12-15

672 40 0
                                    

[1/3, 13:36] Mum Aysar: °🔘° *WASU MATAN* °🔘°
          *1441H/2019M.*

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍️*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

      '''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*

*NA MARUBUCIYA:-*
*MUM AYSAR✍🏼•*

~Wattpad @GaskiyaWritersAsso.~



*Gaskiya na rena comment ɗinku shiyasa bakwa samun postin akoda yaushe yakamata ku gyara idan kuma baku gyara ba to nima zan ajje alƙalamina.*


*DEDICATED THIS PAGE TO ALL MEMBERS OF GASKIYA WRITERS ASSOCIATION.*




*SHAFI NA 12📑*

*__________📖* maganar karatu kam an haƙura da ita dan Kamal ya sami Farida ya faɗa mata shawarar da sukayi shi da matarsa, taji ba daɗi amman ko kaɗan bata nuna musu damuwarta ba saima fatan alkhairi da tayi tare da addu'ar Allah ya sauke ta lafiya.

Bayan sati biyu da haka Zubaida ta tashi da naƙuda tasha wahala sosai sanadiyyar hakan tasa yarinyar data haifa batazo da raiba dan tasha ruwan mahaifa ta koma ga ubangijinta.


Zubaida kam tasha kuka kamar ranta zai fita saboda ta kwallafa   rai akan haihuwar saikuma gashi ta haifi yarinyar ba rai hakan bai mata daɗi ba.

A ɓangaren Aliyu kuwa yaje yasamu Abokinshi ya sanar dashi abinda mahaifiyarshi tace, shima Abokin nashi ya goyi bayan hakan don yasan irin wahalar da abokin nashi yake sha aduk lokacin da rashin lafiyarshi ta motsa, dan haka yabashi shawara akan zai haɗashi da wata Yarinya a unguwarsu take kuma ya yarda da tarbiyyarta, duk da kasancewarta ƴar masu kuɗice amma hakan bai shafi tarbiyyarta ba don kana ganinta zatai dai-dai da ra'ayinka.

Shidai Aliyu kawai jinshi yakeyi don yasan ba lallai  ta burgeshi ba don har yanzu bega kalar matar data burge shiba a duk faɗin ƙasarnan.

Bayan sati biyu da haihuwar Zubaida gaba ɗaya rayuwa ta sauya a cikin gidan dan a yanzu bata ɗaukar duk wani raini ko kus-kure daga gurin Farida don komi ƙan-ƙantar shi yanzu zata hauta da masifa, duk abin da yake faruwa Kamal yana kula da hakan dan haka bai nemi shawarar kowaba ya fara nemawa ƙanwar tashi (admission) kuma yayi sa'a ya samu anan BUK bai sanar da kowa ba saida ya gama komai sannan ya faɗawa Zubaida faɗa kam tayi shi kamar zata ari baki dan harda kukan munafurci wai ya nuna mata ban-banci akan ƙanwarshi da kyar ya samu ta haƙura.



Ranar da ya sanar da Farida zata fara zuwa makaranta murna tashayi tayi mishi godiya tare dayi mishi fatan gamawa da duniya lafiya tayiwa iyayensu addu'a sosai.


Ranar litinin tafara zuwa makaranta bata sha wahala wajen ƙarasa abinda zata zama cikakkiyar ɗaliba ba kasancewar akwai ƙawayenta da suke karatu cikin makarantar.


'''
To Farida munayi miki fatan samun ilimi mai amfani duniya da lahira.'''

_Kuci gaba da kasan cewa damu Gaskiya dokin ƙarfe_


Mum Aysarce😍
[1/3, 13:36] Mum Aysar: °🔘° *WASU MATAN* °🔘°
          *1441H/2019M.*

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍️*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

      '''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*

*NA MARUBUCIYA:-*
*MUM AYSAR✍🏼•*

WASU MATAN                               COMPLETED{02/2020}.Onde histórias criam vida. Descubra agora