💝 *ZATOH*💝
*©HIKIMA WRITER'S ASSO.💜*
_(home of peace,joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)_💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜
_.UMMIEN2018._
💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜 💜💜
_.Alhmdlh,godiya ta tabbata ga allah madaukakin sarki sub hanahu wata alaa mai kowa mai komae daya bani dama cigaba da kawa maku wannan novels din,ina rokonsa daya bani damar kammalawa cikin amincinsa ameen._
Wattpad@UMMIEN2018.
*PAGE 058.*Rayuwa suke a garin da suke service nasu cike da farin ciki saidan abinda ba'a rasa ba...
sannan kuma husna data fada tarkon kaunar tahir wanda zuwa yanzu soyayyarsa tamata mugun kamu na bugawa a jarida,amma kuma taki ta bada damar dazay fahimci hakan...
sannan a gefe daya kuma ga soyayyar dashiga tsakanin zahra da sir saleem na ban mmk...
*asalin tahir da saleem*
sun kasance aboka naine na kut kut tun suna kanana,wanda sanadiyyar hakan har iyayensu suka zamana abokanan shawarar junansu...
wanda a halin yanxu mahaifin tahir shine governor na jihar yobe,sannan mahaifin saleem senator na zone c...
tahir su biyu hajiyarsu ta haifa shida kanwarsa mai suna rashida,wanda akoi taxarar shekaru kusan goma tsakaninsu wacce zasuyi sa'anni dasu husna...
sannan saleem maryama kanwarsa ce wanda suke uba daya,mahaifiyarta ta rasu sanadiyyar zuwarta duniya...
wanda haka yasaka mahaifinsu saleem yabi ya sangarta yarinyar sosai wai inji sa da fada tausayinta yakeyi...ummansu saleem itama saleem ne kawai danta wanda saleem da maryama suka kasance susu biyu ne a gidan mahaifinsu...
rashin kunyan da maryama ke tsugawa a gari a lokacin da take ganiyar kuruciyarta allah ne kadai yasani...
wanda har takai ta kawo takan sha syrup,sannan akoi wani saurayinta mai suna mahfooz wanda shine silar kara rugujewar tarbiyarta da umma ke kokarin wajen ganin ta daurata akai...shi yamaida ta cikakkiyar mace tun a titi wanda karfi da yaji yamaidata karuwarsa...
aikuwa labari yazoma babansu wanda hakan yayi sanadiyyar kamuwarsa da hawan jini,hakan ba karamin kiyayya bane yashiga tsakanin maryama da dan uwanta saleem...
inda ita kuma alokacin tayi dana sanin aykata kura kuranta ganin halin da mahaifinta yake ciki duk a sanadiyyarta...tayi masa alkawari insha allahu bazata kara aykata makamancin haka ba...amma kuma dan allah ya taimaka mata ya aura mata tahir abokin yayanta...
tahir yakasance miskili ne shima na bugawa a jarida a wannan lokacin dabazai wuce 25yrs ba,sannan yana dan taba sigari shima...amma ba sosai ba...
kwata kwata bayan son maryama,har takai lokacin da akazo masa da batun aurenta yace sam baisan zancen ba...wanda hakan yayi sanadiyyar da maryama ta kamu da ciwon zuciya mai tsanani...
a matsayinsa na likitan zuciya wanda kuma shine likitanta ya fuskanci yadda cutar ke barazana da rayuwarta dan haka yaji tausayinta kuma ya aminta da son da take masa ya tabbata a dalilin son da take masa zai iya maidata kalar matar da yake so...
saleem ma kuma ya sakko daga fushin dayakeyi da yar uwarsa shima ya roki abokinsa alfarmar ya taimakama kanwarsa kar ya rasata...anan ya shaida masa ya amince amma da sharadin duk lokacin dayaga wacce yake so kar aga laifinsa
inda ba'a dauki lokaci ba aka daura auren maryama suleiman da angonta tahir abdulrashid...
alokacin da taji labarin daurin auren ta da tahir ba karamin farin ciki tayi ba,aykuwa tafara samun sauki...harta warke garas abinta...amma kuma duk lokacin da take cikin bacin rai ciwonta kan tashi...wanda hakan ne yasaka suke taka tsantsan da lafiyarta...mahaifinsu ma ya warke
inda a shekrar farko da aurensu ta haifo zankadeden yaronta mai kama da ubansa aka saka masa sunan kakansa...
daganan kuma tahir yasaka maryama a islamiya,sannan kuma yasakata a catering school...wanda cikin shekara biyu ta kware a fannin girki,inda itama ya bude mata nata nakanta...
a fannin ilmin addini ma alhamdlh tana dashi daidai iyawarta...tasan yadda zata kula dashi wanda hakan yayi tasiri kwarai domin ko idan ba girkinta kona mahaifiyarsa ba sam baya cin abinci...ko tafiya zaiyyi shikam yakan iya rayuwa da snacks har yaje ya dawo...
tafiyarsa mai duguri duk aykin hajiyarsa ne inda turasa can wai kozai daina miskilancin daya saba...sbd dukda yana kokarin yin magana a duk lokacinn dayake tare da ummansa amma gani take sam ba haka bane...cewaa ma tayi lecturing ko teaching ne kan iya maida sa maganannen dole...
saleem ne yafara tafiya domin gano masu yadda yanayin makarantar yake kamin tahir yabi bayansa...inda acan ne mafarin haduwarsu da su husna...inda har sukayi ta samun takun saka tskaninsu...
bayan dawowarsu kuma saiga su husna a garinsu kuma har cikin asibiti...
a yanxu haka cikin maryam nada wata takwas da sati biyu ne...wanda ana saka rai ko yau zata iya haihuwa sbd akou matan dasuke haihuwa wata takwas...
vote
comment share
follow me on wattpad@ummien2018*Fatima Adam fateh*
*Taummy🥳**UMMIEN2018...✍🏿*
YOU ARE READING
ZATOH
Historical Fictionkunji wata tambaya masu karatu wai shin dama bakar mace ma kyakkyawa ce...? wasu kuma sukanyi ZATOHn cewa muddin yarinya tayi shigar zamani kou makamantansu wai yar iska ce sai mai saka hijab itace kamilar mace...shin hakane kou ba haka ba...?ku biy...