*RAYUWAR KHADIJA*
Story and written by *Faridah*🌹
*jikarbello*@wattpad
Part 6
Assalamu alaikum masoya Rayuwar Khadija inai muku fatan Alkhairi , Allah ya bamu albarkacin sannan rana ta Juma,a Yadda aka bude garin kano lafia inai mana addu,at samun lafia da kwanciyar hankali a jaharmu da kasa baki daya. Allah ya kawo mana karshen wannan annobar ta covid19, yan uwanmu na gida dana asibiti da basuda lafia Allah ya basu lafia mukuma masu lafia Allah ya karama lafia da nisan kwana masu albarka ,
Wadanda suka rash Kuma Allah ya jija su da rahama in tamu tazo Allah kasa my cika da kyau da imani saboda arzikikin Annabi Muhammad (S.A.W).Assalamu alaikum!
Assalamu alaikum!
Assalamu alaikum!Wa,alaikum salam, a,a Delu dillaliya tauraruwa mai wutsiya ganinki alkhairine awajena, shigo ta wajena bari in aika a siyo miki ruwa mai sanyi kisha ko kya samu nutsuwa.
Yauwa Adama dama abunda yasa nace kibari in zo gidanki shine, maganarmu bazata yuwu a waya ba , yanzu dai abu na farko shine , kinada kudi ahannunki yanzu? A akwai dubu goma awajena, yauwa Adama yanzu bamuga ta zama ba tashi zakiyi muje gurin boka mai gani har hanji dake kauyen dabaro, aikinsa kamar yankan wuka haka take.
Shiyasa nake sanki Delu akwai kawo shawara mai kyau, tashi muje kafin yarannan su dawo, ...
Su Adama na fitowa suka tari adaidaita suka kwatanta masa inda zai kaisu amma zai jira ya dawo dasu nan sukayi tsada dashi yace subashi dubu biyar tunda gurin yanada nisa sosai chan kasan kurnane , suka a,a dubu biyu zasu bashi yace a,a saidai su tari wani , aiba ayi hakaba dannan zamu baka dubu uku inyayi maka, shikenan Ku hau muje.
Daga dorayi babba tafiyar awa uku ce takaisu kauyen dabaro suka samu bakin wata bishiya sukace mai adaidaita ya jirasu achan suje su dawo..
Saida suka kara yin tafiyar minti ashirin akafa sannan suka tadda bukkar boka daujadu mai gani har hanji.Delu ce tafara Shiga da baya tana cewa kaci kutumar ubanka (saboda ba,ayi masa sallama saidai ashar itace sallamarsa) sannan suka fara yi masa kiransa kamar haka,
daujadu uban tsinannu kaga jikan barbushe da tsunburbura , boka daujadu na busa tsigarinsa yana dariya hahahhaahh , Delu Yar amana
Boka daujadu, dakata ba sai Kiyi min bayani ba nasan mai ke tafe daku .
Hahaha
Hahahaahhhhhhhhh
Haaahhhhhhhhhhhh, to maganar gaskiya saidai Ku chanja aiki domin mijinki da yarsa sunada ibada bazan iya ba innace zan yi wani abun dan lahantasu to mutuzanyi , mazaku tashi Kuban waje Dan ubanku kafi insa aljanu suyi fata fata daku,..
Adama da Delu har rige rigen fita ake . dagudu suka karaso bakin inda mai adaidaita yake sunata haki, nan suka hau adaidaita suka kama hanyar dawowa gida, suna tafe suna dada tattauna yadda zasu bullowa lamirin, yauwa kawata ga shawara, kawo kunnenki kiji, nan sukayi kus kus dunsu sai shewarsu kakeji.Delu kawata shiyasa nake kaunarki wallahi akwai ki da kaifin basira,
Basu suka koma gida ba sai kusan karfe 9 na dare. Lokacin har su Khadija sunyi barci. Adama ta shiga dakinta ta kwanta tanata tunanin yadda zatayi ahaka har bacci ya kwasheta,Asuba tagari
Asubah nayi khadija ta tashi tayi awala tayi sallah bayan ta idar tayi azkar da addu,o,in data sabayi, bayan ta gama tafara aikin gida kamar yadda ta saba da wuri ta gama dan tanaso ta saci hanya taje asibiti da wuri.
Bayan ta gama aikinta tsaf sannan ta shiga wanka ta shirya dama akwai ragowar kudin motarsu na jiya a gurinta dashi tahau adaidaita sahu yakaita asibiti .
Ta shiga dakin da babanta yake ta tsugana ta gaisheshi babana ina kwana , ya jikin naka? Lafia kalau Khadija, jiki Alhamdulillah ya naki sauki , to Allah ya kara lafia yakumsa kaffara ce, Amin ya Allah, sannan ta juya ta gaisheda Yaya Balarabe,
Assalamu alaikum
Amin wa,alaikum sallam,
Dr barkanku da isowa , Dr samira Dr Zayd da Dr Sadiq ne sai wasu student Dr guda uku ne suka shigo dakin.
Gaba dayansu suka gaishe da Mallam Dauda suka yi masa ya jiki, ya amsa da sauki to Allah ya kara sauki. Gaba data suka amsa Amin ya Allah .
Sannan DR's suka fara abunda ya kawosu , Dr Samira ce ta fara magana Baba kamar yadda nagaya naka ranar asabar dana so to yau litinin insha Allah zamu cire dinkin gurin sannan a duba gurin karayar, shikenan ya'ta bisimillah Allah ya bada sa,a.Nan Dr Zayd ya fara warware Pop din da,aka nada masa, tsaf ya warwareshi tunda Dr Zayd likitan kashine ya dudduba kafar Alhamdulillah kafa ta gyaru sannan ya cire dinkin da akayi masa nanma Alhamdulillah komai nomal , zokuga farin ciki gurin Khadija harda tsalle ta rungume Dr Samira yan Anty Samira ranar za,a sallami babana? Insha Allah Khadija Dr ta bata amsa , yaya Balarabe kaga ikon Allah ko wallahi insha Allah in girma inaso inzama likita saboda indinga taimakawa mutane kamar yadda Anty Samira takeyi, gaba daya suka amsa da Allah yasa, sannan Dr Samira tace Balarabe ya biyota office dinta zata rubuta musu maganin daza,a karbo a gurin magani. Sallama suka tafi.
Balarabe yabi bayan Dr Samira domin karbar takardar maganin dazai karbo , yana shiga office din ta gama gurin ka zauna, amm dan Allah Balarabe in babu damuwa inaso kabani labarin Khadija saboda wallahi Allah haka naji ina kaunarta sakani da allah, ajiyar zuciya ya sauke sannan ya fara bata labarin Khadija daga farko har karshe ., saida ta zubarda hawaye tausayinta , abu na biyu inaso ka bani lambar wayarka koda kun koma gida mu dinga gaisawa, babu damuwa ya karbo wayarta ya samata lambarsa sannan ya karbi takardar maganin ya fito, wata ajiyar zuciya naga Dr Samira ta sauke tana lumshe idanunta .
, azuciyata nace anya Dr Samira bada biyu ta karbi lambarnan ba kuwa, anma baruwana intayi tsami zamuji,.....Vote
Comment
Share
YOU ARE READING
Rayuwar khadija
General Fictionkhadija marainiyace ta taso cikin kuncin rayuwa a hannun matar mahaifinta mai suna Adama Wanda tasha wahala sosai amma daga baya ta samu ingantacciyar rayuwar da bata samu ba abaya.