhammad shaharran ɗan kasuwa ne cikin ƙasa nigeria da waje duk sun sanshi, lokacin da Faruq ya sanar masa daya sami matar aure farinciki ya mamayeshi tamkar shine ɗan fari da zai fara aurarwa duk kuwa da ƴaƴan daya aurar sama da 5 sai dai yana ji da Faruq.
kwana ɗaya Baba ya ƙara a malesia ya dawo nigeria, a daren ranar daya dawo Faruq bai barsa ya huta ba yace sai anje nema masa aurena gani yake idan aka kai wayewar gari lokaci zai ƙure domin kuwa akwai masoyana da yawa da suke masa barazana akaina musamman ayanzu da sukaji cewar yana son aikawa gidanmu.
lokacin da Baban Faruq yazo ya sami Abba na sai ya turasu wurin Babban wansa, sunje sun sami wan Abba nah Alhji Mukhtar nan ya amincewa buƙatarsu da suka zo da ita aka kuma tabbatar masa da an basa ni.
wata uku da maganar badani aka kuma fara maganar aurenmu.
naira dubu ɗari biyar Faruq ya kawo matsayin kuɗin aurena da saka rana.
ƙanƙanin lokaci akasa ranar aurenmu domin kuwa watanni biyar akasanya.
Faroq beji daɗin hakan ba shi idan ta tasa ne a saka sati ɗaya ma tinda ta ko'ina a shirye ake daga ɓangare na har nasa, haka mukaci gaba da gudanar da soyayyar mu har zuwa lokacin da rage wata 1 bikin mu aka kawo laifi akwati goma sha bakwai da kowacce maƙil d akaya na kece raini acikinta.
wai kun san wani abu, a wata sau biyu Abbanmu ya yarje masa zuwa zance amma saboda Faruq bazai iya jure hakan ba sai yazo ƙofar gidanmu kullum ya zauna ya ɓata awanni tukunna ya tashi wai ai ya shaƙi numfashina dake fita.😄
Kwanci tashi lokaci sai ƙarasowa yake, haka muka je mukayi free wedding pictures masu kyau duk da ba'a son raina akayi ba danni a wurina pree wdng baida wani amfani da muhimmanci.
Anata shirye shiryen biki a b'angaren su Faruq da 'bangarenmu, haka Faruq ya d'aukeni muka je naga gidan daya gina mana, masha Allah gida yayi sosai saboda an zuba daula acikinsa wanda koda a mafarki ban taɓa tinanin ni ABIDA zan shigeshi ba.
tinfa saura wata ake ta shiryani, a bani wancan abani wannan duk na kai ciki, haka zansha wani ina kuka wani ina tanɗe baki saboda daɗinsa.
daga adamawa wata yayar mamana tazo da haɗin kazarta, artabu ɗinfa kenan, ai tana cewa dole saina ci na fashe da ihu domin kuwa inda abinda na tsani kaiwa bakina aduniya bai wuce kaza ba ko ƙamshinta da nake dangata shi da wari bana so.
YOU ARE READING
K'ANWAR MAHAIFINA
FantasíaLariba ne akan wata baiwar Allah, da abubuwa suka sha fad'a mata a cikin rayuwar ta, kama daga tausayi cin amana zalinci