Chapter 13&14

67 7 0
                                    

🌀🌀🌀🌀
*IZAYYAH…!*    
🌀🌀🌀🌀
           NA
  *HAFSAT A GARKUWA*

_On_
'''Whattpad='''
*MUM SEEYAMA*
 
Gajeran Labari.
  
©🎆
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* ✍🏻
  _A• W• A•_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._
 
بسم الله الرحمن الرحيم...
'''AM BACK AGAIN'''🚴🏻‍♀️

*SADAUKARWA*

_My Dear Aunty Nice ƙaunarki daban yake a wajena, haƙiƙa ina Alfahari dake a ko ina, Allah ya baki Miji na gari wanda zai faranta miki iya rai iya mutuwa,ina miki Son so Fisabilillah_🥰🌹

*PAGE 13&14*

*……* A haka suka rabu akam in ta sami hanya zata zo gidan su ta kwana ta wuce, tun da Hamdiya ta tafi Fa'eesha take saƙe-saƙen hanyar da zata bi ta gudu amma ta gaza samu, sai ta fito da niyar ta gudu sai ta gansu zaune a falo,haka har dare ya tsala har wajen ƙarfe 12 sannam ta fito cikin sanɗa… Tun da Hamdiya ta tafi, tana zuwa ta sanarwa Mom ɗinta, nam Mom ta mata faɗa sosai akam mai yasa zata bata irin wannam shawaran sam bataji daɗin haka ba, ta ƙudira akan in har Fa'eesha tazo dole ta hana ta guduwa dan hakan sam ba mafita bace… Fa'eesha ko da ta fito bata samu kowa a Falo ba cikon san ɗa ta fito tsakar gidan sai rakuɓe rakuɓe take, Baba dake tsaye a sama yana waya ya ganki Fa'eesha sai leƙe-leƙe take alaman son fita take a gidan, ga jaka a hannunta, cikin tsoro da firgicin abunda takr ƙoƙarin aikatawa yace "Fa'eesha!! da Sauri ta ɗaga kanta ta hangi Baba, gabanta ne yayi mummanar faɗuwa dan bata so ta haɗu da wanda zai dakatar da ita ba, kafin ta gama zancen Zuci Baba ya sauƙo hannunta ya kama suka shi, a ɗakinta ya zaunar da ita, cikin Sanyin Murya yace "Mai kike shirin aikatawa haka Fa'eesha ba dai guduwa kike so kiyi ki barni ba? Fa'eesha karki yi haka, karma ki fara wannam ba shine Mafita ba Fa'eesha nasan kin wahaltuwa a gidan nam, amma ban san mai yasa ba bani da bakin iya Magana akan haka, dan haka karma ki fara Saboda bakisan Hannun da zaki faɗa ba, dan haka ina Umurtanki ko da wasa karki ƙara ƙoƙarin barin gidan nam, inko kika yi haka zan tsine miki Albarka, Cikin kuka ta rungumi Babanta tana girgiza kai Alamun baza ta ƙara ba shima hawayen yake yi, nam ya fara bubbuga bayanta Alamun rarrashi… cikin kuka Fa'eesha tace "Baba Oum bata sona bata ƙaunata na rasa dalilin haka, gaba ɗaya bana samun farinciki a wannam gidan in ba a wajenka ba, ban san mai yake a ƙulle ba wanda na kasa Kuncesa, Baba in har kasan wani abu dan Allah ka sanar dani, domin na farka daga dogon mafarkin dana tafi ta kece da wani irin kuka mai taɓa zuciyar mai sauraro, Baba share hawayensa yayi sannam yace "Fa'eesha ni kai na ban san meke faruwa ba, jina nake wani iri nafi shekara da zuwa gidan mu sai Jiya, sun min faɗa sosai akan bana ziyartar su ko dan iyayena basa raye ne, da ƙyar na shawo kansu, dan na manta Komai na baya da Addu'a da komai na tunasu, dan haka muci gaba da Addu'a tabbas akwai wani babban ƙulli wanda mu muka kasa tunasa, Sosai ya kwantar mata da hankali har tayi bacci sannam ya rufe mata ƙofa ya tafi cike da tausayinta…
*Washe gari*
Ta tashi wasai da ita dan Nasihar da Baba ya mata ya shiga zuciyarta kuma tayi alƙawarin baza ta ƙara yinƙurim barin gida ba, nam tayi aikin da ta saba na kullum, sannam ta shirya ta tafi Islamiyya dan yau gaba ɗaya ƴan gidan basu tashi ba, Saboda Lokacin tashin bai yiwa, ita ma yau ta tashi da wuri ne, gidan su Hamdiya ta shiga aiki taci sa'a bata tafi ba, nam suka Gaisa da Mom, Mom ne take mata faɗa akan ƙudirinta na jiya, Fa'eesha ta sanaraa Mom duk abun da ya faru a jiya, ta kuma yi alƙawarin baza ta kuma ba, Mom taji daɗim haka sosai, nam aka zuba mata abinci ta karya, Hamdiya tace "Ai jiya gaba ɗaya kasa bacci mukayi muna jiranki, amma da muka ji shiru sai muka kwanra muka bar ƙofa a buɗe ko da kinzo ki samu a buɗe Amma shiru, Ashe shirin ya rushe, dariya suka saka duka har Mom, haka suka kammala suka kama Hanya…  
       Haka rayuwa taci gaba da tafiya Sakanni na wuce wa zuwa Mintina, Mintina na wucewa zuwa Awanni, Awanni na wucewa zuwa kwanaki, Kwanaki na wuce wa zuwa satikai, Sati kai na wucewa zuwa Watanni, Watanni na wucewa zuwa shekaru' haka rayuwa tayi ta tafiya har yanzu jiya iyau, duk wani Ƙunci da Fa'eesha take sha ya dame na da ya shanye akan na yanzu, sosai ta kuɗe ta jeme, tayi baƙi ta chanja sosai, duk da ansan Mace da aiki amma ita aikin ya mata yawa sosai azaba ko ba'a magana, Yau ne bikin ƙawarsu Karima ta islamiyya da ƙyar Oum ta barta aka taje ta dan bata taɓa zuwa bikin ƙawa ba sai wannam, dan san Oum bata barinta wai kar taje ta samu Miji Azizanta bata samu ba, Mom Hamdiya ne ta musu anko, Karima tana anguwar Agege, yau ne ake buɗan kan ta waje ya cika maƙil, su Fa'eesha sunyi kyau sosai, tun da suka je wani Abokin ango ki kallon Fa'eesha gaba ɗaya ta kasa sakewa, hakan yasa tace da Hamdiya su tafi gida duk da ba'a jima da fara buɗan kan ba, ba musu Hamdiya sukk fara tafiya dan duk ɗaukarta Oum ta bata lokaci ne, suna cikin tafiya suka ki sallama a bayansu, da sauri suka waiga dan sun tsorata, aiko tana juyowa suka haɗa ido da mutumin da yasa ta bar wajen, Hamdiya ne tace Malam lafiya? Murmushi yayi wanda ya baiyanar da kyan fuskarsa sannam yace "Ni dai sunana  Hayatudden ina ɗaya daga cikin manyan Abokan ango, tun daga Lokacin da na fara ganin ƙawarki naji na kamu da sonta, kuma so ba na wasa ba na Aure matuƙar ta Amince, dan haka ina roƙonki Ƙawarmu kice ta tsaya ta saurareni dan nasan danni zata bar wajen nam saboda na dameta da kallo, Dariya Hamdiya tayi sannam tace "Yo wai dama saboda kai tace mu tafi gida? kai ya ɗaga mata Alamar eh, Nam tace "Yasin da nasan akan haka kika ce mu tafi bazan tafi ba, ta faɗa tana zun gure mata goshi, cikin sauri Hayatuddeen yace "Gaskiya ƙawarmu ina jin kunyarki ya zaki zunguremin abar sona, yasi karki ƙara gaba ɗaya dariya suka saka har Fa'eesha dan ya bata dariya sosai, hakan yasa suka koma gefe wajen wasu kujera guda biyu, zama suka yi Hamdiya kuma ta koma wajen biki, dan dama ba'a son ranta zasu tafi ba…
Cikin Nutsuwa ya shawo kanta Lokaci ɗaya Fa'eesha taji ya kwanta mata, dan suk samarin da Oum take kora basu taɓa zanam miti biyar ba balle taji tana son su sai wannam, duk yadda yaso ta masa kwatancen gidan su taƙi dan tana matuƙar tsoron Oum dan tasan in har yaje kashe tane kawai baza tayi ba, babu yadda ya iya amma zai tambaya Ƙawarta ƙila ita ta faɗa mata, nam ya miƙe yace bari ya ƙira mata Ƙawarta, da to ta amsa masa, yana zuwa ya ƙirata nam suka dawo gefe ya faɗa mata abun da yaƙe buƙata ba musu ta kwatanta masa, No ɗinta ya karba dan Fa'eesha tace ita sam bata taɓa riƙe waya ba yacika da mamaki amma ya dake dan ya ɗauka ƙarya ta masa kawai, duk da baiga haka a idonta ba, ya raka su har suka hau Sahu ya biya suka tafi cikin Farinciki a gidan su Hamdiya suka sauƙa, aiko suna shiga sai ga ƙiran Hayatudden, Hamdiya taba gani ta miƙawa Fa'eesha ba musu ta karɓa, nam ya mata ban gajiya sannam suka ɗan taɓa hira da zummar anjima zai zo,nam ta daburce akan kar yazo yau ya bari sai gobe, babu yadda ya iya dan haka dole ya haƙura, suba gama wayar tace "Mai yasa kika faɗa masa gidan mu Hamdiya? bayan kin san duk abunda ke faruwa, "Hmm Ƙawata kenam kina nufin haka zaki zauba ba aure? kar ki manta kefa bace ce, dan haka dole ki kula Samari kuma har kiyi Aure, sai dai duk mai Oum zata miki ta miki wallahi, Hawaye ne ya gangaro a idanun Fa'eesha cikin kuka tace "Ƙawata ban san mai Oum take so dani ba amma  wallahi ina son Aure, "Insha Allah zakiyi Aure ɗiyata, kuma wannam insha Allah shine mijinki duk da ban san shiga, cewar Mom tana fitowa daga Kitchen ɗauke da Abinci a gaban su ta ajiye tace maza kuci abinci ku share wannam zancen, godiya Fa'eesha ta mata nam suka ci abincin ta tafi gida cikin farinciki, dan yau ɗaya ta tsinci kanta cikin Nishaɗi…

      Bayan ta shiga bata ga wani ɓacin rai a wajen Oum ba hakan yasa tayi kwanciyarta, Washe gari tun da Safe take zullumin zuwan Hayatudden, da Misalin ƙarfe 5 wani yaro yazo akan ana Sallama da Fa'eesha, Babu kowa a falon hakan yasa Fa'eesha sauri fita, Hayatudden yana tsaye cikin shiga na mutunci wanda duk wanda ya gansa yasan mutumin kirki ne kum nera tayi kuka a jikinsa, tsayayyen Mutun ne mai cikat zati da haifa, da sallama ta ƙarasa kanta na ƙasa, cikin Murmushi ya amsa mata, yace "Kinga anacin ki yazo ko? Murmushi tayi tace "Aiko dai kam,nam suka ɗan fara hira amma duk rabin hidan Hayatudden ne keta zubasa kasancewarsa Mutun mai barkonci itako Fa'eesha da kai kawai take amsa masa, suna tsaye ne sai ga fitowar Oum daga maƙota…

'''Yau ake yinta kenam, zamuga ya zata kaya a wanga waje''' ga Oum ga kuma Fa'eesha ga ɗan anacinta Hayatudden😹😹😹😹😹😹😹

*NEXT PAGE IS LOADING…✍🏻*

#Vote
#Share
#Comment

08132761212

*_HAFSAT A GARKUWA CE_*🤙🏻

IZAYYAH...!Where stories live. Discover now