BABI NA TAKWAS

345 13 0
                                        

Ƙarasawa tayi xuwa cikin gidan su Samira,bayan sun gaisa da mai gadin tare da fada mishi wajen wanda ta zo.

Gidan su Samira apartment dan matsaƙaici mai kyau kasancewar baban su babban ma aikacin gwamnati ne da yake aiki da NEMA (National Emergency Management Agency)yana da rufin asiri sa dai dai shi

Bayan shigar ta,wata yar matashiyar mata ta tarar a falo tana goge goge,suka ta gaisa,sannan ta mata bayanin ta zo wajen Samira ne,kafin tayi hanyar dakin su samiran

Su samiran sun kasance su biyar ne a wajen iyayen su Kabir shine babba yana da mata yana aiki a kano a FAAN,Kamal,Salma,Samira sai autar su Amira

Da sallamar ta ta shiga dakin,sai ta hangi Samiran akan gado,ta tayi kwanciyar ruf da ciki da waya a hannun sai typing abu take yi,bata ma ji shigowar ta dakin,ai ko ta daidaici bayan ta ɗaƙa mata duka

Banƙarewa tayi don taji zafin dukan tare saurin juyowadon ganin wanda ya mata wannan dukan wallahi su ƙwashi yan kallo shi

Sai dai ta ga Mimi a tsaye tana mata dariyar mugunta,ai sai tayi cilli da wayar hannun ta kan gado,ta taso da sauri ta rungume ta tare da haɗawa da ihu jin dadi tana fadin

"M.bash dama ke ce? Shine kika min wannan uban dukan a yana tana kara sosa wajen,yaushe kika shigo?ban ma ji shigowar ki ba,taho ki zauna"ta fada tare da jan ta zuwa kan gado ga farin ciki a kan fuskar ta na ganin kawar ta ta

Ita ma Mimi tayi farin cikin ganin Samiran sosai ta dan harare ta ,tana kara dariya ta ce

"Ai dukan ne daidai da ke ashe har na shigo dakin nan baki ma sani ba kin tasa waya a gaba sai rubutu kike yi,wai  me ma kike yi ne da ya dauke miki hankalin haka?

Murmushi Samira ta yi,tare da gyara zama ta kafin ta ce

"Hmm M.bash wallahi fa wani ne fa Allah ya hada ni da shi a kan Instagram dama friend dina ne muna dan gaisawa da ga ranan ya ga nayi posting wani hoto na,shikenan ya bi ya nace min,wai shi sona yake yi,in takaice miki dai,tun bana kula shi,har yanzu na dawo na fara bashi fuska,ban taba ganin sa face to face ba,ko a ig din ma ba posting hotonan sa yake yi ba,sai ranan ya zo muka hadu da shi,kin gan shi kuwa,OMG!guy din ya yi mugun haduwa kyau kamn shi yayi kan shi ,su nan shi Sam'an,shine fah muke soyewarmu,yanxu da kika shigo ma da shi din nake chatting ta whatsapp gashi ya mugun iya soyayya besty "ta karashe fada tana smiling

Mimi idanu kawai ta zuba mata tana kallon ganin yadda take ta jin dadi sbd labrin da take bata daga gani ta gama fada wa son sa sosai

"Samira nima ba zan gaji da jan hankalun ku ba,sau tari ƙyau ko haɗuwa ba su ne suke determining halayyar mutum ba,balle yan social media sabida yawancin su rayuwar karya suke nuna a can,alhali kuma rayuwar da suke yi zahirin su daban,wadansu kuma fake acct ma zaki ga suna using,bht hankalina ya dan ƙwanta da kika ce ya zo har kun haɗu,am really happy for u besty since u like him,pray shi ma he geniunely loves you kamr hakan,hakanan kar ki manta da Hadisin Manzon Allah(SAW) ya hore mu da in zamu so mutum,to mu so shi don Allah,in kuma zamu k'i mutum, mu k'i shi don Allah,don haka kar ki bari wani kyan shi ko wani ƙyale ƙyale ya rude ki,halin kwarai ake so a wurin mutum ,in yazo da kyan ma babu laifi,domin duk wadannan abubuwan za su iya gushewa,amma ban hali na gari

Samiran da tayi shiru tana jin duk maganganin da Mimi wanda ta san gaskiya take fada mata,ta dan sakin ajiyar zuciya tare da faɗin

"Besty na gode da shawarwarin ki,Insha Allah kuma zan yi aiki da su"

Tashi tana ƙara faɗin

ƘADDARA TA Where stories live. Discover now