Episode 5

314 15 0
                                    

RANAR WANKA........
Ummu Subay'a
Wattpad: Ummu Subaya
05
Haj. Hauwa na tafia Mommy ta janyo wayarta ta kira Mama "Albishir" cewar Mommy cikin zumudi, a days bangaren Mama tace" Anty kice ta samu don dagajin muryanki akwai labari" dariya Mommy tayi tace" ina Kawata Hajiya Hauwa matar General Shariff Shuwa" gyada kai Mama tayi kamar Mommy na kallonta tace" eh wadda kikace sanda kika shiga kika fita kafin ta zama kawarki" dariya Mommy tayi tace"aikuwa kin tuna da ita kenan, tohm itace yau tazo taga Maryam tace zata had'ata aure da Dan Mijinta Shatteema" ihu Mama ta saka tace" karki gayamin, wayyo Allah dadi, kaiiii Anty kice zamu kyece raini, tabbb har naga kaina nice surkuwar mai kudi" cikin nishadi da jin ddi Mommy tace" Bari kawai Sadiya, amma fah xama bata kamamu ba don tace sai ya ganta yace yana sonta, ni anan zan kaita AREWA BEAUTY SALOON a gyaramin ita tass ko nawa zan kashe a kanta, don da kudi ake neman kudi, zan Kuma had'a mata abubuwan mata don ta ciko tayi bul bul yadda zai kyasa, zan Kuma turawa Mama kudi taje gun Mal. Audu ya taimaka mana ke Kuma ki had'a da addu'a don ance bakin uwa baya wuce kan Danta" jiki a sanyaye Mama tace "in Allah ya yarda zanyi addu'a tukuru, ai wannan ba abun xama bane" Sallama sukayi Mommy ta kashe wayarta. 
                           MAIDUGURI
Rayuwa Zahra take cikin jin ddi a gidan Yakura har tayi kawama a gefen gidansu Khadija d'iyar wani Malami ne tasu tazo daya ssai, cikin kankanin lokaci sukayi sabo mai tsanani.
da Sallama suka shiga shagon Mustapha, wasu samari guda biyu suka amasa musu sallamar, kallo daya Zahra tayi niyar musu Amma sai dayan yaja hankalinta ta kasa dauke idonta.
Farine sol mai manyan ido ga dogon hanci tareda bakinsa pink mai jan hankali, bakin sajen da ya kewaye fuskarsa ne ya kara masa kwarjini da kyau, baya sahun masu kiba Kuma baya sahun tsiraru yanada kirar karfi ga faffadar kirji a takaice ya gama haduwa irin karshen nan.
"Yan Mata me kukeso?" tambayar da dayan ya musu kenan, limshe idanunta Zahra tayi ta waresu cikin sanyin murya tace" ina Ya Mustapha yaje" wadda ya tambayesu ne ya basu amsa "yaje kar6an kaya a kasuwa" Khadija da batace komai ba tunda sukazo wajen tace" ki ajiye abincin kawai mu tafi" ajiye flask dake hannunta Zahra tayi tace" idan yazo ku bashi" " muce masa budurwarsa wacce ta kawo masa" wadda yayi magana da farko shiya kara magana, dayan kam ko kallonsu baiyi ba balle su saka ran zaiyi musu magana, dariya Zahra tayi tace " wacce cikinmu tayi kama da budurwansa" shima dariya yayi yace "kece kikayi kama da budurwansa" baki Zahra ta kama tace" lallai kam kana ganina 'yar fara Dani mezan da Ya Mustapha baki" duk suka saka dariya Amma banda Gogan" kinci mutunci Mustapha don shi baki ba hali ki zama budurwansa" gyara tsayuwa Khadija tayi tace "Yayana fad'a Mata kam, ta Raina Mazan garin nan Wai sunyi baki dayawa and idan Bata auri baki ba ai abun bazaiyi balancing ba" baki Zahra ta ta6e tace" kada ku had'emin kai, nikam xo mu tafi" ta karashe maganar da Jan hannun Khadija" abincin fah idan kamshi ya damemu muci" Satan kallon Gogan Zahra tayi tace" idan da rabonku zakuci ai, kasan komai rabo ne" " zaku tafi baku fadamin sunanku ba" ya kara tambayarsu, Zahra tace " ka cinka" sanda ya dara yace" I'm not good at guessing" fari da ido Zahra tayi tace " I see, Ni sunana Zahra ita Kuma Khadijah, kaifah me sunanka?" "Allahu Akbar duk manyan suna gareku, Ni Sunana Tahir" dariya Zahra tasa tace " nice name, sai anjuma" suka fice da annuri a fuskarsu
Duban Gogan Tahir yayi yace " Haydar kana jinmu bakace komai ba" tsaki Haydar yaja yace "mezan tsaya ina fad'awa kwailayen nan don Allah, kaga yar yarinyar nan yadda take zuba kamar kurna, kai dakaga zaka iya kayi fama" Tahir kam ko a jikinsa yace "muna kai kamar hula" Haydar zaiyi magana shigowar Mustapha ne ya hanasa maganar, Tahir yace "Allanguro budurwanka ta kawo maka abinci" dariya Mustapha yayi yace "kaiii rufamin asiri Zahra ce budurwata Koh Khadija?  duk sunfi karfina, Zahra fah ita take kunun ayar da kukesha harda santin nan" washe baki Taheer yayi yace" don girman Allah? yanxu yar yarinyar nan ce" jera kayansa Mustapha ya shiga yi yana bawa Mustapha Labarin Zahra, mikewa Haydar yayi yace" guy bara na shiga ciki na watsa ruwa zafi nakeji wlh" ta6e baki Mustapha yayi bayan fitan Haydar yace" ance sai hali yazo daya ake abota Amma Ni banga yadda halinku yazo daya da Haydar ba, mutum sai cin rai da miskilanci jibi kaga yadda yake kamar yacinye kansa tsabagen cin rai" dariya Taheer yayi yace" haka Allah ya hallici kayansa, sharesa kaci gaba da ban labari" .
"Khadi Kinga abunda na gani" Zahra ta tambayi Khadija a hanyarsu ta komawa gida" me kika gani?" Khadija ta mayar Mata da tambaya, cikin shauki Zahra tace " Wannan mutumin kusada Taheer mana, kiga yadda Allah ya shimfida masa kyau, ga haske ga hanci ga idanu ga s................." katseta Khadija tayi ta hanyar cewa" duk wannan abun daya rasa hali duk basu burgeni ba, mutum na zaune kamar dutse, shida kansa ma mugunta yakewa kansa wlh" dukan Khadija Zahra tayi a baya tace" uwar wa yace Miki haka, ai Ni nafison mutum miskili wlh" tsaki Khadija taja tace" da uwar surutunkin nan wani miskili ne zai soki, wlh bama zakiji dadin zama da Miskili ba, niko Taheer nan ne ya burgeni, ga kyau ga kyaun hali" dariya Zahra tayi tace" Kuma kika kuskura kika soshi sai hawan jini yakarki wlh don irinsu tara 'yan Mata" shiga gidanda sukayi ya sakasu katse hiran kada Anty Yakura ta musu mummunar fahimta
Washegari cikin farin ciki Zahra ta dauki kunu da safe takai shagon Mustapha tanata addu'ar Allah ya hadata da Haydar" Ya Mustapha ina abokanka" Zahra tayi tambayar bayan ta juye kunun duka a fridge Kuma bataga alamar su Haydar ba" Wai su Taheer kike magana" Mustapha ya tambayeta kai kawai ta gyada mishi yace" ai sun tafi wajen aiki, kin San su leburorine, sai da yamma ake samunsu jiya abunda yasa kika samesu sun dawo da wurine, Amma yaushe kukayi sabo haka hadda tambayarsu" wayancewa Zahra tayi tace" laah kawai gani nayi kamar abokanka ne, naganka shiru ne kai daya shiyasa" murmushi Mustapha yayi yace "wlh kam Taheer na debe min kewa Amma banda Haydar cin raine dashi" "HAYDAR" Zahra ta maimaita sunan cikin ranta, badon taji ddin rashin samunsu ba Zahra ta koma gida.
Zahra takai sati tana sintiri sau biyu shagon Mustapha amma Bata haduwa da Haydar, hakan ba karamin damunta yake ba don Haydar ya zama barazana ga rayuwarta, tunaninsa ya addabi kwakwalwarta, Allah Allah take ta sake tozali dashi.
Misalin karfe biyar na yamma bayan Zahra ta gama dafa abincin Yamma dabara ya fado mata, ta dubi Anty Yakura dake yankar farcenta tace " Anty kamar maggin nan ya kare fah" sanda Anty Yakura ta karasa yanke farcenda take yanka tace "eh wallahi gobe da safe sai kije ki amso gun Mustapha" carap Zahra tace " Ya Mustapha fah sai 8 yake fita, yaushe mukayiwa Uncle girki yaci ya tafi office, inje in amso  kawai yanxu" "jeki " Yakura tayi maganar a takaice, cikin annushuwa Zahra taje ta dauko gyalenta ta yafa tace "bara naje Anty" bayan Yakura ta gama nazartarta tace "nikam Zahra Koh kin fara son Mustapha ne sai ayi ta gida gida" fuska Zahra ta daure tace "Allah shi sawwake, mezan da Mustapha" dariya Yakura tayi tace" ni wasa nake Miki, ai ke matar manyace Zahra" annashuwa kan annashuwa Zahra ta fita dashi don maganar Yakura ya Mata dadi ssai

Ta Bature ce✍🏻

RANAR WANKAWhere stories live. Discover now