13&14

173 20 5
                                    

👄👄👄👄👄👄👄
*A HAKA NIKE SONTA*
👄👄👄👄👄👄👄

By jameealah jameey
*Yar mutan kankia*
____________________

              ADN
AMMYN KHAIRAT
*GOLDEN GIRL*
____________________

A'k'al'k'ashin k'ungiyar

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊️*
____________________

Had'in gwiwa da👇🏻
*PROFIENT WRITER'S ASSOCIATION*

🅿️1️⃣3️⃣&1️⃣4️⃣

Alhmdulh jikin Umma da sauki sosai, dan tana iya tashi da kanta tayi abunda ba zai gagareta ba.

"Umma ina kwana".?
"Lafiya lau Doctor, amman Doctor dan Allah ka sallame ni hakan dan jikina Alhmdulh yayi sauki sosai na gaji da wannan kwanciyar da nike ai sai ya saman mutunwar jiki".

"Umma dan Allah ki dan ƙara hakuri jikin ya ƙara sauki sosai sannan sai na sallamarku, so nike naga kin samu sauki sosai da sosai ".

"Ai Alhmdulh haka ma Doctor, kuma dawainiyar tayi yawa gwara mu koma gida hakan ma mun gode sosai".

"Umma dan Allah kiyi hakuri karki ce nayi maki musu,amman ba yanzun ba zan sallame ki sai kin ƙara hutawa tukun nan".

"To Doctor, Allah yayi maka albarka, "Amin Umma ina Fatima banganta ba".?

"Yanzun nan taje gida ta chanzo mana kaya itama naga alamun halinku ɗaya baku san nace sallama bayan kuma ni inaji a jikina Alhmdulh jiki yayi sauki sosai, amman sai ku wai na ƙara samun sauki".

"A dai yi hakuri Umma, insha Allah na kusa baki sallama, amman Umma dan Allah zan nemi alfarma guda ɗaya a wajenki".

"Wata alfarma ce haka? Inajinka Allah ya bani ikon yi".
"Amin ya Allah Umma, da man Umma inasan ki bani damar na nemi so wajen Fatima idan Allah yasa ina da rabo to idan kuma rabon wani ce lafiya lau nidai ɗankine Yanzun kuma in ban auri Fatima ba hakan ba zai sa mu daina zuminci ba dan nasan ba kaddarata ba idan Fatima kaddarata ce ko bakuzo asibiti ba sai na nemo ta na aureta itadai lokaci yayi".

"Shiru Umma tayi tana nazarin maganae Dr Mubarak dan magana ce yayi amman mai hankali da Tunani zai gane abunda yake nufi, dan Dr Mubarak yayi mata magana ta fahimta wanda yanzun mutane da dama basu gane hakan ba kamar samarin wanann zamanin, sun manta da shine yake kaddara abu sun mata da idan wanan matarka ce ko tana makkah sai Allah ya haɗaku da zaran lokacin da ya ibarmaku ya cika wallahi sai anɗaura koda ansa maki biki da wani sai a fasa hakan na nufin bashi bane zaɓin da Allah yayi maki shiyasa nike ba yan mata shawara ku nemi zaɓin Allah ba zaɓin ranku ba, kuma kusa a ranku komai yana da lokaci idan lokacin aurenku yayi ku ba'a shirya ba sai anyi shi haka idan bai yi komai kuka saya sai dai ki ajiyeshi underbed ku jira lokaci , Allah yasa mu dace Amin.

"Umma dan Allah kice wani abu ko naji hankalina ya kwanta Ummana".

"Haƙika Doctor Mubarak kanada hankali da sanin ya kamata, zanyi farinciki idan Allah yasa kaine mijin auren Fatima  nasan bazaka barta ta zubar da hawaye ba kuma bazatayi kukan maraici ba, dan haka na baka damar ka nemi so wajen Fatima Allah ya zaɓa maku Alkhari ".

"Nagode sosai Umma, Allah yasa na dace Umma ki tayi da addu'a domin addu'ar iyaye itace gaban komai ".

"Insha Allah zamu cigaba da yi maku ".

Bayan sun gama maganar Dr ya ba Umma magunguna sannan yayi mata allurai ya wuce office yana farin ciki.

_Niko nace su Dr Mubarak sai kace Umma cewa tayi ta bashi bayan izinin kawai tabashi na ya nemi so wajen Fatima ☺️🙈_


Dan Allah kuyi hakuri munsan bamu yi maku readmore, hakan ya farune sobada muna wasu typing ɗin ne a kowace rana kunga Golden Girl tana *ZARATA, MAI ARZIKI DA DR MAHISH MEERAH* kunga dole muyi mata uzuri ga ciwon ido duk tanayi.

Ni kuma Jameelah Jameey ina yin posting ɗin *GIMBIYA HAKIMA*  kuma kwana biyu bani lafiya har yanzun ban dawo dai-dai ba shiyasa Jiya bamu samu damar yi maku posting ba saboda baki ɗayanmu bamujin dadi fatan zaku anshi azurunmu☺️.

Sannan masu yiman magana basu samuna a wattapad kusa #JameelarhSadiq zakuga ganni ko kuma kuyi man magana ta wanann number 08160508316 zan baku wani link a wattapad ɗin zaku samu *A HAKA NIKE SONTA* cikin sauki muna godiya masoyanmu🥰.

Dan Allah kuringa yin share to others group ɗin da kuke, sannan *A HAKA NIKE SONTA FAN'S* bakuyin Comment sosai munsan masuyin Comment dan haka very soon  zamu fidda wanda basu comment dan haka take note🤷🏻‍♀️🙁.

#Yar'mutan kankia
#Golden Girl

#Share
#Comments
#Vote
#Like
#Please

A HAKA NIKE SONTAWhere stories live. Discover now