BABI NA BIYAR

74 0 0
                                    

*😭😭K'ANWAR MAHAIFINA😭😭*

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }

         🎐 '''G•W•A'''🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*LABARI*: '''MISS XERKS'''🌺

*_RUBUTAWA DA TSARAWA_*:

'''SERDEYERH LERWAN'''
*(UMMU HANASH)*

*SADAUKARWA GA*:
*IYAYE MAZA. ❤*
('''Allah ya saka muku da gidan aljannah''')

📓 *2019* 📓

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

'''Dukkanin abinda zakuji a cikin wannan littafin gaskiya ne, bawai kagahhe bane, dukkan al'amarin da zai faru acikinsa kama daga arzik'i ko talauci gaskiya ne babu batun k'arya sunaye kawai zan canja sai dan abinda baza'a rasa ba. ...'''

~Am Back~

*BABI NA BIYAR*

✍ Nana ƙanwata ta rik'oni shima ya rik'oni muka nufi zuwa cikin gidan, abinda na sani muna isa tsakar gidanmu na saki wata k'ara tare da fizge layar dake kaina daga nan kuma ban san abinda ya kuma faruwa ba sai bayan farkawata ake labarta min komi.

Irin abubuwan da nake na shure-shure da fizge-fizge yasa Mamamu tayi saurin cewa Nana ta kira mata Babban Yayanmu wato Y Bukar a ɗakinsa.

koda taje shima da sauri ya taso ya biyota batare daya ja wannan ajin nasa ba suka taho.

Hankalin Yayanmu tashe ya ƙaraso wurin dasu Abid suke kewaye dani.

hannuna ya ƙwace daga na Abid ya shiga tambayar su Mama lafiya?

Uwa ta gari na hawaye tace masa,
"Abubakar ban sani ba wallahi, suna dai tare da Abid suna hira wannan baƙon al'amarin ya sameta...yanzu tashi zakai kaje ka kira Malam Mu'azz yazo ya dubata"

hankalinsa bai kai inda kowa nasa ke kaiba yace, "a'a Mamanmu bari na ɗauko mota mu wuce asibiti kawai emergency"

"banajin wannan aikin asibiti ne Bukar, kai dai jeka kira mani Malam kamin ya bar masallaci"

bai kuma ja da zancen nata ba ya miƙe da sauri shida Abid suka fita.

suna zuwa suka taho da Malam Mu'azz limamin masallacin anguwarmu.

da zuwan Malam Mu'azz ya tarar da halin da nake ciki yace, "kuyi maza ku shigo da ita cikin ɗaki"

Yayanmu ne ya ɗaukeni ya miƙa ni zuwa ɗakin.

ruwan zam-zam Malam Mu'azz ya buƙaci da akawo masa, nan yay tofa ayoyi ya shiga aikinsa na karatun alƙur'ani mai girma.

an ɗau awanni ana karatu amma fafur aljanun da suka bayyana sunƙi magana har sai da sukaji azaba ta ishesu sannan kafirin cikinsu yace,

"Dan Allah ka dakata kada ka cutar dani, kayi min afuwa, ka daina azabtar dani da waɗan nan ayoyin"

Malam yay masa banza yaci gaba da karatunsa tare da ƙara watsa min ruwan adu'ar dake hannunsa a kofi.

wata ƙara na saki wadda duk sai dana firgita ƴan gurin na miƙe zan fita a guje Malam yace su Yaya su riƙoni.

aka riƙoni aka ƙulleni da igiya, nan fa sabon shafin karatu daga qur'ani mai girma ya soma.

yi Malam yake tin ina tirjiya har na daina daga can Moses yace,
" dan darajar ma'aikin Allah Malam kai haƙuri wallahi bayin Kaina bane sani akayi, amma yanzu na maka alƙawarin zan fita daga jikinta na rabu da ita..kuma bani kaɗai bane akwai ƴan uwana mu goma duk da suka ganka suka gudu saboda ni ina da taurin kai shi yasa na tsaya"

K'ANWAR MAHAIFINAWhere stories live. Discover now