WATA DUNIYA!
"Ina son ka Amaan. Na dauki alkawarin ci gaba da kula da kai duk rintsi duk wuya. Zan ba ka gata, zan kaunace ka fiye da yadda nake kaunar kaina, sai dai...!" Numfashi ta ja tana furzar da iska daga bakinta, "Sai dai a boye zan so ka, ba na so kowa ya san da zaman ka, kar ka rinka fitowa a kalle min kai, ina gudun ka...