💗💗💗💗💗💗
SON RAI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗~NA~
*AYSHA A BAGUDO*
~DEDICATED TO~
HAJIYA MARYAM_(JIKAR KULU )_
*Tun a farkon tafiyar nasan ke din masoyiya ce ,na saudakar da wannan labari gareki domin Kin cancaci fiyye da haka agurina ,kin nuna min kauna ta gaskiya ,kin soni da zuciyarki da gangar jikinki ,babu abinda zance sai godiya 👏🏻 Allah ya barmu taren tare, Allah ya rabamu da sharrin mayun media , Allah ya raya mana mardau's"*
warning!!!
don't read my novel , if you know ,you are not married... ❌❌❌coz oll my book contains only for mature people ,
if you read it, is for your own risk ooooooo ......🙅🏼♀️WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
Page 7"Wallahi umma ba turaren kowa ne a jikina ba, Wanda nake amfani dashi "
"Karya kike yi , dan ubanki wannan ba kamshi turarenki bane ,ta jijigata tare da makata akan kujerar three sister har school bag dinta na fad'uwa "ni zaki yiwa karya yesmin ?
"Yesmin bin maza kika fara?
" ko wasa da maza kike yi school ?Cike da matsanancin tsoro da gigita tace "Allah umma ba..bana bin maza "Kuma bana wasa da maza "
"To kamshi turaren uban wa nake ji a jikinki, wannan dai ba kamshin turaren da muke amfani dashi bane a gidan nan , zaki gaya min gaskiya ko kuwa sai shake miki wuya na kasheki ?
Jikinta na tsuma while hankalinta ya sake tashi, ganin mahaifiyarta na k'ok'arin ,gano wani Abu a dangane daita "kiyi hakuri ..!
"kiyi hakuri !! umma , ni dai bansan nayi amfani da wani turare bayanmu wanda na fesa daga gida ..Aiko mahaifiyata tayi kanta gadan gadan tana k'ok'arin take Mata gefen ciki ,sai ga habib ya sanyo Kai cikin parlour'n, da sauri ya k'arasa ya shiga tsakani "kina hauka ne hafsat ko me ?
"Yar tawa guda da Allah ya mallaka min duniya da lahiri kike k'ok'arin kashe min ta ?Hafsat mahaifiyar yesmin ,ta tsaya tana dubansa ranta idan yayi dubu to ya sake 'baci , gabad'aya ilahirin jikinta rawa yake taji haushin dawowarsa ,taji haushi da bata ci kaniyarta ba kafin ya shigo ,dan tasan babu abinda ya tsana a rayuwarsa kamar dukan yaran , bare yesmin daya d'auki soyayyar duniya ya d'aura mata "
"Kin yi shiru kina kallona kashe min ita zakiyi ko kike nufi ?
Naunayen ajiyar zuciya ta sauke saboda ganin yadda ransa ya 'baci ,sannan ta girgiza masa Kai al'amun a'a kana ta soma magana cikin fushi "yesmin bata jin magana .....
"Zataji da izinin Allah "
" kullun furucinki bai wuce bata jin magana ,ta'ba jin magama ba , dukan da kike mata bashi zai sa taji ba ,nasiha shine farko ,ni dai gaskiya bana son wannan duke duke duke , ya k'arasa maganar yana duban yesmin dake rawar jiki "me kika mata take neman kashe min ke ?
Yesmin ta sunkuyar da kanta tana zubar da hawaye sannan muryarta can kasa kasa tamkar mai koyon magana tace "dady Wai ...Wai ...sai Kuma tayi shiru ta kasa k'arasawa "Wai me ?
Tayi shiru taki cewa komai ,sai numfashi da sheshekar kukanta ke tashi a parlour'n ,habib ya waigo inda hafsat take tsaye cike da matsanancin jin haushinsa yace "me tayi miki ?
"Sai yanzu zaka tambayeni abinda tayi ?
"Cikin ni daita wa yafi cancaci ka tambaya tukuna ?
"Gata nan sai ta fad'a maka abinda tayi "tana gama fad'ar haka ta juya ta shige d'akinta ta banko kofar da karfi tana haki ..
YOU ARE READING
SON RAI
عاطفيةson rai ya kunshi abubuwa kamar haka, sansar soyaya cin amanar amintaka ..