⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐
*WACECE NI*
✍🏼 by*fateema Muhammad Suleiman*
Fmsuleiman743@gmail.com
teemacool2020*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*Readers nayi matukar farin ciki da comments*
*Wannan shi yasanya ni* *kwarin gwiwar cigaba da rubutun Ana tare**page* 5⃣&6⃣
Babu Wanda yaji Harbin bindugar sai fadowar mijin na ta tagani, jina-jina cikin jini,babu mutumin babu dalilin shi awurin Kamar layar zana ya bace bat...
Tashin hankali da rudani da kuma kidima kam, hajja fanna ta ganshi a wannan rana da ta kasa mantawa a rayuwar ta.
Jami'an FBI sunyi matukar buncike, amma ankasa gano wanda yayi wannan kisa.
Ankai gawar asibiti domin gudanar da binciken likitoci sun cire blade kuma sun baiwa jam'i an tsaro .
sannan akawuce da shi mutuary...
Embassy sun sanya hannu domin maido shi Nigeria.bayan anyi arrangements din zuwan tare da iyalan shi,
Duk wani mai imani idan yaga *hajja* *fanna* dole Ya tausaya mata ckin kwana uku duk ta zube Kamar ba ita ba dama haka rayuwa take.Mr *suhaib* wani makocin su mutumin Pakistan ne, kuma suna zumunci sosai.
kasancewar *yakaka* da yaran shi suna makaranta daya kuma sa'ani ne da yarinyar shi mai suna *vaishali* sunyi matukar shakuwa da juna.
tunda akayi mutuwar da taga mahaifinta cikin jini taki zama agidansu...
Sai gashi rana daya kaddara zata rabasu daga yaran har manya kuka sukeyi...
Mr *suhaib* ya nemi da hajja *fanna* tabar musu *yakaka* ta gama primary six sai a maido ta Nigerian,tunda 'yan watanni yasaura musu sugama.
idan yaso dukkansu sai su zo Nigeria da iyalansa don suma suna son ganin yanayin Nigeria din...
Ta ce toh amma zan nema izinin iyayenta acen idan sun amince da haka ni bani da matsala.
Mr suhaib yaji dadin bayanan ta yayi mata godiya tare sake ban hakuri, sannan Ya koma gidansa...
hakan kuwa akayi anbar *yakaka* awajen Mr *suhaib* domin hajja fanna ta gamsu da tarbiyansa tun zamansu da shi bashi da matsala, kuma suna kula da addini sosai...
sun barta da sharadin tana gama primary school za 'a maido ta Nigeria.
mr *suhaib* Ya jinjina Kai tare fadin cewa in sha Allaah mune ma zamu kawo maku ita da kammu...
Haka rayuwa ta kasance akwana a tashi babu wuya awurin Allaah...*Yakaka* sun zana jarabawar shiga jss class
Kamar yadda *suhaib* Ya alkawarta sunyi shirin maido ta Nigeria.
Daga shi har iyalansa sunyi shirin yawon bude ido kasashe kafin su zo Nigeria...jirgin ruwa zasubi sun fara yada zango a Jamaica,italy,maxico sannan suka wuce Australia.
duk acikin babban jirgin ruwan vaishali da yakaka wadda suka canja mata suna da *Aazeen* a cewarsu Mai kyau duk sun girma shekarunsu sha biyu, amma zaka dauka sunkai sha biyar.
'yan matan gwanin ban sha' awa,da daukan rai...
YOU ARE READING
WACECE NI Complete
General FictionYarinya ce da aka haifeta ba tare da mahaifi ba kuma mahaifiyarta bata taba yin zina ba,sai wadansu figures da ke jingine da sunanta yayi sanadiyar baiyanar boyayyen sirri da mahaifiyarta ta boye shekaru masu yawa toh menene wannnan sirri? Samun ams...