EPISODE 1-2

2.5K 87 1
                                    

♻♡♡♡♡♻
     *HAFEEX*
            ko
     *UZAIFA*
♻♡♡♡♡♻

          
®© *BY MISS XERKS🌺✍🏼*

*﹩Ѧ¢ґїƒї¢℮ †◎*,
*Uncle Mustapha M. Faraga🇱🇾*

'''I͢n͢ T͢h͢e͢ H͢o͢n͢o͢u͢r O͢f͢ M͢a͢m͢a͢n͢ K͢h͢a͢d͢y͢, K͢h͢a͢l͢e͢e͢p͢h͢a͢ & A͢m͢a͢t͢u͢l͢l͢a͢h͢'''...

*ín dєvσtíσn  tσ вlvd  ѕíѕ nєrnєr αчѕhαєr хєrkѕ😘.*

          
                 ⓿❹
           _❷⓿❶❾_
                p⃟m⃟

_______________________________

🅔🅟🅘🅢🅞🅓🅔 - ⓿❶

Wani kallo yai mata mai cike da ban tausayi a lokacin da ita kuma wani zazzafan hawaye ke kwaranya akan fuskarta.

Cikin sanyin murya ya dubeta da kyawawan idanuwan da Allah ya hore masa farare ƙal yace da ita,

"sannu ya jikin naki"?

Dubansa tai tana mai nazarin irin damuwar dake shimfiɗe saman fuskarsa cikin siririyar muryarta kuma zazzaƙa tace,

"da sauƙi Y Hafix"

"to Allah ya daɗa lafiya ƙanwa tah,yasa kaffara"

"Amin" tace tana dubansa shi kuma idonsa na kan wayarsa ƙirar adroid tecno W4 yana dannawa.

"Yaya Hafix baka gajiya da zuwa dubani? Ka dinƙa hutawa dan Allah kaga tafiyar fa ba ƙarama bace"

"haba Nazneen, kefa ƙanwata ce idan banzo dubaki ba waya cancanci naje na duba,ai ya kamata nayi haka ne shi yasa"

Murmushi tayi tace, "kai dai"

Sai daya ɗago ya ɗan dubeta tukunna yace, "ohhhh a asibitinma sai munyi kenan"

Shiru ta masa ta runtse idonta gam, "mtsswww" tai ɗan ƙaramin tsoki cikin maƙoshinta,to waima miye hakan? ta tambayi zuciyarta cikin jin haushi.

Tsinkayar kakkausar muryarsa tayi cikin kunnenta.

"me yasa ki hawaye Nazneen ,fatan ba jikin naki bane ko?"

"Kaina ke saramin Yaya Hafix kaman zai fita saboda azaba"

Amsar data bashi kenan,amma a zahirin gaskiya ba ciwon kai ke damunta ba, wata wutar soyayyace da take ma Hafix ke ruruwa acikin zuciyarta.

Tattausan tafin hannunsa yakai saman fuskar tata yana goge mata hawayen dake zuba sannan yace.

"ohhhhh Hamida nah nifa ban yadda ba duk yanda akai bayan ciwon nan naki da wata damuwar a tare dake,karki ji komi ki faɗan ni Yayanki ne baki da tamkata"

duk da cewan maganarsa gaskiya ce da damuwa aranta wadda shi bazai gane ba tinda dai baida ganewa wadda bata komi bace face sonsa amma bazata iya faɗa masa ba dan kar class ɗinta datake ji dashi ya tsinke matsayinta na ƴa mace zata ƙwammaci ta rasashi indai har ita zata sanar masa.

Buɗa sexy eyes ɗinta tayi ta kallesa tana turo ɗan mitsilin bakinta kaman wata ƙaraman beb tace dashi,

"nifa babu wata damuwa Y Hafix ,zafin ciwon kaine kawai"

"to ai ba kuka zakiyi ba, kin san cuta sauƙinta sai a hanƙali kiyi haƙuri ki daina kukan kinji insha'Allahu soon zaki warke ki zama kaman baki ba kinji ko ƴar ƙanwata"

"Uhm hakane Y Hafix na gode"

kansa na ƙasa ya kalleta ta gefen ido yace,

"yauwa to ko kefa,kinga yawan kukanki shike daɗa ɗaga hanƙalin Momi"

HAFEEX KO UZAIFA.Donde viven las historias. Descúbrelo ahora