19

464 35 0
                                    

°🔘° *WASU MATAN* °🔘°
          *1441H/2020M.*

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍️*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

      '''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*

*NA MARUBUCIYA:-*
*MUM AYSAR✍🏼•*

~Wattpad @GaskiyaWritersAsso.~


*_wanna shafin sadaukarwa ce gareki tauraruwar GASKIYA WRITERS me haskaka rayuwar mu HALIMATUSSA'ADIYYA ZAERKARIYYA (Mrs Zearks Doughter) Allah ubangiji ya baki sa'ar jarabawa yasa ki fito da sakamako mafi kyauwu ameen,Mrs Nazeer tana godiya gareki._*



*SHAFI NA 19📑*

*__________📖* Mamaki kam Farida tasha shi ganin yadda gaba ɗaya ƙawartata ta sauya mata kuma ta tambayeta ko tayi mata wani laifi ne, tace a'a dan haka ta koma gida da sanyayyan jiki ta sanar da Yayanta abin da ya faru, shima yaji ba daɗi amman ya danne tashi damuwar dan kar ya nuna mata abun yayi mata yawa.



Ita kanta First lady ba ƙaramin daurewa tayi ba ganin yadda ƙawar tata ta rame tayi duhu gashi kuma ga dukkan alamu akwai damuwa a tare da ita hakan ba ƙaramin tayar mata da  hankali yayi ba har cikin dare ta kasa samun nutsuwa dan haka ta yanke shawara akan ta tura mata da saƙo ta sanar da ita abin da yake faruwa, hakan kuwa tayi ta ɗauki wayarta ta fara rubuta saƙon da cewa, _"Amincin Allah ya tabbata a gareki ƙawata da fatan kinje gida lafiya, na rubuto miki wannan saƙo ne domin na baki haƙuri akan abunda ya faru ɗazu da kikazo gidanmu ina mai baki haƙuri ƴar uwata, sannan kuma gobe ina so mu haɗu dake domin akwai wasu shawar-wari da zamuyi dake dafatan zakiyi min uzuri ki kuma yafe min, na gode"._


Farida da take kwance ta fara bacci taji ƙarar shigowar saƙo janyo wayar tayi ta fara dubawa taji daɗin ganin saƙon dan haka batayi wata-wataba ta kirata a waya, tana kira ta ɗaga dariya sukayi gaba ɗayansu kuma ba wacce tayi magana har tsawon sakanni, First ladyce tace, "sai da safe". itama tace, "Allah ya tashemu lafiya". suka kashe wayar.


'''ku ɗanyi manage da wannan bani da lpy shiyasa ina barar addu'ar ku.'''

'''Mum Aysarce''' 😍

WASU MATAN                               COMPLETED{02/2020}.Onde histórias criam vida. Descubra agora