01 Tausayi

772 33 1
                                    

👄👄👄👄👄👄👄👄
   *A HAKA NIKE SONTA*
👄👄👄👄👄👄👄👄

         _By Jameelah Jameey_
           *Yar mutun kankia* 👸🏻

                _AND_

         _AMMYN KHAIRAT_
           *GOLDEN GIRL*

🅿️01

"Sannu Umma Allah ya baki lafiya"..

"Amin Fatima, Allah yayi maki albarka ya baki miji na gari Fatima Allah ya kareman kai daga sharin zamani"..

"Amin Umma insha Allah Umma Allah zai tashi ƙaɗaɗinki Umma"..

"Fatima karki manta Allah baya ƙyale wani dan wani ya ji dadi, Allah da yabaki ni shi zai anshi abun shi nidai Fatima ko bayan raina ki riƙe mutuncinki ku kula dakanki kinga baki da kowa sai ni amman ba ni da zaɓi zaɓin Allah shine zamu bi naso naga lokacin aurenki amman haka Allah yaso"...

"Umma dan Allah kibar faɗin haka, insha Allah baki tafiya ki barni idan kika barni na bani ya zanyi da rayuwata Umma kema kin tafi kamar yanda Abba ya barmu gunwa zani Umma? "..

Ta karasa maganar tana kuka maicin rai dan tana tsoran Ummarn tata tarasu ta barta kamar yanda Abbanta yayi dan har yanzun ta kasa manta yanda taga gawar mahaifinta bata fatar rasa Umma cikin wannan lokacin da take bukatar abokin shawara..

"Tabbas Fatima ba gun kowa zan barki ba nabarma Allah ko kin manta Allah shi ke rayawa ya kuma anshi rain mamaci? "..

"Eh hakane Umma, "yauwa Fatima dan haka kisa a ranki Allah yana tare dake ki rabu da dagin mahaifinki harda dagina domin ba sonmu suke ba dan haka ki miƙa lamarinki ga Allah dan shi yake komai a hannunshi ba mutun ba"..

"Umma na shiga ukuna, Umma dan Allah ki tashi mu tafi asibiti dan ita cuta ba mutuwa bace"..

"Fatima ba asibitin da zani ko munje ba kudi ke garemu  da zamu biya ba kuma kinsan ba kyauta za'abamu maganin ba"..

"Eh Umma duk da haka nidai kiyi man wanan alfarma ki tashi mu tafi asibin nan na fita haƙinki dake kaina na iyaye, idan ban kai ki wannan asibitin ba ba zan taɓe yafema kaina ba Umma "..

"To Fatima Allah yayi maki albarka ya baki kema zuri'a wanda zata sharemaki hawaye kamar yanda kike yi man, "Amin Umma ni zan tafi na samo keke naped sai mu tafi asibitin"..

"To Fatima "..

Nan Fatima ta tafi cikin sauri dan hankalinta baki ɗaya ya fita a jikinta saboda jikin Umma ba ƙaramin tada mata hankali yayi ba, shiyasa bata san mai take ba dan ita kawai burinta ta ganta hospital..

"Bawan Allah dan ko zaka shigo cikin anguwarnan ka ɗauki marar lafiya ka taimakaman"...

"To shikenan ba damuwa mu wuce baiwar Allah "..

Nan Fatima tana gaba mai naped na bayanta har suka iso gidansu nan tashiga ta fito da Umma suka ɗauki hanyar Faderal medical center katsina state..

Bayan sun iso asibiti direct emergency nurse suka wuce da Umma dan jikin yayi tsanani sosai..

"INNALILLAHI WA'INNA'ALAIHIRAJIUN".

Kalma da Fatima take maimaitawa kenan dan bata san yanda zatayi ba shiyasa ta kama faɗin inalillahi, *{gareku yan uwa musulmai idan wani abu na masifa ya samai ka karki ihu ko kuka ka kira Allah dan Allah shine mabuwaye ga gara misali Allah shi zanyi maku maganin matsalarku ba ihu ba Allah yasa mudace Amin}*..

An ɗauki lokaci mai tsayi sanann taga nurse sun turo Umma bisa gadon mararsa lafiya za'a kaita ɗakin hutu sannan likita ya bukaci ganin Fatima a office ɗin shi...

"Come in, "doctor ina kwana?, "lafiya lau kece wanda ta kawo marar lafiya Salamatu Aminu? "..

"Eh nice doctor, Allah yasa ba wani abu ya samu Ummana ba doctor? Ya Allah "..

"Kwantar da hankalinki ba abunda ya samu Umma mudun kuka kawo kudin aiki zata samu sauki"..

"Subuhanalillahi, Allah hunma ajirni fi masibati wa'aklifni kharan minha"..

"Doctor wani kallar ciwo ne ke damun Ummana wanda har za'ayi mata aiki? "..

Kallonta kawai Doctor Mubarak yake domin yarinyar ba ƙaramin burgeshi tayi ba dan yaga natsuwa tare da ita ga hankali da tawaskali..

"Umma tana fama da Kidney Infection yayi was gaskiya dole sai munyi mata aiki sannan zamu samu abunda muke bukata"..

"To doctor nawa ne kudi aikin? "..

"Ina mahaifinki yake?, "Allah yayi mashi rasuwa doctor, kawai ba sai ka tsananta bincike ba gayaman kudin aiki naga yanda zanyi"..

"Allah ya jikinshi, "Amin nagode, "to kudin aiki dubu hamsin ne zaki kawo za'ayi aiki kawai, "doctor kudin magani fa? "..

"Ki fara kawo kudin aiki, kudin magani mai sauki ne dan akwai maganin da ake badawa kyauta wanda zaki saya ba masu yawa bane sosai "..

To shikenan ni zna tafi na kawo kudin Magani, "to shikenan idan kin samo kudin lafiya lau insha Allah zamuyi mata aiki"..

Nan Fatima ta tafi neman kudin aiki..




Nan fa ake yinta jama'a ina fatima zata samo kudin aiki wanann shine abun tambaya 😰

Masoyanmu ku biyo domin jin yanda wanan litafi mai albarka zai kasance *A HAKA NIKE SONTA*..


Masoyanmu kudai ku cigaba da biyomu mune naku

*#Yar'mutan kankia*
*#Golden Girl*

#share
#comment
#vote
#like
#please

A HAKA NIKE SONTAWhere stories live. Discover now