[1/3, 13:36] Mum Aysar: °🔘° *WASU MATAN* °🔘°
*1441H/2019M.*®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍️*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_**NA MARUBUCIYA:-*
*MUM AYSAR✍🏼•*~Wattpad @GaskiyaWritersAsso.~
_Wannan Shafin nakine ƙawata ina godiya da ziyarar da kika kawo min Allah ya bar zumun ci, kiji daɗinki ta wajena *Queen Abidat(quean of the world)* Mum Aysar na yinki irin totally ɗinnan_
*SHAFI NA 16📑*
*__________📖* Rayuwa me juyi-juyi abubuwa da dama sun faru cikin su hadda zana jarabawar su Farida kuma alhamdlillah duk cikin ajin su daga maza har mata babu wanda ya kai Farida da kuma First Lady cin jarabawa, hakan ba ƙaramin daɗi yayi wa Galadima ba dan har walima ya haɗawa ƴar tashi saboda tsabar farin ciki gashi kuma babban ɗanshi shima ya dawo ya kammala karatun shi dan haka walimar ta koma party dan maza da mata suka taru aka sha chasu.
Farida kam taga ƙauna acikin gidan Galadima dan kowa yasan ta komai tare akeyi da ita dan kuwa suna nuna mata ƙauna dai-dai gwar-gwado.
First Lady dogayen riguna ta siya musu ita da ƙawarta sukayi anko dan ta sanar da Galadima cewar ranar walimar su itace ranar zagayowar ranar haihuwar Farida tanaso tayi mata ba zata saboda haka yasa ta shirya komai a ɓoye ba tare da sanin ƙawartata ba, har masu kwalliya ta ɗauko suka yi musu komai nasu iri ɗaya kamar tagwaye, masha Allah gaskiya sunyi kyau sosai fiye da yadda kuke tinani.
Walima aka farayi sannan First Lady tace, "my sister kizo mu shiga ciki ki sake kaya".
Dariya Farida tayi tare da kallon jikin ta tace, "wanne irin sauya kaya kuma bayan na jiki na?".
Marai-raice fuska tayi tace, "dan Allah ki taso mana, karki bani kunya akwai dalilin da yasa hakan".
Ganin yadda tayi mata yasa tace, "to, muje shikenan?".
Kai ta ɗaga tare da kama hannun ta a hankali suka koma cikin gidan, wanka tace tayi, amman cikin rashin fashimta Farida take cewa ita baza tayi wanka ba ta goge kwalliyarta.
Dariya First Lady tayi tace, "ai wata za'a sake miki idan kinyi wankan karki damu".
Wankan tayi tazo aka sake mata sabuwar kwalliya, masha Allah tayi kyau fiye da ɗazu wata doguwar riga ta sake bata ta saka aka kafa mata ɗauri, ita dai kawai kallon su takeyi dan abun yana bata mamaki ta kasa gane me hakan yake nufi.
Maman First Ladyce ta shigo ɗakin da wani takalmi mai tsini tace Farida ta saka su fita, hakan kuwa akayi suka fito, abin mamaki shine bata ga kowa a gidan ba sai su kaɗai sai kuma Yaya Kamal da Aunty Zubaida kanta ne ya sake ƙullewa.
Bata sami damar tambayar ƙawartata ba sabo da mutanen da suke tare dasu haka aka kawo mota aka ɗauke su basuyi nisa sosai ba taga an shiga wani gate motoci ta gani a harabar wajen binsu kawai take da kallo dan idan banda faɗuwar gaba babu abin da yake damun ta.
Kama hannun ta Momyn First Lady tayi suka shiga wajen, kai gaskiya wajen ya ƙayatu sosai kawayen su ta gani da anko ajikin su sune suka taso suka shiga bayan ta, ita kuma suna gaba ita da Momy da First Lady, flowers ake watsa musu suna taku a hankali cikin isa da gadara da kuma taƙama har suka kai kan step suka zauna Farida tana tsakiya First Lady a gefan ta Kamal a ɗaya gefen.