CHAPTER 3
dur kusawa nayi a kasa nace baba kohda sau dayane ka aminche inganshi, Alfarmar danakeso kayimun kenan Abba nayi ma alkawarin bazan baka kunya ba, shuru Abba yayi saboda yana tsananin kaunata bankuma taba neman Abu na rasa a wajensa ba.
Tashi kije na aminche, murmushi nayi Wanda yafi kukan wuyan yi saboda innuna mishi farincikina, Amman Chan kasan zuciyana nasan angama tarwatsa ilahirin rayuwata, banyi wata wata ba sama na hau nayi wanka na gyra jikina NASA rigar bacci wato nighty, a ranar koh waya banyi da imran ba, Asuban farko yakira, *Hello sweetheart Good morning I missed you throughout yesterday kiyi hkr beb I was a little bit busy ne shiyasa hope kina lfy hope kinfara shirin tarban bako?*
Murmushi nayi bansan lokacin da hawaye masu zafi suka sakko daga kwarmin idanuna ba, bansan lokacin danake mishi eh ba, tell me what is your favorite ta yadda zan dafa maka, Sablove favorite Dina koh a gidanmu ranar da za'ayi sai cooks na gidanmu sunsha wahala cos saboda abinchin larabawa ne kuma kinsan ni balarabe ne dukda nasan baki sani ba, Sablove na shirya tsaf Don zuwa ganin hasken idanuna, na shirya tsaf Don ganin masoyiyata, kar incikaki da surutu naba zainab da fadila Instagram handle dinki zasuyi following dinki, kuma ina farincikin sanar dake zaki samu Zee da fadila a Nile cos achan suke but zee takusa gamawa fadila koh tasamu Admission kamar yadda kika samu,
Wani murna nayi nace haba waiyo sweetie naji dadi nasan suma haka suke kyawawa kamar kai, anan mukagama hira sai karfe goma na sakko Abba kuwa ya wuce Abuja saboda wani business trip dayake dashi Mommy kuwa tatafi kaduna tanada meeting itama, Samir, Samira, Areef, Noor sun tafi school sai masu aiki sai kaiwa da komowa sukeyi, masu gadi kuwa sai safa da marwa suke, gidanmu katafaren gidane Wanda zagayashi a lokaci guda aikine, duk yan'uwana maza sunada part dinsu Amman saboda karancin shekarunsu yasa baa barsu achan sukadai ba, Larai nakira ta hadomun Breakfast Egg omelet, plantain chips, offals soup, Apple and orange zaune nake ina Chi ina editing Video danayi jiya tuni nayi posting ruwan likes kawai nake gani, Larai na Kara Kira nasanar da ita gobe akwai bako,
Inaso a gyara koh ina inaso dakin baki dake wajen clinic a tabbatar a gyara kuma inason ayi girki na gani na fade kisamu chef kice mishi harda abincin larabawa za'ayi inaso kafin karfe daya an kammala komai, sannan yanzu kicewa driver inason zanje shopping Don jibi in Allah ya kaimu zan tafi school kicewa Cashier cewa I need an ATM domin zuwa shopping.
Gamawata keda wuya natashi nayi wanka na shirya tsaf cikin wata boubou gown Dita Mai ruwa doruwa wato yellow simple makeup nayi na fita tuni driver ni yake jira, tafiyar danake cikeda takama ma'aikata keta gaisheni ina amsawa kudi nake basu duk Inna fito kyautar Dari biyar biyar, kuma komai na more rayuwa akwai ba abunda suke siya Amman ihsani yanada kyau shiyasa idan bana gidan basajin dadi.
************
IMAM P.O.V
Ansiyo Kayan alatu daga Kayan sawa takalma, jaka, jewelries, Kayan makeup Kayan kwalam da maku lashe baa magana kudi yayi aiki haka haka sunyi Goma Don banason karanta a rayuwana a haka gani nake sunyi kadan Hajiya tayaba irin kyau na Kayan tace na iya zabe, Dare yayi Dad yakirani yake sanar Dani flight Dina karfe goma ne murna duktabi ta isheni kamar inyi tsalle Amman nayi behaving matured...Zee ce tafito tareda muneera jinayi wani bakinciki ya sokeni a kirjina, Brother naso ace kayi mana booking flight Dani da Munie dasaimu rakaka a matsayinmu na kanninka abun alfaharinka, ni mutum ne da banason surutu, banason ana shiga sabgar rayuwata Amman tunda nakasance a karkashin kamfanin Dad shikenan komai ya sauya dole kazama Mara wasa da daukan Raina, kallon zainab nayi nace tunda kikazo da wannan zabiyar kin bata magana banason Munie hakan yasamo Asaline tun daga wajen uwarta Hajiya Atu, Hajiya Atu hatsabibiyar matsafiya ce uba suka gada da Mom dina, tayi iyayinta ganin taga bayan Mom Dina damu kanmu Don hakarta ta cimma ruwa ta auri Dad Amman kuma a wajen biye biyen bokayenta kidnappers suka kamata sukayi mata yankan rago, dalilin Dayasa Mom ta daukota daga Niger ta kawota Nigeria kenan, zee kiyi hakuri wata Rana zatazo har cikin gidannan, I hate seeing Munie a gabanta nake fada kuma tasan irin tsanar danayi mata ya wuce misali, tashi tayi da gudu ta haye sama Tana kuka, gurin mom ta wuce nikuma na sallami zainab na wuce bangarena dake cikin gidan tafiyar minti shabiyar nayi kafin in karasa.
YOU ARE READING
BURIN SABRIYA
General Fictionlabarin wata yarinyar hamshakin Mai kudi ne Wanda ake fadenshi a fadin duniya, Allah ya azurtashi da yaya biyar Sabriya itace yarsa ta fari, babban burin Sabriya shine rayuwa da Imam a matsayin mijinta boyayyen alamari ya bayyana Wanda burinta ya Ga...