💔CIWON SO💔
Na
Hafsat ( Hafsy baby)Da sunan Allah mai rahama mai jinkai.
*NO...1*
Yan Mata guda biyu suna ta shiri zasu school ad'auki wannan a shafa wannan cikin sauri Meenat tad'auko kaya tasa Amma safeeya batada niyyar tashi a bakin mirror har Meenat tasa cikin fad'a Meenat tace "Amma kinsan yau muda lecture d'in Dr Ahmed kuma shine first, kuma kinsan idan ya shiga class babu wadda zai Kara shiga Amma kintsaya sai wani lindar fuska kike''. Safiyya tace "sorry, sis yanzu Zan tashi kikara hakuri. Tana idarwa ta wuce ma' adanar kayansu(wadrope) tasa wani red din material Masha Allah tayi kyau Abinka da farar Mace suka fito suka iske umma da Abba bisa dinning table domin break fast had'a baki "morning umma, morning. Abba, umma" Abba suka ce lafiya twins din Umma da Abba Sukaja kujera suka zauna sharp sharp sukayi break fast. Suka mike "umma nd Abba muntafi school". Sukace "A dawo lfy". Suna. Fitowa safeeya tace "pls, my sis kiyi driving zuwa school banason b'ata kwalliya na. Meenat tace chabb!! Sai dai muyi late sai in natuk'amu cikin fuskar rarrshin safeeya tace "pls my sister nandai ta rarrsheta sukaje ( ummaru musa yar aduwa university).bayan sun isa suna shiga Suka nufi class suka zauna ko 5 minutes baayi ba sai ga Dr Ahmed.ya shigo nanda kowa ya shiga hankalinsa yan Mata kuwa kowace jiki yace morning class. Sukace morning sir, yarubata test bisa Allo kowa ya firgita da hakan 30 mints yabada kowa yagama. Nan safeeya ta kalli Meenat masu niyya suka Fara masu maida hankali Akan Abinda Ake saffiya ta tambayi wani question tabata ganeba Dr Ahmed ya Lura da itah yace "ke get out!, tace "pls. Sir Am sorry" yace "I say get out" cikin sanyi jiki ta tashi tabar class din.
💔CIWON SO💔
Na
Hafsat ( Hafsy baby)
*NO..2*
Safeeya na fita ta nufi wani wajen da babu mutane sosai tazauna tayi tagumi tafada tunani zuciyata meyasa kikayiman haka nafad'a cikin son Dr Ahmed mutumin daya tsane ni bayason ganina ba batasan sadda hawaye ke tsiyaya da fuskar ta ba saboda CIWON SO Dr Ahmed ke damunta kullum kara yawa yake tare da itah. Kamshi wani turare taji mai kamshi ya ziyarci A hanci tadago fuska ta ga waye sai sukayi Arba da Dr Ahmed ya wuce da barandar datake zaune. Can taji wasu yan Mata na gulmar suna cewa "keh Aseeya wallahi Dr Ahmed ya hadu Amma ya cika miskilanci Rannan naje office din Amma kinga fuskar yadda kikasan bataba dariya haka yadaure fuska nayi sallama nashiga nace sir inayini cikin daure fuska ya Amsa yaceman meke tafe Dani nacemasa Dama wutowa nazo yi nace bari nashigo bebari na ida ba ya kwasaman wata. Tsawa yace nabarmishi office dinshi cikin sanyi jiki. Nafito". Safeeya taja wani tsaki tana takaicin wasu matan dake bada Kansu ga wasu mazan domin ita ko ciwon so zai kasheta bazata taba tarar dr Ahmed tace tana sonshi ba. Can kuwa bayan Meenat sun fito tana ta neman safeeya. Tarasa can taga wasu wadda. Suke gaisawa. Ta tambyesu sunga safeeya suka ce tana baya can tanufa ta iske ta zaune. Tace shine zaki bani wahala ko tace sorry sis Meenat ta nemi wuri ta zauna tace "wai sis mekika yima Dr Ahmed yake miki haka ne?" safeeya tace "wallahi sister bansan Abinda nayi masa yakeman haka". Tace "yanzu yazakiyi da test din datawuceki ne yau. Kizo muje office dinsa mubashi hakuri" safeeya tace. "Sister kinsan hali Dr Ahmed bazai yiba tace kedai tazo muje. Cikin sanyi jiki ta tashi suka nufi Amma sai sukayi rashin sa' a office di'n kulle yake...
💔CIWON SO💔
Na
Hafsat (hafsy baby)
*NO.. 3*
Cikin damuwa Meenat tace "kinga bayanan ko? sis "safeeya tace "Eh mujuya gobe nashigo dakaina da munshigo school din nabashi hakuri" suka juya suka koma cikin makaranta bayan sun idar da lecture din dasuke da itah suka hau mota suka nufi gida suna isa gida suka nufi dakinsu suka wasa ruwa Dama lokacin sallar Azahar yayi suka sallah Meenat ta Lura yau safeeya bata cikin walwala sosai bata surutun nan Nata data Saba tace "wai sister meke damunki na Lura tun school bakya walwala meyafaru ne ko tun abinda Dr Ahmed yayi miki baki manta bane?". Safeeya tace "yazaayi na manta sis mutumin yatsaneni ban San Abinda nayimasa sister Abinka kadan zan masa ya disgani cikin mutane kina kallo yau fa bani kadai nayi magana Amma nikadai ya hango yafiddo ni''. Bata Ankara sai hawaye shar shar. A fuskarta domin wani ciwon so Dr Ahmed ke tasomata A zuciya Meenat tace safeeya meyakai na kuka safeeya tace Abinda yakeman yasani kuka( batasan ciwon so Dr Ahmed bane yasa safeeya (Hawaye) Tace "kiyi hakuri taso muje kinsan Umma batasan dawowar mu ba" suka nufi d'aki umma su suka isketa zaune bisa darduma tana lazimi sukayi sallama suna shiga tagama laximin bayan ta idar tace "yan biyun umma Andawo?'' "Eh, umma mundawo har munyi sallah ma" tace "toh madallah kuje ga Abicin kucan bisa dinning koh". Sukace "to umma" suka nufi dinning safeeya tura kawai take domin batasan Meenat tafahimci halin datake ciki. Bayan sun idar suka tashi suka nufi dakinsu.
Bayan sallar isha' I suna zaune falo da suna kallon labarai da Abba su duka dai. Har wajen karfe goma. Sannan sukayi ma iyayen nasu sai da safe suka nufi dakinsu. Meenat naxuwa tafada gado domin bacci takeji sosai. Safiyya tabi bayan ta Amma takasa Bacci tunani Dr Ahmed kawai take sai juye juye take.har dai bacci yadauketa. Asuba tagari
YOU ARE READING
Ciwon So
Gizem / Gerilimta tsinci kanta cikin Ciwon so malamin ta Tasha kuma Alwashin ko ciwon son shi zaya kashe ta bazata taba zubar da Ajinta ta fur ta mishi soyayar ta ba ya Abun ke yake..kubiyoni