Couple Crush👫

134 11 5
                                    

REMINDER💕
And whoever fears Allah He will make for him a way out and will provide for him from where he does not expect. And whoever relies upon Allah – then He is sufficient for him. Indeed, Allah will accomplish His purpose. Allah has already set for everything a [decreed] extent." [Qur'an, 65: 2-3]
PS.
You can also call this Chapter Ramadan Bonus😂❤️for the sake of Ramadan i updated twice today💃😌
CC👫
Washe gari da taje school kasa zuwa ajinsu Ramlat tayi da break. Wani nauyi takeji zuciyarta da gangar jikinta sun mata.ta yaya ma zata hada ido dashi (ina ruwan ban saba ba.this is her first love)
Shikuwa da yaji shiru bata zo ba. Da kanshi ya tawo ajin nasu.da mamaki kowa a ajin yake kallonsa.kowa yanaso yaga wajen wa yazo dan bai taba shigowa cikin ajin ba.wajenta ya nufa hakan kuwa  ya kara mata wani nauyin akan wanda takeji.zama yayi a kusa da ita kafin yace Baby gani nazo tunda ke baki zo ba.cigaba yayi da magana ba tare da ya jira ta bashi amsa ba.abunka da wanda ya saba tsara yan mata.
        Tun Zarah na dari dari akan soyayyar har ta ware.dan Imran ya wuce tunaninta.toh ita da bata taba soyayyar bama ballantana tasan muhimman abubuwa akanta.Yaya Hafsat ce dai ta kusa da ita da tasan tana soyayya.ita kuma ba damuwa tayi da sanya kanta a wannna lamarin ba.har mamakinsa take at such a young age ya akayi ya iya soyayya haka.he acts bigger than his age. Da break kuwa yanzu shi yake dauko Ramlat su tawo ajinsu Zahra.a cewarsa Sarauniya ce ita....a makaranta kuwa in dai kace couple Crush toh su za'a nuna maka.ba wanda bai san da zaman soyayyarsu a makaranta ba.
      Lokaci yana ta ja.Soyayyar Zahra da Imran na dada yin Nisa.ga shi har sun fara Zana WAEC.daman baiyi Jamb ba.yace shi bawani cigaba da karatu da zaiyi. Business zaiyi.su da suka iya wahala sai suyi tayi.ba yanda batayi dashi ba amman yace he has made his decision.
A gida kuma ba wanda ya fuskanci halin da Zarah take ciki saboda bata bada kofar da za'a gane hakan ba.Abdool ne kadai yasani shima saboda School kuma ta ja masa kunne akan kada ya fadawa kowa.Yaya Hafsat ma da suke kwana su tashi tare bata da nutsuwar da zata tsaya gane wani chanjin da Zarahn tayi saboda shirye shiryen bikinta da ya rage wata daya.
Yau birthday din Zarah zata cika shekara 17.da yake a gida basa celebrating birthday batayi expecting ranar ta zama daban da sauran ranaku ba.ta dai san ta cika shekara sha bakwai.shikenan nothing more.wayarta ce tayi ringing dauka tayi tare da yin murmushi ganin wanda ya kira.cewa yayi baby fito ina kofar gidanku.tohm kawai tace masa kafin ta cewa Yaya hafsat bari na je wani dan ajin mu ne yazo wucewa shine yace bari ya tsaya mu gaisa.ba tare da tunanin komai ba tace mata tohm.Veil kawai ta dora akan Abayar dake jikinta ta fita.daman mama bata nan sun fita da Yaya mami siyo kayan bikin Yaya Hafsat.tare da abokinsa Aiman sukazo.gaisawa tayi dashi kafin ta juya kan uban gayyar.yaushe za'ayi party ya tambayeta.ce masa tayi bama celebrating birthday ai mu.toh fah yace kafin ya bude bayan motar ya fito mata da wani box ya mika mata yace ga birthday gift dina.kin karba tayi da farko sai da Aiman yasa baki sannan ta karba.sallama sukayi ta shiga gida.
     Da kallon son jin karin bayani Yaya Hafsat take kallonta.eh lallai akwai wani abu a kasa dan ta lura kwanan nan Zarah bata bacci da wuri.ga wayar dare wadda ita a zatonta ko da su Ramlat take yi tunda ita ba kasa kunne take taji mai take cewa ba. Zarah wa ya kawo miki wannan.zama tayi a darare sannan tace saurayina ne.tambayarta tayi wane shi? A ina kuma kuka hadu da shi?.fada mata tayi iya duk abunda tasani akansa....sauke numfashi yaya Hafsat tayi kafin tace Zarah kiyi a hankali.i can't tell you to unlove him tunda kin riga kin fara.amman So da kike gani abune mai wuyar sha'ani.amman a hankali in ka lakance sa sai ya zama mai sauqi.ballantana ku da kuke yara daga ke har shi.bana tunanin kuna da tabbacin abunda kukeji a game da juna so ne???.koma dai mene duk lokacin da kike da bukatar shawara ina nan.Allah ya shige mana gaba tace.Ameen Zarah ta amsa...tashin da yaya Hafsat tayi zata amsa waya shi yasa to koma kan zancen da zuciyarta take mata.anya ta yankewa kanta hukuncin daya dace.da sauri tayi fatali da wannan tunanin da ta tuno Imran da kuma yanda suke son junansu.
      A yau su Imran suka gama Exams gaba daya.murna yake kamar me zai bar makiyiyarsa makaranta wani bangaren kuma na zuciyarsa yana masa ba dadi.yanzu shikenan bazai rinka ganin Zarah ba.wata zuciyar ce tace masa inaa dole tasan yanda zamuyi mu rinka haduwa.haka dai suka rinka daukar hotuna har da Zarah.Instagram yaje yayi posting tareda tagging dinta.
         Yau gidan nasu Zahra a cike yake saboda yau ake kawo lefen yaya Hafsat.a hankali ta sudade ta fita daga gidan.daga chan bayan gidansu ta karasa wajen Imran da yayi parking.kallon ta yayi yana dariya yace kin ganki kamar wata mara gaskiya.dariya tayi itama sannan tace to ai mara gaskiyar ce tunda ba'a san na fito ba.suna cikin hira yace mata baby banga kinyi commenting akan picture mu da nayi posting a Instagram ba.cewa tayi ban gani ba ai.wayarta ya karba sannan ya shiga Instagram din.ai kuwa yayi mummunan gani dan wani abokinsa ya gani yayi mata sending DM wai yana sonta.ya tabbata tagging dinta da yayi anan ya samu username dinta don bai dade da bude mata account dinba saboda da batayi....lafiya tace masa ganin yayi shiru.ce mata yayi abokina ne ya miki sendn DM fa.dariya tayi sannan tace to ai laifin kane da kayi posting hotona kuma harda tagging kaga ai baka ji haushin sa ba.da bakayi posting ba ai ba zai san dani ba.aww laifi nayi dan nayi posting hoton mu?ke ai dadi ya kamata kiji I'm showing the world you're mine.kallon shi tayi kafin tace akwai bambanci tsakanin keeping a relationship private and keeping it a secret....a fusace yace bazan fasa abunda na ga dama ba saboda wasu.ganin ransa ya fara baci yasa tace bari nayi sauri na tafi gida kafin a fara nemana.
        An fara bikin yaya Hafsat yayin da gidansu ya kara kacamewa da Jama'a duk da su basa wani bidi'a a biki.walima kawai ake ta mata zallah in da ake kiran Malama tayi wa'azi.sai kuma daurin aure daga nan akai amarya.ita kuwa zarah dama ta samu ranar walima suka yi zancen su itada Imran.dan a yanda takejin zuciyarta yanzu a kansa babu abinda ba zata iya ba akansa.zuciyarta ta kekashe.shi kadai take gani.a haka aka gama biki suka sha kukansu itada Yaya Hafsa na rabuwa aka kaita Tudun Yola.
           Waya yake mamansa ta shigo.cewa Yayi ga mama nan Zarah ku gaisa.mikawa mamansa wayar yayi. in da sabo ta saba da wannan gaishe gaishen da yan matan Imran.ita duk daukan hakan take a yarinta ce kawai.karba tayi suka gaisa da zarah kafin ta bashi wayar ya kashe.ce masa tayi aiken ka zanyi gidan Yayan ka.matarsa zaka kawai food flask dinta.tohm yace sannan ya karba ya fito.ya na zuwa yaga kanwarsa wadda take binsa bata fi Sa'ar Zarah ba a compound din gidan tare da wani.wani kallo da ya mata sai da taji kamar ta yi fitsari a wando.karasawa yayi wajensu yace shige ciki dan uwarki.ai a guje ta shige.bin ta yayi shima yana huci.lafiya yayan nasu ya tambaya ce masa yayi yaya zance fa naganta tanayi a waje.kallonsa yayan yayi sannan yace kai yan mata nawa kayi.ohh ashe ba dadi.kai zaka batawa yayan wasu lokaci kai kuma naka kannen baza'a bata musu ba ko?to ni na bashi izinin ya ganta.sha sha sha mai shegen son kan tsiya.ajiye musu food flask din yayi ba tareda yace musu komai ba ya fita.
        A hankali tafiya tana kara yin nisa.Daman ance baka sanin wane  mutum sai ka kusance shi sosai.to haka abun yake.a hankali Zarah ta gane Imran mutum ne mai saurin Fushi ga zuciya da taurin kai.shi dole sai an bi ra'ayinsa shi kuma bazai taba bin naka ba.ashe wasu abubuwan da take ganin yana mata na doki ne.so da yawa rigimar tasu dukda haka dai yana sonta sosai.kawai dai tafiya ce tayi nisa halaye suka fito.
       A zaune suke itada Ramlat suna shirye shiryen saukar su da za'ayi Imran ya kirata.dauka tayi sannan tace tohm ta katse.tashi tayi tace Ramlat bari naje Imran yana jirana.kallon mamaki Ramlat take mata .Zahra gaba daya ta chanja.wai namiji ta macewa haka.
A haka dai da dadi ba dadi(through the ups and downs) suke tare.a haka Zahra take hakuri da halin Imran wanda a ganin ta shine abunda ake nufi da love is sacrifice.love is staying through it all.Zahra da Nadiya sun Gama school.wanda yayi marking Shekarar su biyu tareda Imran kenan..
Haka ta kwana tana tunano mafarin komai.yanda taga rana haka taga dare.kiran sallar Asuba da akayi shi ya saka ta tashi ta shiga toilet ta dauro alwala ta tada Sallah.a gaggauce tayi Adhkar dinta saboda wani kaikaiyi da idonta yake mata alamun bacci take ji. tashi tayi ta koma kan gado ta kwanta.

Tohh ga dai mafarin komai kunji.
Nasan har yanzu kuna da tambayoyi.
Ku cigaba da biyoni domin samun amsoshin tambayoyin ku da kuma samun wasu a gaba da tasu amsar suma.
Don't forget to Share NB with your friends(there's love in sharing u knw😉)
Again don't forget to vote 🗳 and comment💬

Northern BelleWhere stories live. Discover now