😭😭 *K'ANWAR MAHAIFINA*😭😭
*LABARI*: '''MISS XERKS'''🌺
*RUBUTAWA DA TSARAWA*:
*Serdeeyerh Lerwan*
*(UMMU HANASH)*🌈KAINUWA WRITER'S ASSOCIATION✍
'''United we stand and succeed, Our ambition is to entertain and motivated the mind of readers'''
*_LABARIN GASKE_*
*SADAUKARWA GA*:
IYAYE MAZA.❤
('''Allah ya saka muku da gidan aljannah''')📓 *2019* 📓
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
'''Dukkanin abinda zakuji a cikin wannan littafin gaskiya ne, bawai kagagge bane, dukkan al'amarin da zai faru acikinsa kama daga arzik'i ko talauci gaskiya ne babu batun k'arya sunaye kawai zan canja sai dan abinda baza'a rasa ba....'''
*Ina jin dad'in yadda kuke zuba ruwan comment a cikin littafin nan, ina matuk'ar godiya gareku sosai sai dai duk da haka ina buƙatar daɗin sharhi*.
'''Bani da bakin godiya gareki bestie (miss xerks) sai dai nace Allah ubangiji yabar zumunci, ya albarkaci rayuwar ki, Allah ya barki da Baby muzo musha biki'''.😍😘
*INA ALFAHARI DAKU*
'''Kainuwa writers Asso.'''
'''Xumunt@ Novell@ GRP.'''
'''Ummu Hanash and Miss Xerks novel GRP.'''*BABI NA UKU*
✍ Na kai awa a durk'ushe ina kuka daga nan na tashi na mik'e na k'wanta akan gadonmu na takura kaina kamar wata marar lafiya,ina jin motsin za'a shigo nayi saurin rufe idona kaman mai bacci.
jin Mama ce yasa nai saurin ɗora hannuna saman marata, ganin haka ta ƙaraso da sauri tana faɗin,
"Yaya ciwon marar ne"?
D'aga mata kai nayi alamun eh, da sauri ta d'aukeni ta fito dani, Yaya Bukar ta kira yaja mota muka tafi asbiti, to kasancewar duk ciwon marar da zanyi sai anyimin allura nake jin sauk'i wata ran ma sai an samin drip, haka yanzun ma ina kallo akamin allura aka bani magani duk a matsayin ciwon mara, bamu dawo gida ba sai yamma.
Bayan mun dawo na kasa samun sukuni, na kasa sanar da kowa abinda ke damuna a tare dani, hakan yasa Mama ta fuskanci akwai damuwa a tare dani, tambayata tayi ko akwai abinda ke damuna bayan ciwon marar nace mata bakomae.
Da daddare Abba ya dawo kowa yana zuwa yana masa sannu da zuwa amma banda ni, ya tambaya aka ce masa bani da lafiya, tashi yayi yaje ya dubani sannan ya wuce warsa d'aki.
Washe gari da sape da misalin k'arfe 6:30 Abba ya aika yana kirana, tashi nayi naje wajensa, ina duba fuskarsa naga yana cikin damuwa, shuru nayi ina sak'awa a zuciyata ko dai Abba yaji abinda ke faruwa, ban k'arasa maganar zuci ba naji yace,
"Abida meya shiga tsakaninku da Faruq"?.
dum gabana ya faɗi, yanzu mi zance ni kuwa, shiru nayi ban iya cewa komai ba, can naji yace,
"Tambayar ki nake, ba wasa na kiraki kimin ba, karki kawomin shashanci a cikin al'amura na",
"Meya had'a ki da Faruq"?.
Naji ya sake maimaitamin wannan tambayar.
Can nace masa "bakomae ban san laifin dana masa ba Abba"
nai maganar cikin zubar hawaye da ƙunar zuciya.Sai naji yace,
"Daman kin san abinda ke faruwa"?.
Da "Eh". Na amsa masa

YOU ARE READING
K'ANWAR MAHAIFINA
FantasiLariba ne akan wata baiwar Allah, da abubuwa suka sha fad'a mata a cikin rayuwar ta, kama daga tausayi cin amana zalinci