💔CIWON SO.. 💔
41...TO END..
41
TUNA BAYAAbba yadora yace bayan Baba yakawo makaranta bekara waiwayrmu.
Gashin malamin Azzulumine inkaje bara kadawo kasamo Abinchi kwacewa yake,
Dahaka mukai tahakuri domin bamu da makwancin kwana sainanan
Anahaka nida mustapha muka Fara shiga kasuwar central market munadago muna samun Abinchi dazamuchi muka daina bara,
Damunyi dako munchi Abinchi lokacin tashi yayi sai mutafi makaranatar da Akawomu, mu kwanta daan tashi dasafe munyi karatu, Antashi ma karanta sai mutafi, cikin kasuwa, ko makarantar marece daake zama bamu zuwa, Amma malamin besaniba domin shi babu ruwanshi,Anahaka wata Rana nadauko ma wani Alhaji kaya, shinkanfa yabude boot domin nasakamashi,
Ashe ya fiddo wata jakka baka.
Ya aje bayan nasa masa shinkafa yarufe boot din. Ban luraba sai daya tada naga jikka Aje nadauka nabishi Dagudu inbashi domim ya manta Amma nakasa cimmashi,
Nadauki jikka nan na nufi wajen mustapha nace mustapha kaga Alhajin danayima dako yamanta jikkashi,
Mustapha ya Amsa yace mugani mustapha yana Amsa yabuda yagani yana budawa yaga dame dame kudi yace yaya sule!!! Kudi ne ciki,
Naduba naga kudine ciki nace rufe mustapha, nace taso muje,
Nan najashi muka nausa canciki inda babu mutane kuma nagaka babu mai hangenmu nayi rami na rufe jikkanan,
Kullum rokonake Allah yahadani dawannan mutumin.
42
Kwatsam rannan ina yawo cikin kasuwa naga wannan mutumin yashiga wani shago naji rash har yafito, nabishi daga baya nace Alhaji, yawaigo dominshi har yamanta dana taba daukarmasa kaya, yace yaakayi yaro nacemasa Alhaji kamantani ne,
Nine wadda yataba daukar maka shinkafaa har kamanta wata jikka,Dasauri , hannu na cikin murna yace nataono yaro nacemasa muje nadaukomaka muka nufi har inda na binne jikka, nabashi,
Yabuda yaga kudin yadda suke haka suke, yarufe yace Alhmdlh nagode nagode. Yaro naji dadi,
Yasunanka nace masa sule yace suleman nagode, yace dan wane Gari nacemasa rimi, yace Kai daya ne nace nida kanena ne,
Daganan Alhaji Muhammad yafara taimakonmu nida mustapha, yabudeman shago cikin kasuwar central market muna saida Atamfofi,
Alhmdlh muna samu dganan Har Alhaji Muhammad yabanj jari nakaina Aruyuwata bazan taba mantashi,
Dagannan nace mustapha yafara zuwa makanta yabarni shagon
Daganan akayimasa cukun cukun takardun primary kawai yatafi secondary,
Yanabarina shago nikuma,Munata sanaarmu cikin rufin Asiri, har yakammalaa
Yatafi FCE can suaka hadu da murja suka Fara soyaya ,
Akace yaturo iyeyensa Alhaji Muhammad yayi mana tsaye har Akayi bikinsa,Nan muka yanke shawarar tafiya dauko saude munje mun isa lafiya Amma bamu Bari kowa yasan dazuwanmu ba sai Abokina Ilu nan yake gayaman bayan tafiyarmu Anyi bikin saude da Iro,
Subar garimamn
Nan ranmu yabaci kowajen maifinmu bamuje ba domin munsa bamu gabanshi Azzulumar matarshi tarabamu dashi,Saidai mustapha yayi shekara 5 da Aure sannan nayi na Auri Khadeeja sannan An haifi haidar yana shekara 4 tanazuwa sayayea shagona,
Nanma Alhaji Muhammad yayimani tsaye akayi bikina Aruyuwata bazan manta Alhaji Muhammad ba Allah yajinkanshi,
Khadeeja haihuwarta na farko ta haifi hassana da hussaina, wato saffeya da Ameena,
Daganan haihuwarta ta tsaysmata, shima mustapha haka,Daganan muka bude company mustapha yana zuwa kasashen waje sari,

YOU ARE READING
Ciwon So
Mystery / Thrillerta tsinci kanta cikin Ciwon so malamin ta Tasha kuma Alwashin ko ciwon son shi zaya kashe ta bazata taba zubar da Ajinta ta fur ta mishi soyayar ta ba ya Abun ke yake..kubiyoni