EPISODE 4

852 40 4
                                    

°🔘° *HAFEEZ KO UZAIFA* °🔘°
              *1441H/2019M.*
      


®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍️*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

      '''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*

*NA MARUBUCIYA:-*
*MISS XERKS✍🏼•*

*SADAUKARWA GA:-*
*UNCLE MUSTAPHA .M. FARAGA (LIBYA)•*

*DOMIN JIN DAƊIN:-*
*NERNER XERKS•*


~Wattpad @GaskiyaWritersAsso.~

*SHAFI NA 4📑*

*__________📖* haka na fito ina ta faman kumbure-kumbure, tsaye nayi ina waigen mai kiran nawa, daga can gefe naji horn, na juya na kalla farar motar dak fake ƙasan bishiya.

ina ganinta na gane mai ita,murmushi nayi na taka na ƙarasa inda motar take.

ina zuwa ya buɗe min murfin mota da niyyar na shigo,girgiza masa kai nayi kamin na buɗi baki nace dashi,

"a'a Salim, sai dai ka fito daga waje domin bana shiga motar saurayi".

fitowa yayi yay tattaki ya zagayo zuwa inda nake, sallama ta biyu ya ƙara min na amsa masa ina kallonsa.

"Ƴan mata kwana da yawa ko ne mana ba'ayi".

ya faɗa yana mai sunkuyowa ya kalla fuskata dake kallon ƙasa.

"hmmm daka damu dani ai zaka nemeni".

abinda nace dashi kenan ina mai ɗage girata sama.

ya maido min da amsar, "hmmm kawai ke dai baki damu dani bane, amma tsakani da Allah tinda kika ji shiru har haka ai kya neme ni, wata huɗu fa ba wasa ba Nazneen".

"hakane, to amma duba da nayi tin zuwanka na ƙarshe da naga ka tafi da alamu na ranka ba daɗi kuma ko sallama baka min ba shi yasa kawai na share ka".

ya murmusa yana mai mamakin yarintar dake tattare da kalamai na, yace dani,

"to saboda na tafi da ɓacin rai shine bazaki iya kirana kiji dalilin hakan ba?".

cike da ƙosawa nace, "kaga yanzu dai ai ya rigada ya wuce ko, ya kake ya kwana da yawa?".

"lafiya lau, sai dai nayi rashin lafiya sose dan watana uku a asibiti a kwance sai da aka mani dashen ƙoda, amma ba anan nigeria muka zauna ba egypt muka fita".

"ya subhanallah ai ban sani ba, Allah ya sauƙi ya ƙara maka lafiya".

na faɗa ina mai kallonsa cike da tausayawa.

ya amsa da faɗin, "ameen".

muka hau babin hira abinmu, kusan mintinmu ashirin tsaye saiga Yaya Hafiz ya dawo.

gaba ɗaya ma ni ban kula dashi ba dan ko tsayuwar mashin ɗinsa banji ba sai da Salim yace, "min ga babban Yaya nan".

ɗago da kaina sama nayi ina kallon ta inda Yaya Hafiz ke tahowa.

gabanmu yazo ya tsaya ya zare siririn farin galashin dake idonsa, hannunsa ya fiddo daga aljihu ya miƙama Salim suka gaisa, wanda sallama ce kawai yay masa itama da ƙyar ya iya tattaro yawun bakinsa ya faɗeta.

cikin takunsa na ƙasaita kamar wani mai jinin sarauta ya juya ya shiga gida.

ƙaramin tsoki nayi cikin raina ina faɗin,

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Nov 28, 2019 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

HAFEEX KO UZAIFA.Where stories live. Discover now