*RAYUWAR KHADIJA*
Story and written by *Faridah*🌹
*jikarbello*@wattpad
_Bismillahir rahmanir Rahim. Da sunan Allah mai rahama mai jinkai,tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyen halitta annabi Muhammad (S.A.W) da ahalin gidansa da sahabbansa da masu bin tafarkinsa har izuwa ranar saka mako. Ina godiya da Allah daya bani ikon fara rubuta littafina na farko mai suna *RAYUWAR KHADIJA* kuma inafatan yadda na fara lafia Allah ya bani ikon kamallawa lafia._
*Godiya ta musamman ga Zeeneert novels da Zulaihat ibrahim abdulhamid su suka karfafa min gwiwar rubuta novel dinnan sukace farida kije zaki iya Allah ya bada sa'a. Zeeneert and zulaihat ina alfahari daku Allah yabar zumunci*🥰
*Amin*
*Part 1*Khadija! Khadija! Khadija! nikam ba khadija nake kira bane dan ubanki? kina inane kikai min shiru saboda kin mayar dani sa'arki ko?
"Inna ganinan" khadija yar kimanin shekaru goma ta fito daga daki tana amsa kiranda Adama ke mata. budar bakin adama sai cewa tayi "dan ubanki ban hanaki kirana da inna ba? niba uwarki bace danni Aisha kadai na haifa ita take da ikon kirana da inna bakeba domin uwarki Sa'ade ta dade da zama kwarangwal a kabarinta dan haka kada ki kara kirana Umma kina jinako? shegiya me kinibibin tsiya. maza dauki bokitinnan kije tuka tuka ki debo min ruwa kidawo ki dafa abincin kuma wallahi kika dade na lahira saiya fiki jin dadi"
Haka khadija ta dauki bokiti tana tafe tana kuka. a hanyar tafiyarta ne tahadu da kawarta mai suna Zainab,
Khadija khadija khadija a firgice khadija ta juya tace "naam Zainab"
Zainab da mamaki tace "tun dazu nake miki magana kinmin banza lafia naga kina kuka?"Khadija share hawayenta tayi sannan tace " Zainab kinfi kowa sanin halin danake ciki yanzu haka. Inna ce ta aikeni tukatuka in debo ruwa indawo inyi girki" kiyi hakuri khadija watarana sai labari sannan ki cigaba da addu'a kinji,muje in rakaki ki debo ruwan.
Toh Zainab nagode Allah ya bar zumunci.
Suna isa tukatuka khadija ta debi ruwan suka kama hanyar dawowa gida,a hanyama Zainab ta cigaba da bata shawarwari da kwantar mata da hankali.
salamu alaikum! Khadija tayi sallama akofar gidan. toh bakar munafuka sai yanzu kika gadamar dawowa? shegiya tsinanniya wallahi saina kasheki da wahala agidannan, tassssssss jikike Adama ta kwadawa khadija marinda saida ta fadi kasa saiga bokitin ma yabiyota kasa ya fashe,aiko Adama tasake jawo khadija sai duka kamar an aikota can saiga Mallam Dauda nan ya shigo "ke Adama bana hanaki dukan yarinyaran bane acikin gidannan? duk biyayyar datakeyi miki bakya gani? tayi miki bauta keda yar'ki amma sakamakonta shine duka da zagi fisabilillahi? tukunnan ma ina ita Aishar take daba zataje debo ruwan ba? ni wallahi 'Yata ba kalar wahala bace ita wannan din meye anfaninta daman? anfaninta shine ta bauta min,danma bakasan irin tsanar danayi mata bane Mallam, na tsani khadija!
Da mamaki Mallam Dauda yace "Adama agabana kike cewa kin tsani Yar dana haifa? Toh wallahi kika kara sai na saba miki domin da khadija da Aisha duk daya suke agurina, nina haifesu sabida haka bazan taba nuna musu banbanci ba".
"Uhm banbanci na nawa kuma ai ba tun yauba nasan kafi son khadija akan shaleleta to wallahi yanzu nafara sakata bauta.
"haka kika fada?"
"Eh haka na fada"
"Shikenan kije duniyace ta ishi bagaruwa jima sannan kibi duniya a sannu wallahi".
"Uhmm! Ahayye chassssss asssss. sannu akarama kallahu Mallam Dauda ai bansan ka fara wa'azi ba mtsssssswwwww, kaga banida lokacinka".
Haka Adama ta wuce Mijinta tayi shigewarta daki.
Mallam Dauda ya dago khadija daga kasa yace "Khadijata kiyi hakuri kinji watarana sai labari, bayan wuya akwai dadi".
Shin wanene Mallam Dauda?
Mallam Dauda asalinsa dan garin badume ne dake karamar hukumar bichi kasuwancine yakawoshi cikin birnin kano yake zaune a unguwar dorayi babba yanada Mata biyu Adama itace uwar gida shekararsu hudu da aure Allah bai basu haihuwa ana haka ya karo aure inda ya auri Sa'ade Yar kanin mahaifinshi. tarewar Sa'ade keda wuya Allah ya bata ciki ta haifi 'Yarta mace kyakkyawa ranar suna aka rada mata suna Khadija, tun daga lokacin Adama take nunawa Sa'ade da 'Yarta karan tsana ana haka kwasam ciwon kai ya kama Sa'ade kwananta biyu tana jinya Allah ya karbi rayuwata ta mutu tabar 'Yarta Yar wata shida da haihuwa alokacin kuma Adama nada ciki wata daya. tun daga lokacin rikon Khadija ya dawo hannun Adama inda bayan wata tara Adama ta haifo 'Yarta Aisha,ta dauki son duniya ta dorawa Aisha yarinyar ta taso da rashin kunya dan haka Adama taiwa Aisha hudubar shaidan kancewa kada taso Khadija wannan kenan!
Cigaba labari
Ba irin wahalar da Adama bata ganawa Khadija dukda karancin shekarunta haka take hakuri da Matar Baban nata ahaka Mallam Dauda ya saka yaranshi a makaranta brains college dake chirinchi. Aisha bata son karatu duk lokacin da Aisha taki zuwa makaranta to sai Adama tasan yadda tayi Khadija bataje makaranta ba. wata rana Mallam Dauda ya fito zai tafi kasuwa daidai kofar famfo mota ta bigeshi mai motar daya bigeshi ya gudu mutanen gurinne suka samo motar da aka kaishi asibitin murtala.
Pls fans votes da comments dinku shi zai bani karfin gwiwar ci gaba da rubutun Rayuwar khadija. Nagode
YOU ARE READING
Rayuwar khadija
General Fictionkhadija marainiyace ta taso cikin kuncin rayuwa a hannun matar mahaifinta mai suna Adama Wanda tasha wahala sosai amma daga baya ta samu ingantacciyar rayuwar da bata samu ba abaya.