(☆^O^☆ ☆^O^☆)
*❤️ LAIFINA NE❤️*
(☆^O^☆ ☆^O^☆)NA
*FRESH UⓂ️MIEY XEEY*_Wattpad....Freshummieyxeey_
'''Ina mai baku hakuri na jina shuru da kukai, nashiga busy ne and ban muku akawarin typing kullun ba amma idan kuna comment I'll try my best....Son so to you❤️🔐'''
*PAGE 3️⃣5️⃣*
Sallama Fauxeey tayi, taga Bobo tsaye a kofar gate din, amsawa yai ciki ciki, hada ido sukai taga sam ba annuri a fuskarshi. karasowa ya farayi ahankali
Yana matsowa tana matsawa baya
Kallon da Bobo yake mata gaba daya ta rude, Ahankali ya karaso gabanta cikin isa da ji dai ya tsaya gaf da ita, suna shakar nunfashin Juna yana mata wani irii mugun kallo
Karjinta kuwa bugun takwas takwas yakeyi, tana addua
Matsawa yayi baya dan wani abu yakeji yana mai yawo a kwakwalwarshi sai ya fake da warin talauci kikeyi
Hannu yasa ya turata kanta ya buga da jikin bango, Yadan tsorata amma da yake muguntane a zuciyarshi be karaya ba
D'ago wa tai ahankali, Allah yasa bata bugu sosai ba, Itama wani irin kallon Wulakanci takemai, Banda lokacin ka tace mai tai tafiyarta
Janyo hijab dinta yayi, gaba daya hijab dinta ya sauka a kafadarta, ganin gashin kanta yayi baki wuluk, yasha Gyara se kyalli yakeyi
Da yake Bobo nason gashi gaba daya ya rude, Aranshi yace beautiful kamar yakai hannunshi ya shafa kan se kuma ya bita da harara
Maida hijab dinta tai ta rufe kanta, tacigaba da tafiya
Biyota yai har falon da take Zama yana Ji aranshi be yarda da yarinyar nan ba, Ga kyau ga Gashi anya kuwa, Wata zuciyar tace kuma koma meye ai ba Fita zata karayi ba, Ta shugo kenan
Tsare ta da ido yai yace 'yar talaka jiya na baki kudi dan ki wanki da wanka dan naji warin talauci kkeyi shine Kika tafi kikabarshi ko? Uban me kke takama dashi?
Eh Tace na barshi din saboba baka kai matsayin da zan amsa kudi a wajenka ba
Hura iska yayi a bakinshi yace huhh, ranshine ya baci yazo zai kai mata chapka ta matsa be sameta taba, Tace Ubanka yayi kadan dan iska kawai
Ubana fa kikace? Se a time din taji meta fada dan kirjinta bugu kawai yakeyi
Fita yayi da zafin rai yashiga kitchen ya ebo ruwa a dan karamin bucket bata ankara ba ya watsa mata gaba daya, Yace yar matsiyata kawai se nayi maganinki, Qila ruwan dana watsa maki ki tage wari
Sharkaf fauxeey tayi, aranta tace lalle wannan da rainin wayon
Yanda kayan yabi jikinta saboa ya ji'ke duk sassan jikinta ya fita, haka yabi jikinta da kallo, ga yar jakarta a makale ta cikin hijab tsoranta karya janyo jakan ta shiga Uku
Yanda yake kallonta ta mai kyau aanshi yace Wow
Ita kuma aranta tace bakomai bane illa alhakin Haidar, Dole na nemeshi na bashi hakuri Koda kuwa bazai kulani ba, lalle na tafka kuskure, Alhakin Haidar
Hawaye masu Zafi suka zubo mata, Bobo ya fara murmushi mugunta, yace Yarinya kenan banfara miki komai ba har se kin amince abun da nakeso muyi if not se nayi by fire by force
Ya juya zebar dakin Waigowa ya sake yi yace make sure Kin gyara dakin kin goge kin fesa room freshner dan karki gogawa dakin warin talauci
Jan tsaki tai tace Mugu kawai, har ya murda kofa zai tafi ya waigo ya karaso kusa da ita

YOU ARE READING
LAIFINA NE
FantasyDuk da kasantuwarta mai rauni amma hakan bai gagareta girmama kanta fiye da kimar kowa ba. Ta fara gina labarinta cike da izza da kyamatar halin da namiji. Duk da akance abinda aka gasa shi yaga wuta to saidai ita ido biyu suka yida wutar. Tayi musu...