Page 5

90 14 2
                                    

*RAYUWAR KHADIJA*

Story and written by *Faridah*🌹

*jikarbello*@wattpad
.

Part 5

Khadjida ta Shiga gidansu da sallama, ta suguna ta gaisheda Adama, amma ko kallon arziki bata samu ba, haka ta karasa daki ta cire kayanta ta saka wata doguwar riga ta fito sakar gida ta dauki sinsiya ta fara shara.

Bayan Khadija tagama sharar ta dauki buta zatayi alwala sobada an fara kiraye kirayen sallar magariba, haka tayi alwala tayi sallah tayiwa mahaifinta da mahaifiyarta addu,a.

Tana idarwa ta shiga daki tayiwa Adama da Aisha shimfida kafin akira sallar isha haka tayi ayyukanta tagama, lokacin sallar isha nayi ta dora alwala tayi sallah, Bayan ta idar ta dauki tabarma ta tafi soro ta kulle kofar gida sannan tayi shimfida ta kwanta , tana kwance tanata tunanin mahaifiyarta da Abbanta har barci ya dauketa.

Asuba nayi tayi maza ta tashi ta shiga bandaki tayi wanka tayi alwala tayi sallah bayan ta idar tayi azkar da addu,a samun waraka a rayuwarta data mahaifinta , sannan takoma bacci, safiya nayi ta nannade shimfidarta ta shiga daki ta ajiye lokacin Adama ta tashi ta gaisheta amma ko amsawa Adama batayi ba .

"Haka ta shige ta fara aikin gida, tayi shara sannan ta dauki bokiti ta jido ruwa daga tuka tuka, saida ta cika gaba daya robobin ruwan gidan sannan ta hau aikin wanke bandaki bayan tagama ta tambayi Adama meza,a dafa akai asibiti? Budar bakin Adama sai cewa tayi Ubanki za,a dafa yau babu komai dazanyi wahalar baki ki dafa inkin gadama kije asibitin yau Inba haka Kiyi zamanki kinji ko.

Zanje inna, Haka Khadija tashiga daki ta dauki hijabinta ta saka ta fito, ta shiga gidansu Zainab ta gaishe dasu Mama Asabe, Mama yau inna
Adama tace babu abuncin daza,a kai Asibiti , kyaleta Khadija bari na dafa ruwan shayi tunda yau babu makarantar boko saiku tafi asibitin tare da Zainab kinji, to Mama mungode Allah yasaka da alkhairi, Mama Asabe ta dafa ruwan shayi ta zuba a flask ta dauko burodi ta hada dashi a cikin leda viva, sannan tace , kuzo Ku karya Ku tafi kunji yan albarka, suka amsa da to Mama.

Bayan sun gama cin abinci Mama Asabe ta basu dari biyu kudin mota sannan tace musu anjima yayanku Khalifa zaizo kawo abuncin Rana inyaso saiku dawo tare suka, amsa da to Mama mun tafi, Allah ya kiyaye Ku kula da kanku kada wani ya tsayar daku Ku tsaya innaji labarin haka nida kune maza Ku tafi Allah ya tsare.

Karfe sha daya na safe suka isa Asibitin murtala kai tsaye emergency suka shiga dakin da baban Khadija yake nan sukaga wayam babushi, nan take jikinsu ya fara kyarma kardai mutuwa yayi shikenan Zainab tawa ta kare, taki bata kare ba Khadija insha Allah sai baba yaga aurenki.

Gaba daya suka juyo a sukwane ganin wayake magana sai sukaga ashe yaya Balarabe ne, ya nufosu yana murmushi , sannan yace musu, likita ya mayar damu dakin maza manya da,aka yiwa aiki amma naje naga dakin mutane sunyi yawa shine na bugawa mai gari waya nasanar dashi halin da,ake ciki , dazu yasa aka Turon da kudi muka kama amenity wato dakin mutum daya saboda ba,ason hayaniya tayi masa yawa, shiya sa yanzu nazo in tafi daku dan kada Ku zaci wani abunne ya fara, sai a sannan suka saki ransu, Yayanmu ina kwana , lafia kalau Khadija ya gida , alhamdulillah, Khadija! Naam yaya , wacece wannan kawar taki,? Law yaya Yar gidan Baba Kabiru ce makotanmu abokin Baba sunanta Zainab, to Masha Allah, suna mai dadi.

To kuzo muje nan suka fito daga emergency suka tsallaka dayan bangaren Asibin Murtala suka mike kadan sai gasu a amenity, suka Shiva dakin da sallamarsu , nan Khadija da Zainab suka durkusa suka gaishe da Mallam Dauda, Baba ina kwana, lafia kalau yaran kirki , ya gida ? Alhamdulillah Zainab ya mutanen gidanku? Dukk sunanan kalau Baba, to Masha Allah.

Baba!!! naam Khadija, ina wayarka? Meza kiyi da ita? Babansu Zainab zamu kira mu fada masa an chanja maka daki tunda bai fita daga gida ba ya fadawa Mamansu Zainab saboda tace yaya Khalifa zai kawo abuncin rana anjima kaga kada yazo yayyta bulayi, to Khadija gashi. Nan aka bugawa Babansu Zainab waya aka fada masa ,ya shikenan shima zaizo saisu taho tare da Khalifa daganan ya wuce kasuwa.

Nan sukayi hira sosai tana bawa babanta labarin abun dariya , suna cikin hira saiga Dr Samari ta shigo , suka gaisa , tace, Masha Allah jiki ya fara warwarewa insha Allah gobe litinin in muka zo aka kwance gurin karayar da gurin dinkin da,akayi muka in muka duba muka ga babu wata matsala insha Allah zuwa juma,a zamu sallameka saikaje ka karasa jinyar a gida, to likita nagode Allah yayi albarka kinji , Dr ta amsa da amin ya Allah . to nizan tafi dama na shigo dubaka ne to yarnan ki gaida gida, Khadija da Zainab sai murna sukeyi za,a sallami Baba.

Wajan karfe biyu saiga Mallam Kabiru da Khalifa sunzo nanda hira ta sake barkewa wajan karfe uku Balarabe yace, oya kuzo Ku tafi gida lokacin islamiya ya kusa , Khadija!!! Naam yaya Balarabe, ungo kayannan ku tafi daku gida nasan bazaki iya wankesuba ki ajiye in mun dawo gida na wanke kinji.,, to yaya naji, yauwa Ku taho in rakaku , sukayi sallama dasu Mallam Kabiru ya dauki kudin mota ya basu .

Karfe hudu a gida tayi musu nan Khadija tace Zainab mazaki shirya ganinan zuwa bari in shiga gida in sako uniform kada nu makara kisan jiya mun makara, to Kiyi sauri,

Assalamu alaikum ,
Wa,alaiki assalam, ganta filfil sai yanzu aka dawo gaki mai uba ko nida kene, ummm, inna ana saran ranar juma,a za,a sallami Baba Rasss gaban Adama ya fadi nan tashiga tunani akan bata cimma burin datayi akan Khadija gashi Mallam zai dawo, hmmm naji tashi ki bani guri jikar layya mayya, sum sum Khadija ta Shiga daki ta saka sofaffin uniform din islamiyarta ta fito ta tafi gidansu Zainab, ananne ta chanja zuwa sababbin uniform dinta suka wuce islamiya itada Zainab.
bayan tafiyar Khadija Adama ta kiro dillalayi delu kawarta a waya ,

Adama, halo Delu

Delu, naam Adama ,ya gida?

Adama, gida babu lafia

Delu, to kibari gobe zanzo Unguwar taki sai mu tattauna kinji,

Adama, ,, shikenan sai anjima.

Yauwa nasan in Delu tazo zata kawo shawarar yadda zanyi da Khadija. Saini Adama uwar Aisha shalele naci dubu sai ceto Wii huhu ,...

Ina alfahari daku masoyan Rayuwar Khadija ina ganin sakonninku..

Comment dinku da votes dinku su suke dada min karsashi da karfin gwiwar rubutu, Ku cigaba dayi. Nagode Allah ya saka mu da alkhairi Allah yabar zumunci. Nice taku Farida ( jikar bello)

Comment
Vote
Share

Rayuwar khadijaWhere stories live. Discover now