12

946 29 0
                                    

*_
A kwana a tashi ba wuya a wajen Allah, domin shi 'din mubuwayi ne gagara misali, sakamon(result) jarabawar dasu Fa'izah sukai ta jamb ta fito, Masha Allahu za'a ce domin kowannen su ya samu cutoff mark din da jami'ar bayero take so, Sai dai kash 'kasarmu ta gurb'ata da yanayin wa ka sani waya sanka? Komai sai kanada connection, abunda yasa nace haka kuwa shine daga Aliya har Fa'izah sun fito da score din da ake buk'ata. Amma yanayi na corruption yasa aka hanasu courses din da suke zab'a suyi, dakyar da sanayya aka baiwa Fa'izah gurbin karatun Mbbs wato medicine, Aliya kuwa ba'a bata Law ba dakyar aka musanya mata da karantar 'bangaren Faculty of education, department of LIS wato library science..

Tuni Baba Sulaiman ya sassayo musu komai da zasu buk'ata na makaranta, da sun so su zauna a hostel saboda yanayin nisa, Baba Sulaiman ya hana yace off campus zasu yi. Fa'izah a Buk old site zata dinga lectures har lokacin da gurbin karatun su zai koma asibitin makarantar na koyarwa wato 'Aminu kano teaching hospital'. Aliya kuma a new site zata dinga lectures, Masha Allahu za'a ce, domin kowacce daga cikin su shiri take na yadda zata fara karatu ba wasa, musanman Fa'izah da 'bangaren ta yafi wahala. Tuni suka fara zuwa lectures, bayan Baba Sulaiman ya biya musu kudad'en makaranta ya kuma basu handouts, JJC/Freshman year(shine sunan da ake kiran 'yan level one dashi) domin duk inda kagansu zaka gane su..

Zuwa lectures 'din farko kowaccen su tayi 'kawaye kamar yadda al'adar makaranta take, 'bangaren Aliya tayi 'kawaye har uku wato Nawal Mukhtar, Nour Hadee, da Zarah Usman, komai tare sukeyi, domin ko subsidiary courses tare suka 'dau electives, na 'bangaren International relations, da sociology. To hakama 'Bangaren Fa'izah dake old site sashen Mbbs, sun 'dau subsidiary's na; Dentistry and Dental Surgery, da Human Nutrition and Dietetics. Itada sabbin 'kawayen ta su Raheenah Sani, Amina Modu da Salaamah Khamis, sai Husnah 'kanwar Sahal, Wadda sai a ranar farko suka ga juna itada Fa'izah, Daganan kuma zumunci ya 'dore...

Yau kam tunda Aliya ta tashi take jin b'acin rai da kunci a cikin zuciyarta, addu'a kawai take yi dan samun sassauci amman ta gagara jin dad'in ranta, ko yaya kayi mata magana sai ranta ya b'aci ta hau masifa, a haka tayi shirin tafiya school sai faman ciccin d'aci take yi. Fa'iza kuwa tunda taga yanayinta tasan ba kalau ba dan haka ko uffan bata ce mata bare tayi abinda zai sanya su yin hayaniya.

Tsab suka shirya sukaje gurin Baba Suleiman ya basu kud'in da zasu hau napep suka yiwa Umma da gwaggo sallama suka fita. Suna zuwa bakin titi suna jiran mai keke napep yazo suka ji dirar mota a gaban su, d'auke kai suka yi gabaki d'aya tamkar had'in baki musamman Aliya da take cikin b'acin rai, suka ga mai motar ya zuge glass tare da yi musu magana,

"Yan mata muje na sauke ku mana."

Fa'iza ce tayi magana domin Aliya ma harta matsa can gefe da alama yaufa kowa ta shafeshi a wannan dacin ran da take yi,

"Lahhh mun gode ka barshi kawai."

"A'ah hakan bai dace daku ba, 'yan mata daku tsayuwar titi ba naku bane, kuma ai baku kuka roka ba nine nayi niya."

D'auke kai Fa'iza tayi tana kallon Aliya wacce ke k'ok'arin tsayar da mai keke napep, a hankali Fa'iza ta kalli mai motar tare da cewa,

"Ka dai yi hakuri, mun gode da k'ok'arin kare mana mutunci da kayi Allah ya baka lada."

Tana kaiwa nan tayi gaba zata tafi mutumin yayi saurin kiranta, kamar ba zata koma ba sai dai taje tare da tsayawa nesa da motar tana jiran abinda zai ce, yana gyara hular kansa yace,

"Dan Allah waccan sister d'inki ce?"

Fa'iza tayi shiru can kuma tace,

"Eh uwa d'aya uba d'aya."

"Ohh masha Allah toh ya za'ai na samu contact d'inta please?"

Kallansa Fa'iza tayi tare da d'aga idanuwa sama ta kuma kallansa, babban mutum ne dan a shekaru zai yi arba'in da biyar, kai da ka ganshi kasan cewar kud'i na wulakantuwa a gurinsa, wani k'atan tunbi da Fa'iza ta hango a jikinsa shine ya bata damar cewa,

KAI MIN HALACCI..! ||PAID NOVEL✅ (COMPLETED)Where stories live. Discover now