episode 02

492 14 0
                                    

RANAR WANKA...............
02
Kusan a lokaci daya  Batula da su Amina suka iso Maiduguri, tarba ta musamman Sadiya ta musu.
bayan sunci sun koshi aka bude bajakolin hira "wai nikam ina Ya Abubakar ne? bai San zamu zo bane" Amina ta tambayi Sadiya, baki Sadiya ta ta6e tace " yanacan wajen shegiyar matarsa wai babu lafiya" shewa Batula tasa tace" Allah mai iko ni har mancewa nake yanada Mata, kice shegiyar na nan" "tana nan sai bin bokaye da malamai, sai tayi kamar zata jashi sai na bugawa Mama a karkatoshi" Sadiya tayi maganar cikin jin dadi, cikin jin dadi itama Jamila tace " ai babu abunda zamu biya Mama dashi tana mana kokari sosai, kwanaki ban sanar daku bane kawai Buhari ya samu wata shegiyar Fulani ta makale masa wai zai aureta har Cameron mukaje da Umma aka yanke alakarsu kwata kwata yanzu baya maganar kowa" dariya suka saka hadda shewa " Anty Batula ya maganar bikin nan ne, baki ce komai ba" cikin katsaita irin ita mai kudin nan ne Batula tace " Abdul'Azeez zamu Kira a cashe, ko nawa ne zan biya, takwaran Mama ce fah" " naji wai matsiyatan nan zasuzo Amma sai sun gama hada kayan tsiyarsu" Amina tayi maganar tana yatsine fuska "su waye kenan?" Sadiya ta tambayeta "su Hauwa mana gayyan tsiya" " ke kikasan gayyan tsiya kam" cewar Batula, Haka sukayita kushe dangin Alh Abubakar
Sai dare Alh Abubakar ya dawo, yana shigowa Sadiya tayi cikin cikin da rai taki mishi magana, nan su Batula suka mishi caaa wai baya kula da 'yar uwansu, zama yayi gefen Sadiya bayan ya dauki jaririyarsa yace " sannu Anty Batula da Anty Amina yau Kun zama manyan na zama karami, too bazan lamunta ba" dariya sukayi Batula tace" haba Ya Abubakar mun isa mu mai daka karami. ai kai din ne da abun haushi tun dazun munata mararin ganinka baka dawo ba, ya mai jiki Sadiya tace mana Falmata ne bataji dadi bane ko bbu lafiya ne, ni na manta ma"  murmushi yayi yace" eh wlh Falmatance bataji dadi ba, ashe ma nakuda ne, Kuma Allah ya sauketa lafiya ta haifi diya mace" ba Sadiya kadai ba hadda sauran 'yan uwanta sanda suka girgiza da jin Labarin nan, lokaci kankani Alh Abubakar ya gano wannan tashin  hankalin a fuskokinsu, dakyar Sadiya tace " an ta6a haihuwa bbu cikine? Kuma ai kai kace bazata sake haihuwa ba? Kuma baka ta6a sanardani tanada ciki ba" ajiyar Zuciya Alh Abubakar yayi yace "babu yadda zamuyi da ikon Allah Sadiya, taya ma zan fara fada miki Falmata nada ciki bayan kince min bakison na ambaci sunanta dana Danta gabanki" cikin munafurci Batula tace" kai Kuma sai ka biye Mata, ai ba haka akeyi ba, gaskia Sadiya baki kyauta ba, wannan ba halin addinin Musulunci bane" karrr Alh Abubakar ke kallon Batula don yasan duk kanwar jace, murmushi kawai yayi ya sauya akalar hiran" Har yanzu su Ahmad basu dawo islamiya ba"  "eh" Sadiya ta amsa a takaice, mikewa Alh Abubakar yayi yace" bara na dubasu
Alh Abubakar na fita Sadiya tasa hannu akai ta saka ihu " na shiga uku na lalace Falmata ta fara haihuwa Kuma" cikin jimami Amina tace" abun nan da mamaki a cikinsa, Amma ai Boka yace mana ita da haihuwa sai a lahira idan anayi" cike da takaici Jamila tace "meyasa Bokan nan yamana karya, kema Anty Sadiya da laifinki da bakice ya daina Miki maganar Falmata ba da ai kin San tanada ciki tun tale tale da yanzu mun barar dashi" tsaki Batula tayi tace" ai ba kowani maganar boka bane gaskia, yanzu dai komai ya lalace" haka suka dinga jimamin abunda ya faru dasu.
Ranar suna Jaririya taci sunan Mama wato MARYAM, anyi bidi'a iya bidi'a, an gwangwaje an shashe an zubda gallon na mutunci kala-kala, washe garin suna su Batula suka koma, Su Hauwa Kuma sai da sukaje sunan gidan Falmata inda yarinyar taci sunan Umma wato FATIMA BINTU ZAHRA.
Ana gama ribibin suna Alh Abubakar ya tattari iyalansa suka koma garin Kaduna da zam.
                        DANGANTAKA
Mallam Muhammad da Mallam Musa wane da kani wadda suke zama a Funtua da iyalansu cikin zaman lafiaya, Mal. Muhammad nada Mata daya Fatima (Umma) da yara Hudu Abubakar, Hauwa, Zainab da Aisha.
Mal Musa shima yanada Mata daya Maryam (Mama) da yara  biyar Batulu, Amina, Sadiya, Jamila da Nafisa.
Ana zaman lafiya sosai a gidan kasantuwar Umma ta kashe zuciyarta tana bin Mama a hankali, Mama tanada zafi sosai ga son abun dunia, tanaso yaranta su auri masu hannu da shuni.
Bayan Abubakar ya gama karatunsa ta jami'a ne Mal Musa da Mal Muhammad suka yanke hukunci za' a aura masa Batula ana cikin wannan zance wani babban Dan siyasa yazo yace yana sonta, koda Mama taga haka sai tabi ruwa tabi Rana ta hana auren Abubakar da Batula, Batular ta auri Alh Mustapha suka tafi Abuja.
Allah cikin ikonsa ya bawa Abubakar aikin Company nan take Allah ya buda masa har ya auri Falmata wadda yar asalin Bama ce, kanuriya ce tanada hakuri ga Kuma kirki suka haifi yaro aka saka masa Suna Muhammad ana kiransa da Anwar
Hauwa ta auri wani makeri a gefen gidansu, hakan yayiwa Mama dadi sosai, Amina itama tayi goshi don babban Dan kasuwa ta aura a Funtua tare akayi aurenta da  Zainab wadda ta auri wani Ustazi mai koyar dasu a islamiya, bayan haka wani mahauci ya makalewa Sadiya yana sonta samm Mama taki wannan xance, nan idanunta ya kyalle kan yadda Abubakar ke samun abun dunia ta kawo shawarin hada Abubakar din da Sadiya, ba'a dau wani lokaci ba akayi auren, suka Kuma bazama wajen bokaye don a hana Falmata sake haihuwa, a fasahar Mama idan Abubakar din ya mutu su gaji arziki, a ganin Mama burinta na gab da cika tunda Sadiya nada yara har uku Ahmad, Nasir da Maryam.
Nafisa ce kawai ta auri Talaka cikinsu don itama ta fisu hankaline batada damuwa sam kamar Umma ce ta haifeta
Maman Ummace ta rasu a malumfashi. Mal Muhammad, Mal Musa,Aisha da Umman suka tafi don Mama Sam taki tafiya wai zata kula da gida, a hanyarsu ta tafiya sukayi hatsari Allah ya musu rasuwa dukkansu, ba karamin tashin hankali zuri'ar nan suka shigaba, idan anzo ta'aziya sai Mama tayita cewa Allah yasota Bata bisu ba da an rasa madafa

Ta Bature ce

RANAR WANKAWhere stories live. Discover now