🌀🌀🌀🌀
*IZAYYAH…!*
🌀🌀🌀🌀
NA
*HAFSAT A GARKUWA*_On_
'''Whattpad='''
*MUM SEEYAMA*
Gajeran Labari.
©🎆
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* ✍🏻
_A• W• A•_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._
بسم الله الرحمن الرحيم...
'''AM BACK AGAIN'''🚴🏻♀️*SADAUKARWA*
_All My Pan's ina muku so domin Allah_
*PAGE 17&18*
*……* Da sauri yayi kan Fa'eesha dake kwance ko motsi ba tayi, ruwan ya yayyafa mata nam taja dogon Numfashi, ta fara buɗe idanunta a hankali wanda yake cike da tsantsar tsoro da Hawaye ta sauƙesa akan Hayatuddeen da yake ta mata fifita da rigarsa, duk yabi ya kiɗimi gani ta far faɗo ne ya sakar mata ƙayataccen Murmushinya, bata san Lokacin da ta mai da masa ba ita ma, Oum da tayi wani kasaƙe tana kallonsu, nam ta ɗibo wani Ashar ta runtuma ta ƙara da cewa "To munafuka kin farfaɗo daga sumar Munafurci, Fa'eesha a firgice ta miƙe nam ta tsugunna a gaban Oum tace "Oum dan girman Allah ki faɗan gaskiya, ke kika haifeni? "Jar uba amma wannam yarinya kin raina min wayo ni kike faɗawa haka? to ban sani ba sai ki shaƙeni na faɗa miki, Murmushin takaici Fa'eesha tayi tace "Tabbas Oum bake kika haifeni ba, inko kece to ba makawa farraƙu aka mana a tsakanin mu… "Babu wani farraƙu da aka muku, Oum ba ita ta haifeki ba Fa'eesha kiyi bincike da kyau, dan Mahaifiya duk abunda ke tsakanin ku baza ta taɓa miki haka, cewar Hayatuddeen, Oum katsaƙe tayi tana kallonsu, gani tayi tamkar asirinta ya tonu tabbas dole tayi wani abu, cikim tsawa tace "Kai! Hayatu kana son Azizar ko baka sonta, dan na faɗa maka baza ka taɓa samun Fa'eesha ba don ina tsoron maka ka shafi cutar dake tare da ita, ta ƙarasa tana hararan Fa'eesha da tuni waye suka gama wanke mata idanu, Hayatuddeen ɗan murmushi yayi sannam yace "Oum Fa'eesha na fara so kuma ita zan ci gaba da so har ranar da zata shigo gidana, Aziza ko Allah zai bata miji ba sai ni ba, dan duk cutar da take tare da Fa'eesha to tabbas ina sonta a haka kuma zan zauna da ita, Fa'eesha tafi gida gobe insha Allah ƴan uwana zasu zo nema min Aurenki, daga haka ya faɗa mota yaja yabar wajen Fa'eesha gida ta shige tabar Oum kamar an dasa ta a wajen, Wani ashar ta ƙunduma tabi bayan Fa'eesha.
*Washe gari*
Da misalin ƙarfe takwas na dare, aka aiko akam ana Sallama da Fa'eesha nam Oum ta saɓi hijabinta ta fita, aiko tana fita taga shine, tace kai malam bari na maka kankat bata nam kuma Mahaifinta bai barya ta fara kula samari ba kaga sai anjiman ka, nam ta barsa tsaye yayi saƙaƙo kamat gunki haka yaja ya tafi, ko da ta shiga gida ta ƙira Fa'eesha bayan ta zauna tace "Yanzu ke Fa'eesha wannam kike so ki aura? to bari kiji irin wannam masu kuɗin in suka Auri mace badan komai suke aurenta ba sai dai suyi kuɗi da ita saboda duk yawanci irin waɗan nam masu kuɗin ƴan mafiya ne, dan haka ni shawaran da zan baki shine ki fita sabgarsa inko kina so ki mutu kuma shikenam, Tashi ɗaya tsoro ya ɗarsu a zuciyar Fa'eesha ta ƙudira a ranta ko yazo baza ta fitoba, Washe gari kamar Kullum sai ga yaro ana ƙiranta, Baba dake falo yace Fa'eesha maza tashi kije kiga wake ƙiranki, ba musu na miƙe cikin tsoro dana tuna da maganar Oum bayan Mun gaisa ne dashi da Abokinsa, nam suja ɗan gai gaisa, Fa'eesha tace "dan Allah Hayatuddeen kayi haƙuri ban tashi Aure ba ka nemi wata, cike da mamaki yace Fa'eesha mai ya faru kuma? "Babu komai ni dai don Allah kayi haƙuri daga haka ta shige gida, Shiko Abokinsa yayi ta bashi baki akan ya haƙuri kawai tun da ta faɗi haka, nam suka tafi yana ta saƙe saƙe kala daban daban.
*Bayan wata Uku*
Fa'eesha har yanzu rayuwata cikin ƙunci take sam bata sakewa bata walwala, kwatsam tana zauna da yamma, aka turo ana ƙiranta, Oum bata yi yinƙurin hana taba, dan a lokacin Aziza ta samu Miji mai matuƙar arziƙi, Fa'eesha tana fita tayi ido huɗu da Hayatuddeen, Ya ƙara kyau fiye da yanzu cikin mamaki ta ƙarasa dan ta jima da manta dashi, gaida shi tayi cike da mamaki, Murmushi yayi yace "nasan za kiyi mamakin gani na, amma ni kam bazan yi mamaki ba dan tun da muka rabu na san shige da ficen ki duk abun da kike tamkar a idona kike yi, da sonki nake kwana dashi nake tashi, yanzu ma nazo da ƙoƙon barana akan Aurenki in har kin shirya kuma zaki ban daba.
Murmushi tayi tace Insha Allah, nam suka ɗan taɓa hira ya bata tsaraba da ƙyar ta karɓa ta masa godiya ya tafi da zummar gobe iyayensa zasu iso, tana shiga ta miƙawa Oum tace Hayatu ne ya dawo shine ya bani wannam , Oum gabanta ne yayi mummunar faɗuwa amma ta dake nam ta fara buɗr kayan su Leshi ne atamfa turare mai da dai sauransu, nam Oum ta ƙira Aziza tace maza tazo ta kai ɗakinta tana amfani dashi, Fa'eesha ko ajikinta dan sam bata buƙatarsu, ta tashi tayi ɗaki hankalinta kwance…
Aiko washi gari sai ga dangin Hayatuddeen nam suka samu Baba ana masa kwatancen Hayatu ya ganesa,bayi wata wata ba ya basu saboda Hayatu babu wanda bai san saba Mutumin kirki ne sosai, nam aka tsaida ranar Aure Wata Uku dai dai dana Aziza kenam, Fa'eesha taji daɗin hakan dan ko ba komao zata bar gida inda ake ƙuntata mata Oum da taji hauka ne kawai bata yi ba saboda Asirinta ya kusa tonuwa matuƙar Fa'eesha ta fara soyayya, Fa'eesha da Hayatuddeen soyayya suka fara mai matuƙar tsafta da nishaɗi babu hayaniya a tsakaninsu, a kullum Oum gabanta faɗi yake saboda yadda taga tsakaninsu, nam ita da Hajiya Kubrah suka ƙulla tura maaa ƴar Hajiya kubrah saboda ya Aureta ya rabu da Fa'eesha amma sam yace musu baya buƙatarta, yau ma kamar Kullum hira suke cikin Aminci, nam Fa'eesha taji wani irin faɗuwar gaba, nam ta fara tuna…
Abun da ta manta shekara da shekaru, riƙe kanta tayi da yake barazanar ɓallewa, da sauri ta tsugunna, Hayatuddeen cikin tsoro yace "Ya dai Fa'eesha mai ya same ki mai kike ji? Cikin kuka tace "Tabbas Oum ba ita ta haifeni ba a yanzu na tuna komai da ya faru, Allah na gode maka, tabbas Allah ba azzakumin bawansa bane sai dai bawa ya zalunci kansa, Haƙiƙa Uwa baza ta taɓa yiwa ɗiyarta irin Abunda Oum take min ba, Allah sarki Umma na da Kaka ta masu matuƙar son Farinciki ne raboda da ganinku har na Manta Wayyo! Allah na, Allah na gode maka.
"Fa'eesha wai meke faruwa ne kin sani a duhu fa? nam tayi Murmushi tace kai kam ka tayani murna tare da godewa Allah, a yau abun sa na manta shekara da shekaru yau a kuma nam wajen na tuna komai hakan ya sake tabbatarmin kai bango ne a gareni, nam ta zaiyane masa komai yayi kuka kamar ransa zai fita ya kuma tausaya mata, ya zama kamar ƙaramin Yaro, domin duk wanda yaji Labarin Fa'eesha duk dauriyarsa sai ya zubar mata da ƙwalla babu abun da yafi masa ciwo irin Abincin da ake xuba mata a leda, a Lokacin ya ƙudira a ransa tabbas sai ya share maya hawaye sai ya saka ta farincikin da ba ta taɓa riskar sa ba, nam Fa'eesha ta katse masa tunani ta hanyar cewa "Dan Allah ka bani aron wayarka na ƙira Kakata naji Muryarsu, da sauri ya miƙa mata, nam ta saka No ɗim ta danna ƙira, Kaka dake kishin giɗe cike da tunanin a wani haɗi jikarta take taji wayarta na ƙara, Umma dake ɗaki ta fito taje, Mama ɗaga wayar man kiji waye "Ke ni bazan iya ba ke ki ɗaga kiji, da sauri Umma ta ɗaga dan jin zuciyarta tayi tana tsanata bugawa, Fa'eesha tana ji a ɗaga cikin sauri tace "Kaka!! ai Umma da sauri ta ƙara riƙe wayar da kyau tace "Fa'eesha!! kece? sai kuma ta fashe da kuka, Fa'eesha ma kuka ta fashe da ita...'''Wayyo!!! Yasin Fa'eesha kin bani Tausayi lalle Hayatuddeen shine bangon ki a rayuwa.'''😿😿😿😿😿😿😿
_Yasin yau a zuba min sharyin da zai girgizani, My pan's ina muku son so fisabillah._🤗
*NEXT PAGE IS LOADING…✍🏻*
#Vote
#Share
#Comment08132761212
*_HAFSAT A GARKUWA CE_*🤙🏻
YOU ARE READING
IZAYYAH...!
Kısa HikayeLabari ne mai cike da tsantsar Munafurci, da Azaba mai tsuma zuciya, mai cike da Ilimantarwa tare da faɗakarwa da kuma Nishaɗo