Chapter One

22 1 0
                                    

Chapter 1
    RASHIN SANI By Mrs. Kwaise Laaquish

Al-amin danAllah kayi hakuri ka yafe min, kar ka fasa aure na. Wata mace matashiya tasha uban makeup nagani  durkushe kan gwiwowin ta cikin hawaye face-face tana rokon Alamin. Amma ko jinta bayayi, a fusace ya fita ya bar mata dakin saboda yanda zuciyar shi ke kuna tana bugawa. Motarshi range rover 2019 ya shiga ya ja ta a guje ya bar lounge din. Lounge din ya sha decorations Sosai, ko ina an sa balloons da  flowers da kuma wani katon banner a sama an sa “will you marry me? Personal assistant dinshi farouk, wanda yazama kaman aminin shi tunda komai tare suke, Yana ta kwala mai kira, amma inaa...Alamin ya riga da ya fizgi motarshi ya bar gun, bai ma lura da wani farouk ba. Yana tuki aguje cikin tsananin bacin rai yake tuno da maganganun da yaji Ramlah na fadawa kawayen ta. “Ai da zarar na aure shi zanci gaba da harka ta, daman zan auri Al-amin ne kawai saboda kudin shi, dan ni bazan iya zama da namiji daya ba,kuma kun san namiji daya yayi min kadan, taapi kawayenta sukayi da shewa, suna cewa shegiya ke dama ta ya namiji daya zai iya satisfying dinki. Ah toh! Kun gani, shi sakaren yana sakarmin nairori, ni kuma ina kashewa samari na..tana dariya tana tapa hannu da kwarta...dago kanta tayi sama sai kawai karap! Sukayi Ido hudu da Alamin

min,yana tsaye bakin kofa. Chan dai dai park din kusa da villa dinsu yayi parking motarshi,ya kifa kan shi kan steering Motar, maganganun Ramlah na ta mishi yawo a kai. Ya fito daga motan Dan yasha iska saboda kan shi sai sarawa yake dab da isowar Farouk kenan dan yasan nan Al-amin din yake zuwa shan iska da nutswa Duk sanda yake cikin damuwa. Chairman me ya faru naga ka fito a fusace, hope dai lafiya? Juyowa yayi ya Kalli abokin nashi cike da damuwa sannan ya kara juya bayan shi, yanzu Ni shikenan Farouk bazan taba samun macen da zata soni tsakani da Allah ba rayuwata? Haka zan kare, Duk macen da nake so kuma zan aure ta ita kudina kawai takeso baniba. Toh yanzu inda bani da kudin fa? Ko in suka kare? Nan ya zayanawa Farouk duk abun da yaji Ramlah na fadawa kawayenta a gurin engagement dinsu. Farouk ya jinjina kai yaji labarin ba dadi, yana tausayawa abokin nashi. Ka kwantar da hankalin ka, ai ka godewa Allah da ba ayi auren ba kafin ka sani daga baya. Allah Ya kiyaye ka. Kuma inshaAllah zaka samu mace mai sonka tsakani da Allah ba don kudin ka ba. Al-amin ya dan numfasa Ka daina wanan zancen, sai kace a tatsuniya. Allah kuwa da kwai su da yawa, kawai dai kana rashin sa’ar su ne amma mai sonka na nan tafe. Kasan komai lokaci ne sai Allah Ya yi. Wata yar dariyar takaici Al-amin yayi, yace manta kawai duk mata halin su daya,mayaudara ne. Duk babu masu so na gaskiya da tsoron Allah,su dai kawai suga kudi. Sun gara ni dayawa,Ya karashe maganar cike da kunar rai da karyarriyar zuciya. Ya chillo wa Farouk key din motarshi, yayi sauri ya cabke. Muje ka sauke ni a office na manta da wasu files……..

Wata doguwar budurwa da bazata wuce 19years ba,fara sol,ita ba mai kiba ba kuma ba mai rama ba, idanuwan ta round dara dara farare kaman ta sa musu kwalli,eyelashes dinta dogaye kaman sawa tayi,eyebrows dinta a cike bakake,hancin ta dogo kaman kara,lips dinta pink dan madaidaici kaman an zana mata shi. Idan tana magana ko dariya gefen kumatun ta lotse wa suke(dimples). Amrah kenan yarinya mai kyau mai tsada. Tsayawa gaya muku kyaun ta bata Lokaci ne saboda Allah ya hore mata kyau ta ko ina, ta hadu karshe, ga diri. Duk namijin daya Kalle ta sai ya juya ya kara kallon ta….. Sanye take da kayan bacci na riga da wando pink masu hoton maguna amma ta dora bakar abaya mai budeden gaba(kimono),ta nada mayafin abayar baki sai takalman ta flat shoes, ta fito daga wani babban supermarket da ledoji biyu a hannu sai sauri take kaman Zata tashi,gashi har an fara kiran sallar isha’i ta,ga maamah sai calling dinta take, kusa gab da motar ta yar corolla sai kawai ji tayi ‘falsal! An fallatsa mata ruwan tabo a jiki daga saman ta har Kasa, take nan ta saki ledojin hannun ta suka zube cikin ruwan tabon saboda firgita, in ranta yayi dubu ya baci. Tana kokarin share ruwan daga fuskar tata don taga waye yayi mata wannan wulakancin, a fusace ta dago kanta ta ga wata mota ta wuce ta, tana daga hannu da mita amma inaa motar tayi gaba, zuciyar tana ta tafasa. Farouk ya Kalli front mirror din motar yaga Wata mace nata dago musu hannu tana mita kuma ga kaya sun zube a gaban ta, yace chairman kaman fa mun watsa wa wata ruwa a baya da muka dan fada ramin nan, naga ma munyi mata barin kaya. Ya dan numfasa Kadan cikin shan kamshi yace toh yi reverse. Tana tsugune cikin mita tana kokarin kwashe kayan da laluben key dinta,sai taga motar da ta watsa mata ruwan na yin reverse gurin ta…. Winding down tinted glass din motar yayi har Farouk ya leko daga inda yake ya bude baki yana kokarin bata hakuri, Al-amin ya Kalle ta daga sama har kasa, sai yaji gaban shi ya fadi yaji kuma wani sabon bacin rai, ya dauko wasu sababbin bundir din dubu daya ya cilla mata,ko kallon inda take beyi ba ya ja window din motar yacewa Farouk ja mutafi……..

Ku biyo ni kuji ya zata kasance tsakanin Al-amin da Amrah

RASHIN SANI

     BY

 Mrs. Kwaise

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Nov 20, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

Rashin Sanin Zuci ❤Where stories live. Discover now