Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin kai
Na rubuta wannan littafin shekara ɗaya da rabi kenan , zan sabumta shi ne yanzu da yardar Allah. Fatan za ku ba ni haɗin kai wajen sharhi da vote.
Na sadaukar da wannan littafin ga ƙanwata Maryam Mrs Ahmad official Marcy
Jinjinar ban girman ga Marubutan KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
Jinjiga gare ku ƙawayena na amana 6 stars, Allah Ya ƙara haɗa kawunanmu.
"Samira tun ɗazu nake yi maki magana amma a banza! Wai me kike jira da ba za ki tashi ki je gidan aiki ba, kin san dai aikin nan naki da shi muke ci muke sha, don Allah tashi ki kimtsa ki tafi kar ki janyo mana abin da zai sanya a koro ki"Cewar wata dattijuwar matar da take zaune saman tabarmar kaba yayinda hankalinta ya karkata ga wata ƴar matashiyar buduwa mai kimanin shekara goma sha biyar da da haihuwa da take kwance ta yi filo da kafafuwanta.
Wacce aka kira da Samira ta zumɓura baki haɗe da yamutsa fuska sannan ta ce
"Wallahi Inna ni sam na gaji da aiki wancan gidan, ni gidan aiki ma zan sauya saboda kullum Alhajin gidan ba shi da aiki sai kallona, ni kuma ina tsoron wanan masifaffiyar matar tasa mai masifar tsiya, kin san dai halinta inna! Kuma har ga Allah tsoronta nake ji innata"
Ta ida maganar a raunane kamar za ta fashewa da kuka.Tun da ta fara magana inna take kallonta a nutse tare da jinjina maganganuta wanda take yawan faɗa mata su kwanan nan na kallonta da Alhaji Habibu yake yi in ta je gidansa, ba yau ne rana ta farko ba da ta fara ce mata mai gidanta yana yawan kallonta ba, amma kuma ba ta yi wani abu a kai ba, don duk a zatonta ƙarya ne take yi ko kuma ta gaji da aikin gidan ne? Sai kuma ta fi gazagata maganar yau da take shirin yi mata kuka! Amma maza da abun mamaki suke, wanda yake da Hafsat wato uwar dakin Samira, me zai wani kalla ga Samira bayan kwaillaci, wacce duka ba ta jima da fara al'ada ba, ba kuma wani kyau ne da ita balle ta ce shi ya gani yake kalla, ko kuma wani girma na azo a gani ba ta da shi balle a kirata da cikakkiyar budurwa. Dole ne ma ta san abun yi gaskiya tun abu bai yi nisa ba lokaci ya zo ya ƙure mata a ɓata mata yarinya, saboda a shaidun ɗan yau duk da dai Alhaji Habibu mutumin kirki ne amma dai ɓacin rana ake tsoro. Allah sarki in ba don matsin rayuwa ba kuma da rashin lafiyarta ba ta yaya ma za ta sakin kamar samira yarinya ƙarama tana aikatau a gidajen masu kudi?
A nitse inna Suwaiba ta kalli Samira sannan ta ce
"Ki yi hakuri ɗiyata wlh da ina da yadda zan yi da na yi kin bar zuwa aikin nan, sai dai babu yadda na iya ki ci gaba da haƙuri, da kamun kai, kuma in har kin tafi gidan ki daina yarda hanya tana haɗa ku da shi balle har ya kalle ki, iya gaisuwa kawai ce tsakaninki da shi babu ruwanki da shiga sabgarsa, da izinin Allah wata rana sai labari kin ji ɗiyata ƴar albarka""Shikenan innata na yi hakuri ɗin kuma zan yi yadda kika ce"
Cewar Samira ta ida maganar tana tashi tsaye haɗe da wucewa ma'adar bokiti, sai ta ɗauko shi ta wuce wajen pampo ta zuba ruwa ta yi wanka sharp-sharp. Bayan ta fito daga wanka ne ta kalli inna tana yi mata murmushi da ta gani ta yi zungum tana tana tunanin rayuwa. Sai
inna ta bi ta da kallo tana cewa
"Allah Ya yi maki albarka autata"Murmushi ta yi tana amsawa da amin sannan ta wuce ɗakinsu ta yi shirinta daidai na ƴaƴan talakawa, sai ta ɗauko kwanon abincin da take tafiya da shi gidan aikin, ta yi wa inna sallama tana cewa
"Inna na tafi sai na dawo"Inna suwaiba ta ce "Allah ya kiyaye hanya Samirata ki gaishe min da su, a dawo lafiya"
Samira ta amsa da "Amin" tana yin gaba.
Tafe take saman hanya a nutse tana kallon yara yan makaranta da suke wucewa saboda lokacin ƙarfe takwas na safe ba ta yi ba, tana sha'awar makaranta sosai sai dai babun halin haka, saboda tun bayan rasuwar mahaifinta sai kulawarta ta koma ga mahaifiyarta shiyasa ta bar zuwa makaranta saboda ita take zuwa wajen aikatau dayake inna ba ta da isashen lafiya, shiyasa ta bar zuwa makaranta saboda da aikatau ɗin ne suke ci suke sha kuma ba su da sana'ar fari balle baƙi. Amma dai Allah Ya yi ta mai kokari saboda tana 5e( js2 kenan) ta bar zuwa makaranta dukda tana son makaranta amma sai haƙuri ta yi da zuwan saboda mahaifiyarta. Tana tafiya tana tunani har ta kai gidan aikinta wato gidan Alhaji Habib dan canji da uwar gidansa hajiya Hafsat.
Tana zuwa gidan babu kowa sai mai gadi da yake ƙofar gida zaune, ita kuma kaitsaye buɗe babban falon gidan ta yi dayake tana da makulin gidan. Ba ta tsaya ɓata lokaci ba ta fara aikinta kamar yadda ta saba a kodayaushe, tana aiki tana famar mitar halin matar gidan na kazanta in dai a kan gyaran gida ne ba ta da shi sai dai gyaran jiki kawai, wanda ba shi ne kaɗai tsaftar mace ba, a fili ta furta
"Mace har mace amma ba ta san ta gyara gidanta ba sai dai kullum yar aiki ta yi mata komai, ni wallhi matar nan ta fara isa ta sai son jikin tsiya ga masifa, kuma har ma aikin gidan ya fara isa ta wallahi, Allah Ya nuna min dai na samu wani gidan aikin na huta da wannan gidan, ina dalili na gaji da aikin nan!"Haka ta ci gaba da mitarta can kuma da ta ga an ɓata kujeru da wani abu kamar ruwan madara sai ta fara gyarawa sannan ta ƙara cewa
"Kuma yanzu tana iya zuwa ta yi mani jarabar cewa ban gyara daidai ba kamar ni na ɓata ɗin , Allah dai ya raba ni da gidan nan lafiya sai na yi sadaka a ranar"
Nan dan nan ta share palour ta goge ta feshe shi da turare mai daɗin kamshi, sai gidan ya fito tsaf gwanin kyau ba kamar lokacin da ta iske gidan ba ga shi nan sai a hankali kamar gidan cin abinci, amma yanzu ko da ta gyara sai ya fito sak gidan mutane. Tana gama gyaran falon ta gyara ɗakin Hafsat wanda har da shi cikin aikinta don ko shi Hafsat ba ta iya gyara sai an gyara mata, can ma lokacin da mahaifiyar Samira tana yi masu aiki ita take gyaran gidan har da ɗakin Alhaji Habibu take gyarawa amma ko da ta bari sai Alhaji Habibu ya ce ba shi da buƙatar gyaran ɗakin Samira don ba zai yiyu ba budurwa tana shigar masa ɗaki ba shi ne dalilin da ya sa take gyaran ɗakin Hafsat kawai ko shi ma don babu yadda zai yi ne da ya hana hakan.
Bayan ta gama da ɗakin Hafsat ta gyaran ɗakin yaran gidan sannan ta ɗora abincin rana shinkafa da miyar yakuwa ta yi masu dayake ta kware wajen iya girki, yarinya ce karama amma girki ta iya sa sosai sai dai abin da ba ta taɓa gani ba shi ne kawai zai ba ta wahalar girkawa. Ba ta wani jima ba tana aikin ba ta gama saboda ba ta fatan matar gidan ta dawo daga aiki ba ta gama girki ba saboda ƙarfe sha biyu da minti sha biyar suke tashi, kuma ga ta da yara za ta ce sun kwaso yinwa amma ba a gama masu abinci ba, shiyasa duk yadda za ta yi kafin sha biyu sai ta gama girki sai dai in an samu ɓacin rana. Dayake saman gaz ne nan da nan ta gama, tana gamawa ta kwashe abincin ta jera shi saman dinning ta wanke tukunan da ta yi amfani da su ta ajiye su sannan ta rufe masu falon ta yi gaba da kwanon abincinta da ta zubo nasu. Ba ta tsaya komai ba ta tafi saboda ba ta so matar gidan ta iske ta don ta san kaɗan daga aikinta ne ta sanya ta wani aikin, saboda sanin halin uwar ɗakinta, Allah Ya yi ta mai son jikin tsiya kamar mage, ita kuma tana sauri ta je gida ta ga innarta ba za ta wani tsayawa ba yin abin da bai cikin aikin da aka ɗauke ta don yi shi ba, tunda dai ta yi mai wiyar can su karata ita da son jikinta ita ta yi gida.
Samira ba ta wani jima da fita ba mota ta yi horn mai gadi ya wangale masu ƙofar gida, ana gama parking wata mata ta fito daga motar tare da wasu yara kanana su biyu mace da namij. Matar nan ta haɗu ba karya black beauty ce, tana sanye da riga da zane na atanfa ƴar cote d'Ivoire kore mai ratsin ruwan madara, mayafinta ma ruwan madara ne da jaka da takalmi su ma duka ruwan madara. Matar ba ta cikin munanan mata haka kuma ba za a kira ta da masu kyau ba, kyawunta daidai gwargwado ne dayake ta iya ɗaukar wanka ne shiyasa kullum in za ka gan ta za ka ganta tsaf-tsaf da ita kamar wacce za ta je gasar kyau in ta yi shiri saboda tana da kirar halitta ta ɗan Adam wacce kowacce mace take son ta samu, ta fito ras da ita kamar a sace a ruga da gudu. Ba kowa ba ce wannan matar face Hajiya Hafsat uwar gidan Alhaji Habib uwar dakin Samira ƴar gidan inna Suwaiba.Don't forget to :
Vote
Comment
ShareReal Nana Aicha
VOUS LISEZ
Ƴar aikin gidana(Sabon Salo)
ActionSamira ƴar aikin Hafsat ce wacce ta auri mijin Hafsat ba boko ba Malam. ku shigo daga ciki domin jin yadda za ta kasance.