44&45

99 5 0
                                    

⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐

        *WACECE NI*
 

    ✍🏼by
 
*Fateema Muhammad Suleiman*
Email fmsuleiman743@gmail.com
Wattad teemacool2020

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is ton entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*page* 4⃣4⃣&4⃣5⃣


*wannan page nakune masoyan wacece ni musamman masu yimun comment _zaratun_ tana godiya da kulawarku*

Best Line

“Keep in company of people of virtue; you will become one of them. Keep aloof from people of vice; you will remain safe from them.”
Remove your gaze from the splendor of the World. Do not let the love of this World enter your heart. Beware! The love of this World does not perhaps destroy you, just as it had destroyed previous nations.

(H) *Umar Bin Khatab* ( r.a )


Ina zaune a bakin gadon gaba daya asibitin gundireni,  yau wata daya da sati daya kenan. tsananin mamaki da al'ajabi nake rayuwar duniyar kenan,Allaah kuma mai iko ne sannan shi mai yawan hikimane da jujjuya lamuransa yadda yaso waye zai kawo  a ka cewa ni ce sanadin tona asirin wanda ya kashe kakana, tun kafin asan da zuwana duniyar? sai da na tiriyo dukkan abubuwan da suka wuce masu ban mamaki sannan na nisa na fada a fili cewa lallai Allaah mabuwayine gagara misali.sallamar da akayi ne ya dawo da ni daga tunanin da nake Dr zayd ne yashigo fuskarshi dauke da Fara'a.na amsa mashi sallamar cikin sakin fuska,ya shigo sai da ya zauna a kujerar da ke dab da gadon sannan ya ce your Excellency,ya dai duk tafiyar ce kike zaune a daburce haka?

Na rausayar da idanuna sannan na lumshesu na bude dama idanun nawa yanayinsu kamar mai jin baccine,na ce wallahi kuwa, duk na kagu ingani a gida gaba daya zaman asubitin ya gundireni,

Sai da ya gama karemun kallo sosai sannan ya yi murmushi ya ce mu kuma gashi bamu gaji da ke ba,saboda ke yanzu fitila ce ga wannan asibitin kin zama sarauniyarmu,saura kiris ki dane kujerar mulkinki ya karasa yana dariyarshi mai ban sha'awa Masha Allaah shima bashi da makusa kib kib da shi.

Na waro ido cikin mamaki, na ce nidince sarauniya? lallai ko da anga mulki.

Ya ce aiko kin tara kin samu domin mulki kam sanya a ranki kamar kinyi ne sai dai kiyi ta shan kamshinki,mu kuma muna tayaki.

Na ce toh Allaah ya bamu dukkaninmu
Ya ce Aameen.

kusan minti uku babu Wanda yakuma cewa komai sai can ya nisa sannan ya kira sunana da wata siga da bantaba jin ya yi irin ta ba.

Na dago idona sai kuma nayi saurin sadda kaina kasa ganin yanda ya kuramun manyan idanunshi masu matukar shiga rai gaskiya na kasa juriyar ganin idanun nashi.

Sai yayi saurin cewa ki dago idanunki ki kalleni maganar da zan maki mai mahimmanci ne inason ki fahimce sosai
Da hankali na juyo da fuska ina kuma fuskantarshi ido cikin ido.
Ya gyara zamanshi ya jingina bayanshi jikin kujerar sosai,fusjarshi kuma ba yabo babu fallasa cikin dakewa ya ce your excellent,

Tun kafin ya cigaba da maganarshi na katseshi da cewa haba Dr,wani irin nadi ne kukeson dangantani da shi?
ina fahimtarku tun jiya kuke dangantani da wani excellency,ina murmushin yadda yayi kasake yana kallon lebuna na,kamar yau ya fara ganinsu.
sai na ce zanfi jin dadi da kirana zaratun

Sai da ya sauke numfashi sannan ya ce haba wannan sarauta fa Allaah ne ya baki ba mu ba saboda haka dole kin amshi abin ki kawai,yanzu ma na zo da kokon barata ne bazan boye maki da gaskiya zuciya ta takamu da sonki wanda ina ganin idan bata sameki ba zata iya fadawa cikin wata matsalar duk da nasan akwai masu sonki ba sai kin fadamun ba amma nima inaso ki sanyani cikin masoyan naki tunda ance allura cikin ruwa mai rabo kan dauka.

WACECE NI CompleteTahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon