RANAR WANKA..........
Ummu Subay'a
Wattpad: Ummu Subaya
06
Tun daga nesa Zahra ta hango Haydar da Taheer suna zaune a bakin kofar gidansu dashike gidan a had'e yake da shagon Mustapha, take ta gyara tafiyarta ta maidashi cat walk, da fara'arta ta isa wajensu da sallama, Taheer ne kawai ya amsa Mata tace" Ya Taheer ana ganinka" murmushi Taheer yayi Mata yace" ba gashi kin ganni ba, yau ina Khadija" baki Zahra ta ta6e tace" yamma tayi tana can tana fama da karatu" mikewa Haydar yayi yabar wajen Zahra ta bishi da kallo, Taheer dake kallon Zahra yana murmushi yace" ke meyasa bakije wajen karatun ba" inda Haydar ya tashi nan Zahra ta zauna tace" ni ai bakuwa ce a kowani lokaci zan iya komawa" share maganar Taheer yayi yace" Wajena kikazo ko wajen Mustapha" duban kofar shagon Mustapha tayi tace "wajen Mustapha nazo, ni kuwa mezanzo nayi a wajenka" Daria yayi yace" nasan ko kin kyasa Kinga handsome guy" Daria hadda kama ciki Zahra tayi tace" iyyyeh lallai Ya Taheer" ware Mata ido Taheer yayi yace" ko ban Miki bane"har yanzu dariar Zahra take ta mike tace " wlh baka rabo da abun Daria ni kaga tafia ta" shima mikewan yayi yana tayata Daria suka jera har shagon Mustapha.
Bayan ta gama amsar maggin ya rakota har hanyar gida, suna isowa kofar gidansu Khadija Zahra taga Taheer ya xubawa kofar ido tace" kai Koh me kake dubawa anan" wayancewa Taheer yayi yace " fasalin ginin ne yamin kyau" ci gaba da tafia sukai Zahra tace" gaskia ginin nada kyau kam, ko don babban Malami ne oho " " kin San mai gidan kenan?" Taheer ya jefa Mata tambaya, murmushi Zahra tayi tace "gidan Malam Madu Goni Ari ne fah wadda aka fi sani da Malam KaKa Abban Khadija ne" ware ido Taheer yayi yace" kina nufin nan ne gidansu Khadija" kai Zahra ta gyada mishu tareda da cewa" ya naga kamar ka firgita ne" ajiyar zuciya Taheer yayi yace " Dole na firgita Zahra wlh sonta nake Kuma naga tafi karfina" kallon Tara saura Zahra ta mishi tace " ina tafi karfinka? mace nafin karfin namiji ne? by the way 'yar malami ce baza'a samu matsala ba"tambaya Taheer ya Mata" kina ganin baza'a samu matsala ba ina lebura mai gini" daria Zahra tayi tace " wlh bbu komai indai daso da kauna" maraice fuska Taheer yayi yace "Allah yasa" har bakin kofa Taheer ya raka Zahra kan ya juya.
Zahra na ajiye Maggi batayi kasa a gwiwa ba ta nufi gidansu Khadija, taje a daidai don ta samu Khadija ta gama karatu, kamar kurna Zahra ta shiga baiwa Khadija Labarin yadda tayi da Taheer, dariya Khadija dake tankad'e tayi tace "wlh dake da Taheer din duk bakuda aiki, nifa ban shiryawa soyayya ba karatu na saka a gabana" harara Zahra ta hurga Mata tace" kedai kice mai kudi kawai kikeso don kinji shi lebura ne" tsayarda tankad'en Khadija tayi tace "Allah sarki mena munana min zato Zahra, arziki da rashinsa duk na Allah ne, sai kiga abunda wani leburan xai Miki yafi na mai kudin, Kuma auren talaka yafi kwanciyar hankali" kad'a kai Zahra tayi tace " idan hakane tohm ki yarda da magana Taheer, kin yarda?" Zahra ta karashe maganar tana leka fuskar khadija, tabe baki Khadija tayi tace "Kinga kada ki dameni Kona amince ma sai naja mishi aji tukun" tsaki Zahra taja tace " Allah yasa ya tsinke" Daria Khadija tayi suka bar maganar sukaci gaba da wani hira.
Cikin kankanin lokaci Khadija da Taheer suka fara soyayya sosai, Soyayya ma Jan hankali da burgewa, a dayan bangaren kuwa Soyayyan Haydar ya mamayewa Zahra zuciya, ta rasa natsuwa ta rasa kwanciyar hankali, shiko Haydar koya kula, Khadija na iya bakin kokarinta wajen danneta kada ta nuna, abun yakai har Mustapha ya ganota " Wai Zahra kada dai ace son Haydar nan kike?" Mustapha ya tambayi Zahra bayan ta gama kar6an abunda take so, jiki a sanyaye Zahra ta zauna akan plastic chair tace " wlh hakane Ya Mustapha ni kaina bazance yaushe hakan ta faru Dani ba, nayi duk yadda zanyi Amma abun ya faskara" ta karasa da hawaye, cikin damuwa Mustapha yace " Subhanallah, gaskia Zahra bakiyiwa kanki adalci ba, Ina ke inason Dan Cirani lebura, wadda baida galihu, kada ki yarda kyaunsa ya rudeki, Haydar ba level dinki bane Zahra" zafafan hawayene ya shiga fitowa daga fuskar Zahra tace" Ya Mustapha koya yake Ina sonsa a haka, sonsa daga Allah ne, ina kaunarsa fiye da numfashi, ji nake kamar na tareshi na fada mishi" tsaki Mustapha yaja yace" Wai kina cikin hayyacinki kuwa Zahra? kin San idan Anty Yakura taji abunda kike Shirin yi zata maidaki Kaduna ba tareda da lokacin komarki tayi ba, kin San wannan mutumin mai bakin halin nan ba sonki zaiyiba har abada" kuka Zahra ta shiga yi kamar ranta zai fita, sosai ta bawa Mustapha tausayi.
Jiki a sanyaye Zahra ta bar shagon bayan taci kuka ta share hawayenta, a inda suka saba zama ta hangi Haydar shi kadai yana zaune, ta gabansa tazo ta wuce ranta na kuna, ko daga ido bayyi ba balle ya dubeta hakan shi ya kara tabbatar Mata maganar Mustapha wadda yace har Abada bazai sota ba, wani sabon hawaye taji yana zuwa Mata, tayi saurin sharewa ta wuce.
Har gida Mustapha yazo ya sanarda Anty Yakura halinda Zahra ke ciki, godia ssai Anty Yakura ta mishi ta Kuma ajiye Zahra "Zahra ki dubeki da kyau, Ina Allah ya tauye halittarki har zaki rasa wadda xakiso sai wani leburan banza mai bakin hali, tooh ki bude kunnenki dakyau ki jini bbu ke bbu wannan mutumin Kuma daga yau bazaki sake fita ba har lokacin komawanki Kaduna yayi, idan badon Sadiya bama da kin kokawa gobe goben nan" kuka Zahra ta sakawa Yakura don ta kasa cewa komai, kukan ya kara tunxura Yakura ta dinga yiwa Zahra fad'a.
Kwana uku Zahra tayi bata cin abincin kirki Sam taki sakin fuska, abun ya ishi Yakura ta Kira Falmata ta sanar da ita, nan Falmata tace a bawa Zahra wayar "Mamana meyasa kikayi haka, shekarunko har nawane zakiso wani wadda bai damu dake ba, ki tuna burinki Mana na zama likita, bazaki so ki saka Maminki, Ya Anwar da Abbanki alfahari dake ba" Kuka Zahra tasaka tace "wlh Mami ina sonsa ban San ya zanyi da raina ba" murmushi Mami tayi tace" daina kuka Mamana ki shirya cikin satin nan ki dawo, insha Allah zaki mance dashi, nasan kewarmu ne ya saki sonsa" ita dai Zahra maganar Mami batayi tasiri a kwanyarta ba, Amma tace "Toooh" ta mikawa Yakura wayar.Ta Bature ce ✍️