💔CIWON SO💔
NaHafsat (Hafsy baby)
*No..16*
Nasaudakar da wannan page din gareki ( Mumcy husnah)
Allah yakara lafiya.Safeeya Gabanta na faduwa tanufi office din Dr Ahmed Tayi sallama yabata izinin shigowa jikinta nadar nadar.
Tace sir ga papers din OK, yasa Hannu yakarba Yacemata thank you, tajuya. Tafita
Dr Ahmed yabita da kallo Har tajuya tafita,
Muryata kawai dayaji yasa shi wani farin ciki. Da nishadi.
Safeeya nakomawa Meenat tare ta sister wani wulankacin yayi miki ne. Safeeya tace girgirza Mata Kai tace A,a.
Lokacin tashinsu school yayi sunnufo zasu dauki Mota suga Dr Ahmed tsaye wajen Motar shi yana latsa waya, har suka shiga suka tafi.
Nan ko Ba latsa wayar yakeba kallon safeeya yake Afaikace. Har sukaja motar suka tafi. Sannnan shima yashiga tashi.(Ciwon so fa yakama Dr Ahmed)
Abangaren Safeeya Kuma har suka isa gida datuno Kalmar thank you,
Da Dr Ahmed yafadamata sai taji kawai cikin Nishadi, Har wani murmushin farin ciki take.
Suna zaune Suna cin Abinchi Meenat kecema Safeeya gaskiya sister nayi mamakin Dr Ahmed,
Safeeya tace wurin me kenan, tace yadda yacanzamiki mana,
Rannnan fa har tambayar sunanki yayi, yau kuma harda cewa ki tatttara papers kikaimashi,
Bakiji yadda class Ake surutun hakaba Wallahi,
Safeeya saidai tace uhum sukacigabada da cin Abinchi, Bayan sun idar ne lokacin sallar La' asar ne suka tashi sukayi.
Bayan sungama sukadawo Falo. Suna Kallon AREWA 24
Suna shirin Muna Kwarya
Umma daman batanan tafita zuwa Gaisuwa matar Abonki Abba tarasu a sanadiyyar hadarin mota,
Bangare Dr Ahmed kuwa yana shiga gida ya iske hajiyarsa tayi tagumi Har yayi sallama batasan yashigo ba,
Saida yazauna yataba Hannunta Sannan ta firgita Ahh Ahmed yaushe kadawo ne, yace nashigo ita sallama bakiji Ba, ne meke damunki Hajiya sai kawai yaga Hawaye sunbiyomata mata, Ahmed yace meke damunki ne Hajiya harda Hawaye don Allah kifadaman kowani laifi na Aikata gareki bansani Ba,
Hajiya saudat tace babu Abinda kayiman Ahmed Ina tunanin yan uwana Yaya sule, da yaya mustapha,
Tunkafin A haifeka rabon danasu idanuwana Basan suna da raiba ko sun mutu, nan tabashi Labarin sanadiyar Batansu, Dr Ahmed yaja Numfashi yace ki kwantar da Hankalinki Hajiya insha Allah inda rabon zaku hadu zaki gansu. Nan ya kwantar. Mata da Hankali,
Yatashi yashiga ciki yawatsa ruwa yayi sallar la'asar yahau gado. Yakwanta,
Yajawo wayarsa yakira Amininsa wato Hafiz, suka sha firar su irinta Abokai.
Bayan sungama wayar Dr Ahmed yaruntse idanuwansakawaiyaga saffeyya nayi mashi Murmushi, Dr Ahmed yayi saurin bude idonshi yatashi zaune yace Meke damuna Kar dai ciwon so yazautani ita batasan inayiba ( haka dai kace)
Amma tayaya Zan furtamata ne can kawai naga yayi murmushi nikaina Hafsat basan mumrmushi meye ba.
Amma mujezuwa
Saffeya da Meenat ce zaune Safeeya nayima Meenat calabar umma Kuma tana zaune suna fira jefi jefi Saiga maigadi yashigo yayi sallama ya agaidasu yace Hajiya wai Ana Neman Hajiya safeeya waje wani mutum yace nakira mashi ita, saffeya tace ni Akace kakira, yace Eh,

YOU ARE READING
Ciwon So
Mystery / Thrillerta tsinci kanta cikin Ciwon so malamin ta Tasha kuma Alwashin ko ciwon son shi zaya kashe ta bazata taba zubar da Ajinta ta fur ta mishi soyayar ta ba ya Abun ke yake..kubiyoni