Dai-dai lokacin Shamsudden ya fito zai wuce, Sanye yake cikin manyan kaya samfarin 'dinkin kufta , yasha zanna bukar hula, Wadda tai dai-dai da kalar kayan jikin sa wato kalar sararin samaniya da turawa ke kira 'sky blue'. Sam khadija bata gane shi ba, domin duk 'daukar ta wani baturen ne abokin shamsu, Ummah dake amsa gaisuwar Khadija, Ganin Shamsudden zai wuce bai gane Khadijan ba yasa ta saurin dakatar dashi ta hanyar cewa,"Auta.."
Ganin matashiyar budurwar dake tsugunne a 'kasa kamar mai neman gafara, duk azaton sa y'ar aiki ce, ko yarinyar makota dake taya Umman aiki, domin tayi kala dasu aganin sa, cikin fad'ada murmushin fuskar sa yace,
"First Love!.."
Ummah ta 'kakaro murmushin yak'e had'e da yi masa dak'uwa alamar ga fa Khadija, Da alama gogan naku kuwa bai gano ba, domin cike da jin dadin ummah ta samo mai tayata aiki yace,
"Laa ummah y'ar tayin aiki kika yi?! Masha Allah!.."
Ummah tai shiru domin ji tayi inama 'kasa ta tsage ta fada kawai saboda kunyar da Shamsudden ya tsinduma ta aciki, Khadija kuwa tun sanda Umman ta cewa Shamsudden Auta! Ji da ganin ta suka gushe na yan wasu dakikai, Domin ta gano lallai Shamsudden gaja a baya, Shamsudden mai rake mai siyar da hatsi da riga y'ar shara shine wannan had'adden gayen a gabanta? Lalle da tayiwa kanta wasarai-rai lokacin da akace an had'ata dashi tak'i. Shamsudden ganin Umma batai magana ba yasanya shi wucewa can kusa da famfon dake tsakar gidah yana wanke goron daya karba awajen Abban su. Muryar Khadija ce ta doki dodon kunnen sa, inda take cewa,
"Ya Shamsu! Ina kwana?!"
Sai daya gama wanke goron tsab kafin ya juya yana dubanta, zai yi magana Ummah ta riga shi ta hanyar cewa,
"Auta ga Khadija, Dijama dai y'ar wajen.."
Cikin sauri ya tare Ummah yana cewa,
"Oh okay..! Sannun ki Dijama"
Yana gama fad'a yai wucewar sa parlor , gwiwoyin Khadija sai suka sage ganin irin amsa gaisuwar ta da Shamsudden yayi a wulakance, Ummah ta lura da yanayin ta, don haka tace,
"Ah'ah sannu! Harda wahala haka? Maza kai masa parlor, Angode Allah yasaka da alkhairi, dama yanzu nake shirin 'dora musu Indomie yau bamu tashi da wuri ba, Kai parlorn bari na 'dakko plates a kitchen."
Cewar Ummah kafin ta karasa shiga cikin kitchen dinsu dake tsakar gdian, Khadija kuma ta shiga parlorn jikin ta duk a sanyaye don batasan irin rashin kirkin da Shamsudden zai kara mata ba, Ai kuwa bakin ta dauke da sallama ta shiga ciki, ya amsa a dakile yana cigaba da danna wayar sa,
"Yaya na ina kwana? An tashi lapia?"
Kallo d'aya Shamsudden yai mata ya dauke kansa yana cigaba da danna wayar sa, ganin irin mayan kallon da take binsa dashi kamar mayya, ya sashi kara had'e ransa, ya tsani mata suyita kallon sa kamar wani abun ci. Cikin mayatar kallon sa da take tana ayyano rayuwar su idan sunyi aure (kuji karfin hali). Ta jiyo zazzakar muryar shamsu na cewa,
"Lapia kuwa?"
Ya fad'a hade da dankara mata harara, cikin inda-inda tace,
"Da..Dama ca nai ko na zuba maka abincin?"
Dai dai lokacin Ummah ta shiga parlorn dauke da flask na shayi da kayan tea, gaban Shamsudden ta dire tana ko'karin had'a masa shayin, Had'a masa kakkauran shayi tayi ta bashi, ya karb'a yana kurba a hankali, Ido hudu sukai da Khadija dake binsa da kallo hadda had'iyar yawu, tab'e baki yayi ya ci gaba da shan tea dinsa, Umma ta shiga bude basket din da Khadija ta kawo, funkaso ne da miyar taushe data sha nama da tantakwashi, sai wata madediciyar kula, dauke take da soyayyen dankalin hausa da 'kwai sai y'ar miyar kayan ciki a wata roba daban. Umman sai yaba abincin take yi, ta shiga lodawa Shamsudden a plate, kallo kawai yake bin ta dashi, mika masa tayi, ya ware idanu yana bin abincin da kallo, kafin cike da shagwab'a yace,
YOU ARE READING
KAI MIN HALACCI..! ||PAID NOVEL✅ (COMPLETED)
RomanceLabarin cakwakiya dake tafe da tacacciyar kauna marar gauraye ta zukata hudu; SHAMSUDDEN DA ALIYA ga kuma SAHAL DA FA'IZAH... 💕Kowanne yana son masoyin dan uwan sa. Wai cakwakiya🤭shin ya ruguntsumin zai karkare???