*RAYUWAR KHADIJA*
Story and written by *Faridah*🌹
*jikarbello*@wattpad
Part 2
Isarsu asibitin murtala suka wuce bangaren emergency, a nanne likitoci suka karbeshi " aka fara bashi taimakon gaggawa saboda jinin dake ta zuba daga jikinsa, lokitoci ukune akansa, Dr Sadiq ,Dr Zayd dakuma Dr Samira. Sun dau tsahon awa uku akansa kafin su iya saida jinin, Dr Samira ce tafito tana tambayar " suwaye suka kawo wanda yayi hatsari yanzu? Mallam Rabi,u da Mallam Ali da inspector Ahmad suka amsa da mune muka kawoshi, Dr Samira tace to Ku biyoni ofishina! Bayan sunje ofishin nata ta nuna musu guri tace su zauna, a nanne tafara yi musu bayanin halin da Mallam Dauda yake ciki; a gaskiya mutuminnan ya samu karaya biyu a cinyarsa ta dama, sannan ya zubar da jini dayawa saboda ciwukan dayaji, ahalin yanzu, zamu Shiga dashi dakin tiyata zamuyi masa dinki sannan a dora karayar daya samu saboda haka yana bukatar jini kamar leda biyu haka. Innalillahi wa innah ilaihi raji,un, itace kalmar da Mallam Rabi,u da Mallam Ali suka furta, Mallam Ali ne yayi karfin halin yin magana, ranki ya dade muma bamu sanshi ba taimakonsa mukayi, mai motar data bugeshi ya gudu a nanne inspector Ahmad yace, to yanzu dole a nemo iyalansa , Mallam Ali yace saidai a duba wayarsa baza,a rasa ba, Dr Samira tace kuyi hanzarin yin haka Inba haka zaku iya rasashi. Inspector Ahmad ne ya duba wayarsa domin yaga dawa sukayi waya karshe, daya duba yaga last call dinshi shine Alhaji Sadi, aka buga wayar harta kusan katsewa daga dayan bangaren Alhaji Sadi ya daga waya, Assalamu Alaikum mallam dauda , Amin Wa,alaika Assalam, bashi bane , ni sunana inspector Ahmad dan sandan dake duty a bakin kofar famfo,,, mai wayarnan yayi hatsarine, a daidai kofar famfo yanzu haka muna asibitin murtala bangaren emergency, Subhanallahi!!! Ni makocinsa ne , bari nayiwa iyalin nasa magana sai mu taho tare dasu, toshi kenan sai kunzo ..... Bayan minti goma haka saiga Alhaji sadi a gidan mallam dauda.
Assalamu alaikum!
Assalamu alaikum!
Assalamu alaikum!
Amin wa,alaika assalam, waye? Nine Alhaji Sadi,; lale maraba , Adama ina wuni, lafia kalau
Alhaji ya gida da iyali ?, Alhamdulillah mungode Allah, masha Allah...
Adama abunda ya kawoni shine, yanzu aka kirani daga asibitin murtala cewar mallam dauda yayi hatsari a hanyarsa ta zuwa kasuwa shine nazo in fada miki,!; wayyo Allah ni Adama na Shiga uku na lalace mallam ya mutu wayyo Allah, Adama bace miki nayi ya mutu ba, to meya sameshi, yanzudai ba kuka zakiyi ba , tashi zakiyi mutafi muga halinda yake ciki sannan musan meye abunyi... To shikenan Alhaji bari in dauko gyalena, yauwa to maza ina jiranki a kofar gida bari in fito da motata , to shikenan.Bayan Adama ta fito ta Shiga mota suka kama hanyar asibitin murtala , daga dorayi babba minti 30 ne yakaisu asibitin murtala , bayan sunje emergency, Alhaji Sadi ya kira wayar Mallam Dauda, inspector Ahmad ya dau wayar yace, Alhaji kun isone? Alhaji Sadi, yace yallabai min iso , to shikenan bari inzo in shigo daku, haka kuwa akayi yaje har gate ya shigo dasu zuwa ofishin Dr Samira, bayan ya inspector Ahmad ya gabatar dasu amatsayin yan uwan Mallam Dauda sannan yayi musu sallama ya koma bakin aikinsa .
Dr Samira ta sake yi musu bayani abunda ke damun Mallam Dauda sannan ta gabatar da su Mallam Ali a matsayin wadanda suka taimaka masa, Adama da Alhaji sukayi musu godiya sannan su Mallam Ali suka tafi. Bayan tafiyarsu Mallam Ali ,Alhaji sadi ya kalli Dr Samira yace, to Dr muje a gwada jinina ko Allah zaisa yayi daidai da nasa sai a duba.
Tace shikenan babu Matsala muje lab sai a gwada' bayan sunje lab an gwada jinin Alhaji Sadi sakamako ya nuna jininsu baizo daya ba saboda jinin mallam Dauda O+ ne na Alhaji Sadi B+ ne, nida nake gefe saida nayi hawaye saboda samun irin jinin Mallam Dauda abune mai wahala akaso dari na jama,a baifi kaso daya keda irinsa jininsa saboda O+ yanada wahalar samu ba kamar sauran ba. Gashi anason jinin da gaggawa, cikin ikon akaje blood bank (dakin ajiyar jini) na asibitin a nanne akasamu jinin da,akeso , sannan akayi maza aka karbi jinin sai dakin tiyata.
Cikin ikon Allah akayi masa aiki da dorin karayar daya samu , bayan awa biyu da aka dauka sai gashi an fito da Mallam Dauda zuwa dakin Hutu, aka Dora masa ruwa a hannunsa na dama jini a hannunsa na hagu, yanzu abunda ya kamata shine Ku Dan fita domin ya samu ya huta domin ba,ason hayaniya daya akansa, insha Allah nanda awa biyar zai iya farfadowa. To shikenan likita mun gode Allah ya saka da alkhairin, Dr Samira ta amsa da Amin,,,,
Alhaji sadi yace, yanzu Adama ki koma gida ki kimtsa ki dawo ki debo muku wasu abuwan anfanin, to Alhaji an gode Allah ya dada girma da dauka, amin ya Allah, ai bakomai Mallam Dauda tamkar Dan uwana na daukeshi, fatanmu Allah ya bashi lafia. Amin
Adama ga wannan ki hau mota , to an gode Alhaji, Adama ni fitowa ta fara sababi tace, uhmmmm ni dama mutuwa yayi kowama ya huta danni wallahi bazanyi zaman jinyarsa ba , zuwa zanyi in turo yar'sa danni ba kalar wahala bace.Banyan Adama ta koma gida ta kwalawa Khadija kira,
khadija!Khadija!Khadija!
Kina ina inane shegiyar yarinya sai shengen kyau uwa jinsin aljanu wallahi ki kiyayeni, Khadija ta amsa da, inna gani, na Shiga uku ni Adama me Dan uwarki yaushe zaki daina kirana inna, na gaya miki sauda dama ki daina kirana inna amma bakya jin magana ko , to saiki shirya kije asibitin murtala bangaren emergency an kwantar da ubanki yayi hatsari, dajin haka khadija ta fashe da matsanancin kuka , dalla malama Niba kuka nace Kiyi min ba , tashi zakiyi ki kama hanya kije kiyi jinyarsa danni ba wahalalliya bace kinjiko.
Inna kudin mota, kudinme kikace? To ko sisina bazan baki ba inzaki tafi da kafa ki tafi inbazaki jeba ki zauna, Kinga kije dakinsa ki dibi kayansa ki tafi dashi, Khadija ta share hawayenta ta je ta dabi kaya kala uku ta koma ta dauki nata kala daya ta tafi , bayan ta fito daga gidane ta shiga gidansu Zainab ta tsuguna ta gaida Mama Asabe mahaifiyar Zainab ,Mama ina wuni , lafia kalau khadija ya gida? Lafia kalau mama, uhmmm dama dama , dama, dama me khadija fadi abunda kikeson fada ni mamanki kinji, mama dama kudi nakeso kibani babane yayi hatsari yana asibitin murtala bangaren emergency shine inna tace ni inje inyi jinyarsa wai ita bazata jeba , Mama Asabe ta saki salati tace, yanzu Adama bazata iya zuwa tayi jinyar mijinta ba saike zata tura, dudu khadija shekararki goma fa amma ta Dora miki wannan nauyin ,
Mallam ! Mallam ! Mallam! Fito ka tayani jin wannan zance , kai khadija kina ganin Rayuwa , amma ki cigaba da Hakuri domin mai Hakuri shike dafa dutse harya sha romonsa yayi gyasa, Mallam kabiru mahaifin Zainab ya fito daga daki yace, Asabe dukk naji abunda yarinyar nan tace , ai banga ta zama ba Mallam dauda mutumin arzikine dole inje inga ya jikin nasa.Vote
Comment
Share
YOU ARE READING
Rayuwar khadija
General Fictionkhadija marainiyace ta taso cikin kuncin rayuwa a hannun matar mahaifinta mai suna Adama Wanda tasha wahala sosai amma daga baya ta samu ingantacciyar rayuwar da bata samu ba abaya.