Chapter 7&8

74 5 0
                                    

🌀🌀🌀🌀
*IZAYYAH…!*    
🌀🌀🌀🌀
           NA
  *HAFSAT A GARKUWA*

_On_
'''Whattpad='''
*MUM SEEYAMA*
 
Gajeran Labari.
  
©🎆
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* ✍🏻
  _A• W• A•_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._
 
بسم الله الرحمن الرحيم...
'''AM BACK AGAIN'''🚴🏻‍♀️

*SADAUKARWA*

'''Wannam Page ɗin naki ne Mummyn Jiddah ina matuƙar Alfahari dake, ina jin daɗin Comment naki Over💞'''

*PAGE 7&8*
  
*……* Sai da suka ga ta suma sannam suka bar dukanta suka kuma gida kowa yana huci kamar Kumurci, gaba ɗaya ƴan unguwar sun tsorata ganin bata motsi kowa tsoro yake kar yaje mutuwa tayi a ɗaura masa sharri dan sunsan Matar ba mutunci ne da ita ba, tsaf zata ƙala wa mutun sharri, Dukan da ruwa ya mata ne yasa ta farfaɗo da kanta, a hankali ta fara janjiki har ta shiga gidan, mutane sun tausaya mata sosai ji suke kamar su ƙirata ta dawo gidansu da zama, dan Yarinyar tana basu tausayi matuƙa sun rasa wannam wacw Uwace a gareta da bata ƙaunarta dai dai da ƙittawan agogo, haka taja ta shigo parlou gaba ɗaya sun chanja kaya suna zaune suna ta shewa, Oum ne ta ganta nam ta miƙe a fusace tace "dan ubanki mai ya shigo dake? maza ki koma chan waje ke da ki shigo gidan nam har sai ruwan da kike gudu karya taɓa ki ya tsaya sannam ki shigomim gida, inko kika kuskura kika shifa ɗaya daga cikin gidan anguwarnam dan kisamu makafa dukan da muka miki yanzu lafulane akan wanda zamu miki nam gaba, Cikin kuka tace "Oum dan girman Allah kiyi haƙuri, ruwannam in ya ƙara dukana zai haifarmin da abubuwa da dama, "Zaki ɓace ki barmin nam ne ko sai naci ƙundun Ubanki ta faɗa da yarensu na Yarbanci, cikin masifa, Ai da sauri taja ta koma a bakin ƙofa ta rakuɓe, gaba ɗaya anguwar shiru kamar ba kowa, duk sun koma saboda sunga ta shiga gida, sun ɗauka shikenam shirin ya ƙare basu sam akwai wani ba, haka ta rakuɓe a wajen ruwa na dukanta, tana kuka har Baba yazo ya sameta a wajen, cikin tashin Hankali ya isa gareta ya kamata yace "Fa'eesha mai kike a tsaye a cikin ruwannam? Mai aka miki? Kuka ne ya kuɓuce mata, nam ta faɗa jikinsa ta saki kuka nam ta nisa tace ba komai Baba, dan tana tsoro kar ta faɗa masa Oum ta ƙara mata wani dukan, Hannunta ya kama suka shiga gidan ransa a ɓace…
  Suna shiga suka samu sun kunna waƙarsu ta Yarbawa amma kamar Cool Music ne sai tiƙar rawa suke tsabar a sara, Oum tana ganinsu tayi Kici kici ta haɗa rai, Baba cikin ɓacin rai yace , "Hajiya miye Fa'eesha ta miki da zafi haka kika mata irin wannam hukunci? Cikin sanyin Murya yake maganar abun ya bawa Fa'eesha mamaki sosai dan yadda ya taho ɗin nam bata zata zai mata da sanyi haka ba, duk da sun saba sai ya taho da zafinsa yana zuwa sai yayi sanyi a gabanta, Oum Murmushi tayi nam ta zaiyane masa komai babu abunda ta rage ko ta ƙara, nam Baba yace "Ke kuwa Fa'eesha mai yasa data saka ki aiki kika ƙiya, karki ƙara haka kinji, daga haka yau haura sama ɗakinsa, yana shiga ya saki wani irin Kuka na baƙin ciki, ya rasa mai yake damunsa in har yaje gaban Bara'atu sai yaji tayi masa kwarjini sosai, nam ya ɗauro Alwala ya fara nafila yana neman mafita, Fa'eesha kuwa ɗaki tazo shigewa jikinta duk yayi tsami sosai,  Oum ne ta daka mata wani tsawa take "Ke!!! Uban wa kika ajiye da zai ƙarasa miki wannam wankin, zaki juya kije ki cigabamin da wanki ne ko sai na ƙara miki lilis, cikin zubar da ƙwalla ta juya a tsorace tana ayyana rashin Imani na Oumahnta, su Aziza ko dariya suka sheƙa, haka taje tana kuka ga ruwa na dukanta ga ciwon da jikinta yake zuba mata, haka ta ƙarasa wankin, sai da takai ƙarfe 11 na dare duk da tasan ba wai sun fita bane amma sam baza ta iya ba wankin yafi ƙarfinta a Lokacin da ta shigo duk baaa Parloun gidan yayi tsit halamun duk sunyi bacci, jo takan Abinci bata biba duk da tana jin yunwa Amma gajiyar da tayi ya hanata sauraran Abincin, Toilet ta shiga ta haɗa ruwa mai matuƙar zafi ta gasa jikinta sannam ta fito kaya tasa masu matuƙar nauyi ta haɗiyi maganin Mura da zazzaɓi dan tuni zazzaɓi ya rufeta nam ta haye gado ta rufu da Blanket  amma duk da haka rawar ɗari take, haka bacci ɓarawo ya saceta…
*Washe gari…*
Haka ra tashi jikinta duk ciwo ga hannunta yadda yayi suntum saboda wankin da tashi sai dai zazzaɓin ba kamar da dare ba, ruwan zafi ta ƙara haɗawa tana kuka ga zafi ta ƙara gasa jikinta sannam tayi wanka tare da wankan tsarki ta fito, Sallah tayi tana kuka tana roƙon Allah da ya kawo mata agajin gaggawa, dan in ba haka ba watarana za a iya samun gawarta, wata zuciyar ce ta bata shawara akan ta gudu, wata zuciyar ko tace in kika gudu ma ina zaki je, kar kije ki gudu ki faɗa hannun da ba na gariba, gara ki zauna a wajen Oum in ma kashe ki za tayi gara ta kasheki akan ki shiga yawon duniya…
        Haka ta ta saƙe²  amma sam bata samu wata mafita ba, mafitar ɗaya ce shine ta gudu kawai, kuma ita ta ɗauka nam ta fara tunanin hanyar da za tabi ta kuɓuta, amma sam ta rasa ganin hakan bazai kaita bane ta tashi ta fara aikin gida kamar yadda ta saba, bayan ta gama ne ta shirya dan tuni su Aziza sun tafi, haka ta ƙarasa Makaranta cikin rashin kuzari dan sam batajin ƙarfin jikinta ko ina na jikinta ciwo suke mata ga yunwan da take azalzalarta, tana isa daga yananinta da Hamdiya ta gani tasan ba lafiya ba, bayan sun biya karatune suka dawo nam Hamdiya tace "Akwai wani abun dake damunki ko? Fa'eesha kamar jira take ta fashe da wani irin kuka, har mutanen dake kusansu suka fara tambayar ko lafiya, da sauri ta toshe bakinta tace lafiya ƙalau, tashi sukayi suka fita, nam Fa'eesha ta rungumi Hamdiya ta saki wani irin Kuka, Hamdiya ma rungumarta tayi ta saki kuka, sai da sukayi kuka mai isarsu sannam Fa'eesha tace "Wallahi Hamdiya guduwa zanyi, bazan zauna ina ji ina gani ayi ajalina ba gara na shiga duniya wallahi…
    "Duniya kuma?" Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" Haba Fa'eesha kina ƴar musulmai kike wannam furucin? dan Allah karma ki fara kar kuma ki ƙara wannam maganar na roƙeki, to wai ma mai aka miki haka da zafi har kike furta irin wannam maganar? duk da nasan kina shan wahala a gidan ku kuma nasan kina haƙuri, Amma mai aka miki daya ƙureki har haka?  Cikin kuka Fa'eesha ta faɗa masa duk abun da ya faru tun daga farko har ƙarshe, Kuka suka gaba ɗaya musamman Hamdiya, data ga abu yayi yawa sosai ga tausayin ƙawarta da take yi, cikin sanyi tace "Fa'eesha anya Oumah ita ce tayi naƙudarki ta haifeki kuwa, na ƙara miki tambayarnam a karo na barkatai, Wallahi ni dai Oumah ina ga ba ita ta haifeki ba, inko ita ce to wallahi ta sanadinki baza ta shiga Aljanna ba wallahi, Fa'eesha take wallahi Hamdiya yunwa nake ji ga zazzaɓi jiri nake ji, da sauri ta kamata tace sannu Muje gidan mu, nam suka kama hanya a hanyar suka samu Napep duk da kusa suke da makaranta amma saboda yanayin abunda Fa'eesha take ji suka hau, tafiya kaɗan suka yi suka isa, Nam Hamdiya ta biyasa suka shiga gidan da Sallama…
      Mom dake Parlou ne ta amsa musu tana kallonsu cike da ayar tambaya, Zaunar da Fa'eesha Hamdiya tayi sannam ta nufi Kitchen haɗu mata Abinci tayi da Fresh milk ta kawo mata shinkafa jalof wanda ya ƙayatu da kayan lambu harda kaza, ta ajiyemata, aiko hannu baka hannu ƙwarya ta fara cikin Abincin, Hamdiya hawaye ne kawai ke zuba mata, haka Mom ma duk da bata san yanzun mai yake faruwa ba, kafin kace me ta cinye Abincin cikin filet sannam ta shanye Milk ɗin duka babban gora wani gyatsa tayi sannam tace Alhamdulillah, Hamdiya ne ta miƙa mata ruwa da magani ta ƙarɓa tasha, nam ta tadata ta kai ta ɗakinta ta kwantar da ita tare da rufeta da Blanket ta fito, Mom ne ya kalleta cikin ayar tambaya hallau, Nam Hamdiya ta zauna ta zaiyanewa Mom komao tace "Wallahi Mom na tsani Oumah nam a rayuwata na tsaneta tsana mai muni, Mom ma hawaye ta goge tace "Haƙiƙa Fa'eesha tana cikin halin da duk wani mai imani zai tausaya mata, Mom tace da zan samu dama zan karɓeta ta zauna a wajena, amma sam hakan bazai yiwu ba, duk da haka a kullum za kina kai mata abinci tunda ba bari take ta fito ba in kp hakan bai yiba sai kina kai mata Islamiya kp kan ta tafi tazo taci, Hamdiya taji daɗin hakan sosai rungumar Mom tayi tana mata godiya, har ƙarfe ɗaya Fa'eesha takai tana bacci hankalita kwance, Hamdiya ganin Lokacin tashi a makaranta ya wuce ne da Sauri ta miƙe dan ƙarfe 12 ake tashinsu gasu yanzu ƙarfe 1 tana zuwa ta tasheta a hankali a zabure ta miƙe tana cewa Oum dan Allah kiyi haƙuri zanyi aikim yanzu… Ganin Hamdiya ne yasa tayi shiru, Hamdiya Tausayinta ne ya ƙara ɗarsuwa a zuciyarta kenam ma har mafarkin ƙuntata mata da Oum take take yi, Fa'eesha tace "Haƙiƙa bani da bakin godiya a gareki amma tabbas kin ceto ni daga ciwon yunwa, tabbas yau naci Abincin da ban taɓa cin kamarsa ba Nagode! Nagode!!! sosai Ƙawata, ta ƙarasa tana goge ƙwalla, Hamdiya tace haba Ƙawata ai ba godiya a tsakanin mu kasan cewar mun zama ɗaya, yanzu ko tashi ki wanke bakin ki saboda har ƙarfe ɗaya, ai cikin matuƙar tsoro tace na shiga Uku yau Oum kasheni ne kawai baza tayi ba, ta faɗa tana mai shiga toilet wanke bakinta tayi ta fito Parlou ta samu an shirya mata Abinci, gai da Mom tayi saboda ɗazu bata samu damar gaida ta ba, godiya ta mata sosai, Mom tace bata son godiya saboda ta ɗauketa tamkat Diya ɗinta, Mom ne ta nuna mata Abinci tace maza kici ki tafi, da Sauri Fa'eesha tace Mom tsoro nake ji saboda su Aziza sun rigan komawa gida bari na tafi kawai,da Sauri Mom tace kwantar da hankalinki kici Abincin tukunma sa ki tafi kinji, ba musu ta zauna taci dan yunwa take ji tuwon Amala ne da miyar karkashi da ganda, sosai taci sannam tasha ruwa, gudu gudu ta fita tana godiya, cikin Tausayamata su Mom suka kasance da tunanin abun da zata tarar a gidan su…

   '''Uhum!!! yau kam bazan iya cewa komai ba ku zaki faɗa min da bakinku'''🤒

_Sharhin ku shi zaisa na gane yadda abun ya muku, daɗi ko akasin haka._🤧🤧

*NEXT PAGE IS LOADING…✍🏻*

#Vote
#Share
#Comment

08132761212

*_HAFSAT A GARKUWA CE_*🤙🏻

IZAYYAH...!Where stories live. Discover now