Page 2

56 4 0
                                    

Na sadaukar da wannan littafin ga ƙanwata Maryam Mrs Ahmad official Marcy

Zaune suke cikin falonsu bayan sun gama cin abinci rana Alhaji Habib da matarshi Hajiya Hafsat tare da ƴaƴansu Iman da Muslim suna hira cike da nishadi dayake Habib in ya dawo daga kasuwa cin abincin rana yana ɗan jimawa bai koma kasuwa ba sai bayan sallar la'asar yake komawa sai ya yi baccin rana wani lokacin ma.

"Papa don Allah tunda yau babu islamiya ka kai mu gidan Hajiya ni da Muslim in za ka koma kasuwa, kenan in ka dawo da dare sai ka biyo ka dauko mu ka ji Papa ?"
Cewar babbar ƴarsu Iman mai shekara bakwai na haihuwa, tana aji biyu a makaranta wacce ta yi maganar cikin shagwaɓa tana kallon babansu jin abin da zai ce mata don ta san da wiya ne ya amince masu da tafiyar.
Ai kuwa sai Habib ya ce da ita
"Ki yi haƙuri Iman har weekend sai mu tafi tare da mamanku, tinda ba ta zuwa aikin ranar, tun da safe in sha Allahu sai in kai ku gabaɗaya in zan tafi kasuwa."

Ba don ran Iman ya so ba ta amince haɗe da cewa
"To Papa Allah ya kai mu."
Habib ya amsa da
"Amin." Haɗe da cewa
"Yauwa my Iman, Allah Ya yi maki albarka ƴar albarka."
Hafsat da take kallonsu cike da so da ƙaunar zuri'arta ta amsa
"Amin Ruhina." Ta ida maganar cikin murmushin da yake tafiya da imanin Habib. Daga nan suka cigaba da ɗan taɓa hirarsu sannan ya wuce ɗakinsa ya kwanta bacci sai bayan sallar la'asar ya tashi nan da nan ya shirya ya yi masu sallama haɗe da tafiya wajen sana'arshi suka yi mashi fatan alƙairi haɗe Allah Ya kiyaye hanya.

💝💝💝💝💝💝💝💝

"Inna na tafi sai na dawo." In ji samira lokacin da ta gama shirinta na tafiya wajen aikatau gidan Alhaji Habib, tana sanye da riga da zane na atanfa ta ɗora hijib ɗinta, ta yi kyau abunta kamar ba ƴar aiki ba saboda babu wanda zai kalle ta ya raina mata wayo ko kuma ya ce shigarta ba ta yi kyau ba dukda atanfar ba mai tsada ba ce irin ta talakawa ce irinsu sai dai babu kazanta ko ɗaya a jikinta saboda Allah Ya yi ta mai tsafta.

Inna suwaiba ta kalleta cike da so da ƙaunar ƴarta sannan ta ce da ita "To ɗiyar Albarka sai kin dawo, don Allah ki hanzarta ba ni so kina yin dare ko kaɗan wallahi, Allah Ya kiyaye hanya kuma Ya tsare min ke ƴar albarka."

Samira ta yi murmushi lokacin da inna ta ce ba ta son tana yin dare, ita kuma ba don komai ba take ƙin tafiya da wuri ba sai don maigidan, ba ta son ko kaɗan suna ganin juna ita da shi balle ma har ya samu damar kallonta. Sai ta ce inna Suwaiba
"In Sha Allahu ma maman mon bonheur (uwata farincikina)."

Inna suwaiba ta yi murmushi jin Samira ta yi magana da farasanci saboda ta san tana son makaranta sosai yanayin rayuwa ne ya fitar da ita, sai ta ce "Allah nuna mani kin koma makaranta diyata zan fi kowa farincinki a duniyar nan wallahi."

Wani tsalle Samira ta yi sai ga ta a gaban Inna ta rungumeta tana mai farincikin da adu'ar Inna don sosai take sha'awar komawa makaranta don babu yadda za ta yi ne da ta yi don komawa makaranta. Sallama ta yi wa inna ta tafi fuskartar tana fitar da annuri jin daɗin addua'ar innarta har ta kai gidan, ta gaishe da mai gadi ta wuce falon gidan kanta tsaye saboda rashin ganin motar mai gidan.


Tana shiga da sallama a bakinta ciki-ciki Hafsat ta amsa mata saboda tinda ta ga Samira ta fara girma ta fara jin ba ta ƙaunar ganinta a gidanta don babu yadda ta iya ne shiyasa ba ta koreta ba, kasancewar innarta take yi masu aiki da farko kuma da rashin lafiya ya kayar da ita sai ta roketa a kan ita ba za ta iya zuwa aiki ba, saboda likita ya hana ta aikin wahala kuma ga shi da aikin ne suke cin abinci suke sha shiyasa kawai ta kyaleta don saboda kunyar inna saboda sun yi zaman mutumci sosai dukda tana tsohuwa tana bata girmanta sosai kuma tana gyara mata shiyasa ba ta musa mata ba lolacinyda ta zo da maganar Samira ta maye gurbinta na aiki, amma kuma yanzu abun ya fara isarta tunda ta ga Samira ta zama budurwa. Abu biyu ne ya hanata korarta na farko kunyar inna na biyu kuma iya girkin Samira da tsafta. Maganar da samira ce ta yi ne ta tsamo Hafsat daga duniyar tunanin da ta fada.

"Anty mai za a dafawa"

Sai da Hafsat ta ga dama sannan ta amsa mata da

"yau dambun shinkafa na so ki dafa mana, sai dai ba ki zo da wuri ba kin je kin yi zaman ki dan rainin hankali, don haka ki yi sauri ki dora mana jalof ɗin macaroni, in kin ɗora ga salat can ki wanke mani shi"

Samira ta amsa da "To* tana yin gaba zuwa cikin gwadala ɗin, nan da nan ta fara wanke kwanonun da suka ɓata sannan ta fara gyara kayanda za ta yi amfani da su kasacewar komai akwai na aiki a gidan sai abin da ba a rasa ba. Bayan ta ɗora sauri-sauri ta fara wanke mata salat ɗinta don ta yi sauri ta bar gidan kafin mai gidan ya dawo ya iske ta duk da dai bai cika dawowa da magriba ba amma ɓacin rana ake tsoro. Tana can tana tunaninta har Hafsat ta faɗo kitchen ɗin ba ta sani ba, sai da ta daka mata tsawa sannan ta ankara da ita

"wai ke wacce kalar yarinya ce ana yi maki magana kin yi banza da mutane don iskanci?"

Sai da Samira ta zabura da tsawar da aka yi mata sannan cikin sanyi magana kamar za ta fashewa da kuka ta ce da ita "dan Allah Anty ki yi haƙuri ban ji ki ba ne"

Hafsat tace " Ina fa za ki ji ni! Kin zo kin sa mutane gaba dan banzan tunanin kawai mtss!" Ta ida maganar da buga tsaki.

Aikin bakon raggo, raggo bakon aikin nan da nan ta wanke ta aje mata a inda ya dace ta je ta dauki abincinta da aka zuba mata saboda in Hafsat tana gida ita take zuba mata abinci, sai in ba ta nan take ɗeba da kanta. tayi gaba abunta, tafiyar minti goma ce ta kaita gidansu.


Samira na shiga gidan da "Asalam Aleikum "

Inna suwaiba ta amsa da

"wa aleikissalam ɗiyar Albarka , ina ta cewa mi ya tsayar da ke har warhaka ana kan kiraye-kirayen sallar magriba"

samira tace "wallahi innata ban samu dama na gama da wuri ba, ni ma ina yi ta sauri kar mai gidan ya dawo ya tayar da ni cikin gidanshi"

Inna suwaiba tace "To ki dai yi sauri ki dauki buta ki yi alwala ya fiye maki wannan surutun " ta ida maganar tana yin gaba zuwa banɗaki.

wacece Samira ?

Don't forget to:
Vote
Comment
Share.

Real Nana Aisha🥰

Ƴar aikin gidana(Sabon Salo)Où les histoires vivent. Découvrez maintenant