*Haka* rayuwa taci gaba da gara musu ta kowanne b'angaren, kowa da abinda yake cikin zuciyarsa da kuma abinda yake buri. Wani hutu dasu Aliya suka yi ne Baba Suleiman ya kwashe su suka tafi garin malam wato dangin gwaggo Talatuwa, sunyi murna da farin cikin zuwa kauyen, Dan an nuna musu soyayya tak'in karawa, ga samari da suka dinga sha'awar son kasancewa da 'yan matan wato Fa'iza da Aliya amman babu wanda yake iya yi musu magana saboda class d'in ba d'aya bane, kusan satinsu uku sannan Baba Suleiman yaje ya d'akko su ya maida su Hotoro, kwanaki biyu da dawowarsu ya d'auki Aliya da Fa'iza ya kai su Bunkure wato dangin mahaifin Aliya, nan ma an karbe su hannu biyu-biyu duk da cewar sunyi fad'a ganin yadda jikar tasu ta girma amman babu aure.Inna Adama ce dake zaune kusa da mai gidan ta wato kakan Aliya ma'ana mahaifin da ya haifi babanta tana bud'e masa langar tuwo da miya, sai da ta tura masa komai a gabansa ya faraci sannan ita ta samu guri ta zauna, kallon Aliya tayi wadda ke zaune tana cin gyad'a marau, Fa'iza kuma na cikin rumfa tana sallar isha'i, muryar inna Adama ta katsewa Aliya cin gyad'ar da take yi ta hanyar cewa,
"Wai ke Aliya zaman me kuke yine keda Fa'iza haka baku yi aure ba? Dan Allah ki duba yadda kukai rid'a-rid'a (manya-manya) daku amman ace ko maganar aurenku ba'a yi har yanzu, dubi su d'ahare dasu Altine duk kin girmesu amman ko wanne da yara uku ke kin zauna ko uban me kuke yi ban sani ba."
Toshe baki Fa'iza tayi wadda yin sallamarta kenan daga sallah dariya ta taho mata jin yadda inna Adama take cewa uban me suke jira. Aliya kuwa hannu tasa ta rik'o hab'arta tare da kurawa inna Adama ido, sam taji ta kasa cewa komai saboda yadda taga inna Adama ta had'e rai ita a dole ga wadda take cikin b'acin rai,
"Wai ba kyajin ina yi miki magana ne, ko kin zama bebiya ne?"
"Toh inna Adama fisabillahi me zance dake? Tunda kikaga har yanzu bamu yi aure ba ai Allah ne beyi ba, shifa aure bawai kiransa ake yi ba no! Shi yake zuwa kuma ko kanaso ko baka so sai kayi shi, toh ki taya mu da addu'a kawai bafa samarin ne bamu dasu ba, akwai su wallahi kawai dai sai mun gama karatu sannan zamu fito dasu."
"Ikon Allah, karatun banza karatun wofi, kaji min yarinya mu karatun bokon da bamu yi ba meya rage mu gamu a raya muna ci muna sha?"
"Hahahaha unbelievable..!"
Cewar Aliya tana wata muguwar dariya, jin abinda tace ne yasa inna Adama kallanta tare da cewa,
"Kardai ki zageni da yaran arna ya hudawa dan naji kin fara yi min."
"Tab! toh inna kinga rashin ilimin boko yaja miki na fadi abu kin juya shi da cewar zagi ne, ya kamata ki daure koni na dinga koya miki dake da malam."
Allah ya kiyaye mana, kuma kema yanzu nayi nadamar maidake can dan nasan ba zasu aurar dake da wuri, kuma yanzu ma ba zan bari ki koma ba sai da auran ki, anan kinfi yin samari masu sonki dan har yanzu d'an Bala mai markade be dena tambayar kina ina ba."
Tsikaro baki tayi jin abinda inna Adama ke cewa, tasan tsab zasu iya!aurar da ita a gobema ba sai an wani ja lokaci ba, karasowar Fa'iza kusa da ita ne yasa ta cewa,
"Sis dan Allah bani da samari a can gidan?"
"Kina dasu mana bama d'aya ba ba biyu ba."
Cewar Fa'iza tana murmushi, cikin tab'e baki inna Adama tace musu,
"Oho kwaji dashi, mudai ba zaku raina mana wayyo ba, Allah ya kaimu safiyar gobe da rai da lafiya wallahi zanje nace da d'an Bala ya fito ayi."
Tamkar Aliya ta d'ora hannu aka haka take ji sai faman turo baki takeyi, malam dai bece komai ba tuwonsa kawai yake ci harma baya son asako shi, dan yasan ko kashe Aliya za'a yi yanzu ace sai tayi aure za'a dawo mata da rai toh ta gwammace a barta ta mutu,
YOU ARE READING
KAI MIN HALACCI..! ||PAID NOVEL✅ (COMPLETED)
RomansaLabarin cakwakiya dake tafe da tacacciyar kauna marar gauraye ta zukata hudu; SHAMSUDDEN DA ALIYA ga kuma SAHAL DA FA'IZAH... 💕Kowanne yana son masoyin dan uwan sa. Wai cakwakiya🤭shin ya ruguntsumin zai karkare???