*KUDI..*
_Kumbar susa_ !2
Bangaren amarya fatima kuwa bayan sun idda nafila shafin hira mai dadi mai tsafta suka bude tsakanin ta da angon ta alhj aliyu,acikin hirar har yake mata tambayoyi dayawa daya shafi addini wanda aganin shi ya kamata ace kowacce ya mace tana sane da su kafin auren ta
Yau dai Wani nishadi da kwanciyar hnkli ke ratsa shi wanda ya dade baiji irin sa ba,duk dama yasha gwada kawo mata amma Allah bai nashi nasarar samun nazama ba amma fatima ta dabance aransa
She feels so differnt with her،ita ba zabin mahaifiyar sa ko dangin sa bane old time love ce wanda ya sa rai ita zata warkan da zuciyar sa akan abunda daya dade yana damu wa da shi akan rayuwar auren sa.
Ko ba ace ba yasan matarsa ramlat tamkar buhun kaya ne akansa kamar yadda ta zame kashin kifi wajen uwar sa da kuma dangin sa.
Sudai Basu taba cewa ramat itace makasudin rashin zaman amaren nasa ba anma abun a fili yake tunda takanyi ikirarin bata taba bari anyi auren sa lpya batare da ta tada mumunnan hargitsi ba sai akan wannan.
Karfe 10cas agogon batman dake jiki bango ya buga nan alhj aliu ya mike ya shige closet domin rage kayan jikin sa
Inda amarya fatima take xaune kunya yama hanata motsawa mayafin ta kawai ta iya cirewa ta kishingide akan makaken gadon ta tana aduoin da malamai suka bataA haka cikin so da shakuwa alhj aliyu ya lallabata suka raya daren,cike da tatttali da nuna kwarancewar sa wajen iya nuna soyayya ya tarairaiye ta
Da shagwaban nata duk yabi ya like yana rarrashin ta don ko a cikin cikakkun mata masu niima yau ya dada sanin fatima ta dabance.
Tsaban ta wahala a hannun shi Ko bacci da kyar ta iya komawa,jikin ta yayi matukar kyau cikin nityn data sa dayake kalar ruwan powda ne da kyar ya iya runtsawa ya bar kallon ta
Da asubahi ma shi ya fara farkawa ya shiga gyara mata kwnciya ganin alamun ta jigata sosai a hannun shi ya sa bai tashe ta
Ba Kawai sai ya dora towel a kugun shi ya nufi bathrum abnsaMurdawa da Rufewar kofar sa yyi dai dai da bude idon ta,tarwal ta bude idon kamar wanda dama ba baccin takeyi ba
Innalillahi wa inna ilaihi rajiun take son furtawa Har Cikin ranta amma sai taji ta kasa yin motsi da lips din ta,ga sautin kiraye kirayen sallah memakon taji hakan ma sautin Kiran ramlat kawai takeji a kunnen ta ita da ilahirin jinsinf masihirin tan ta.
Ji tayi kirjin ta na bugawa a zauce zuciyan ta na wani irin kakarin tunxira ta ko xata fasa ihu amma hakan baiyu ba cikin zautuwa ta shiga finckewa ita kadai alaman tana neman taimako
Duk nishi da buge bugen dataso yi bata iyawa Wani irin bankarewa ma kirjin ta yayi kamar wacce aka daure ta,da kyar tayi wuf tayo jefa da dankwalin kanta tana yi tana mai mikewa tsaye kamar zautacciya
Wani irin numfashi mai ban tsoro taja Ba bata lokaci ta fixge jiki ta bude kofa ta bar dakin,daga ita sai nityn ta take tafiya babu dankwali bare aron slipers akafar ta cikin kiftawar ido da bude shi sai gata abakin makaken gate din gidan
Allah ne ya bar makansa sani yadda ta tsere ma securites ta shige ta kofar dake garkame da makullai wanda ba a ko sa lahadin bude shi ba
Hanya kawai fatima ta saita ta mike baji ba gani har sanda ta bace ma ganin kowa....
Jim kadan da Fitowar alhaj daga bathrum yayi zaman mamakin rashin samun ta akan gadon amma sai bai daga hankali ba sanda had yaga ya shafe awa guda baiji duriyar ta ba
Bayan ya kimtsa kansa tsaf ya shiga neman ta acikin gidan sai dai duk wanda ya tambaya sai yace masa shima bai ganta ba
"Wani irin bugawa kirjn sa ya shigayi Sam Baiji dadin hakan ba,dmin hakn ba komi yake shirin tuna masa ba sai amaryan sa na karshe wato Khadija da ake zargin itace ta dawo kurciyan da aka samo akan gado sa a ranar daren auren su.
YOU ARE READING
KUDI...kumbar susa!
RomanceYar cikin aminiyarta ta aure mata miji... komin nisan jifa kasa zai fado,haka ma komin nisan dare gare zai waye,qaddara zanen ubangiji ne ayayin da shi mugunta da jahilci kirkiran mutum ne...find out what happen when the unxpected meet the expected...